Ixznarh

Ixznarh it was createted purposely to share reasonable ideas that may be useful to people.

19/06/2026

SAKON DA ZAI SA KA KWANTAR DA HANKALINKA AKAN RAYUWA

Wata rana Sheikh Dr. Mansur Isa Yelwa Hafizahullah
yana yi wa wasu nasiha tare da Abu islam,
Dai ya fadi wata magana mai zurfi
da ta sa mutane da yawa s**a tsaya suna tunani.

Ya ce:
Tun da na fahimci cewa Allah Ya riga
Ya tanadar wa kowane bawa abin da zai samu,
Sai na kwantar da hankalina.

Ya ce abin da Allah Ya kaddara zai same ka, zai same ka.
Ba dabararka ba ce take halittar arziki.
Ba wayewarka ba ce take rubuta arziki.
Ba yawan damuwa ba ce take ƙara arziki.
Allah Ya riga Ya tsara komai.

Ya ce mutum ya nemi halal,
Ya yi aiki, ya yi kokari,
Amma kada ya rayu cikin tashin hankali
kamar shi ne yake juya al'amuran duniya.

Domin mutane da yawa suna tara dukiya suna cewa:
Sai na gama wannan...
Sai na tara kaza...
Sai na yi wa 'ya'yana kaza...

Amma kafin ya gama shirinsa...
Sai kiran Allah ya zo.
Ya tafi.
Ya bar komai.

Sai wasu su zo su ci abin da ya shafe
Rayuwarsa yana tara wa.

Sai Prof ya kawo wani misali mai girma.
Ya ce:
Mutum yana da dukiya.
Matarsa tana da ciki.
Sai Allah Ya yi masa rasuwa.
Lokacin rabon gado ya zo.
Sai a dakata.
A jira jaririn da ke cikin ciki ya zo duniya.
Saboda shi ma yana da nasa rabon.
Ka ga har yanzu bai ga duniya ba.
Bai yi aiki ba.
Bai sha wahala tare da mahaifinsa ba.

Amma Allah Ya riga Ya tanadar masa nasa arzikin.
Ana jiransa ne kawai ya zo ya karɓa.

Wannan ya nuna cewa Allah ba Ya manta da kowa.
Allah Ya san naka tun kafin a haife ka.
Ya san inda zai same ka.
Ya san lokacin da zai same ka.
Ya san yadda zai same ka.

Prof ya ce:
Rashin plan dinka ba zai hana ka arziki ba,
kuma yawan plan dinka ba zai tilasta arziki ya zo ba
Eh, Musulunci ya koyar da tsari.

Amma tsari ba yana nufin mutum ya rataya zuciyarsa
da gobe da jibi ba har ya manta da Allah.

Abin da ya kamata shi ne:
Ka nemi halal.
Ka yi aiki.
Ka yi anfani da abin da Allah Ya ba ka.
Ka kula da iyalinka.
Ka yi alkhairi.

Sannan ka bar abin da yake gaban shekaru
goma ko ashirin a hannun Allah.

Address

Makaurachi
Katsina

Telephone

+2347030409007

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ixznarh posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category