
05/05/2025
Allah ya jikan maza.
An haifi Malam Umaru Musa Yar’Adua a ranar 16 ga watan August 1951, ya kuma koma wajen mai mulkin da ba ya da karshe a ranar 5 ga watan May 2010, yau shekara 7 daidai da rasuwarsa kenan .
Kamin shigar Malam Umar Musa jam’iyyar PDP ya fara da jam’iyyar PRP sannan daga bisani ya koma jam’iyyar SDP a shekarar 1989 zuwa 1998. Bayan nan ya shiga jam’iyyar PDP a shekarar 1998 zuwa 2010.
A ta bangaren iyali kuwa Malam Umar Musa ya auri matarsa ta farko Hajiya Turai Yar’Adua (1975–2010), sai kuma Hajiya Hauwa Umar Radda (1992–97), ya kuma rasu ya bar ‘ya’ya guda tara (9).
A ta fannin ilimi kuwa Malam Umaru Musa Yar’Adua ya halarci makarantar Barewa College, da kuma jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.
Malam Umar Musa ya yi gwamnan jihar Katsina har karo biyu tun daga 29 May 1999 har zuwa 28 May 2007.
Ya ci zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 21 ga watan Aprilun 2007 inda aka kuma rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Nijeriya a ranar 25 ga watan Mayun 2007, a karkashin tutar jam’iyyar PDP .
Bayan nan Allah Ya jarabce shi da rashin lafiya a lokacin yana shugabantar kasar nan, in da aka wuce da shi wani asibiti dake kasar Saudi Arabia, bayan ya dan samu sauki aka dawo da shi gida Nijeriya a ranar 24 ga watan Febrerun 2010, Allah kuma Ya yi masa rasuwa a ranar 5 ga watan May 2010.
1. Malam Umar mutum ne mai son gaskiya komin dacinta koda kuwa a kansa fadin gaskiyar ya k**a, k**ar yadda ya bayyana cewa zabubbukan da aka yi a baya akwai ‘yan kurakurai, kuma za a gyara, daga cikin gyaran da ya yi ne ya dakko Malamin Jami’a Farfesa Attahiru Jega ya nada shi shugabancin hukumar zabe mai zaman kanta, wanda sanin kowa ne an samu canji matuka a fannin zabe.
2. Malam Umar Musa mutum ne mai rikon amana, tattare da 3kishin al’amura