12/09/2021
YAUSHE SARKIN RANO YA ZAMA SARKIN KANO?
Daga
Rabiu Na’auwa
Kowace masarauta tana da wasu keɓantattun kayan tarihi na al’ada waɗanda suke manne da kujerar sarautar masarautar, wato babu wanda zai iya amfani da su, ko iko a kansu sai wanda ya zama jigon wannan masarauta, wato wanda Allah ya naɗa a matsayin Sarki. Waɗannan kayan sarauta su ne ake kira da AlarSarauta. Su waɗannan kaya masarauta tana samar da su ne ta hanyar wasu tsofaffin sarakuna da s**a yi shuhura a wannan masarauta, ko s**a kafa masarautar.
Idan sarkin da ya kafa masarauta yana da wani keɓantaccen abu da ya ke amfani da shi, misali; Mashi ko Takobi ko wata Wuƙa ko Takalmi ko Ƙaho, ko kuma wani abu da ake kaɗa masa k**ar Tamabari ko
Kakaki, ko wani kirari wanda shi kaɗai ake yi wa, ko kuma wani nau’in kayan kiɗa wanda shi kaɗai ake kaɗawa kuma bayan rasuwarsa wanda ya gajeshi shi ma ya ci gaba da amfani da shi. Sarkin da ya yi shuhura a masarauta in akwai wani abu da ya yi shuhura a kansa ko ake alaƙantashi da shi. To ire iren waɗannan abubuwa su ne masarauta take taskancewa ta haɗasu da kujerar sarauta, sai ya zamto duk sarkin da ya gaji sarauta to shi zai gaji waɗannan kaya, idan abin sakawa ne, shi ne zai riƙa sakashi, haka idan abin kiɗa ne ko na busa, shi kaɗai za’a kaɗawa ko busawa, duk ƙasaitar hakimi a wannan masarauta bai isa ya yi amfani da wannan abin da yake cikin ala ta wannan masarauta ba, sai dai in Allah ya yi masa Sarki.
Haka kuma Sarkin da aka tuɓe shima abinda ake fara ƙarba daga hannunsa su ne waɗannan kaya na Ala. A taiƙaice dai su ne suke tabbatar da sarauta, su ne cikar sarautar kowane sarki. Wannan ya sa a kowace masarauta za ka samu suna da tasu Alar, misali a Masarautar Daura, kayan da suke nuna kai ne Sarkin Daƙura su ne : Wuƙa da Takobin Bayajida da Siradan Doki guda biyu, ɗaya yana da wuƙa mai kube da ƙaho a jikinsa na azurfa, shi ne wanda Bayajida ya zo da shi ƙasar Hausa. Sai likkafa ta Tagulla da sarƙa, sai kayan Sulke, da Zabban azurfa guda biyu babba da ƙarami da carbi, da Tambura guda biyu na Magajin Turu da Kuntukuru, sai kuma wasu guda uku wanda ake kiran babbansu da Gamariga.
Waɗannan su ne kayan ala na masarautar Daura, sabo da haka duk wanda yake Sarkin Daura shi kaɗai ne zai iya riƙe wua ko rataya takobin Bayajida, duk ƙasaitar hakimi ba zai riƙe su ba, sai dai Sarkin da yake sarauta.
Haka abin yake a masarautar Kano akwai waɗannan kayayyakin Ala guda 7 a masarautar Kano wanda dole sai wanda ya gaji Gidan Rumfa ne kawai zai iya amfani da su;
1. Tagwayen Masu
Tagwayen masu sun samo asali ne tun a zamanin wasu sarakuna ‘yan biyu ‘Nawata da Gawata’ ɗiya ga Sarkin Kano na uku a jerin Sarakuna Haɓe wato Sarki Gajimasu. waɗannan tagwayen sarakuna sun yi mulki a Kano a lokaci ɗaya duk da cewa ɗayansu ya mutu ya bar ɗaya. Ɗaya ya yi wata bakwai ya rasu, sai ɗayan ya ci gaba da mulki, shi ma ya ƙara shekara ɗaya da wata biyar ya rasu, gabaɗaya dai tsawon shekar biyu s**a yi suna mulki a Kano. Waɗannan sarakuna kowane cikinsu yana da mashi, wannan ya sa bayan rasuwar dayan sai ɗan uwansa ya haɗe waɗannan masuna guri ɗaya, shi ne s**a zamto Tagwayen Masu, sannan aka keɓesu ga Sarkin Kano, wato sun zama cikin abinda ake kira Ala.
2. Takalmin Gashin Jimina,
Takalmi ne da ake yi masa ado a samansa da gashin jimina, kuma Sarkin Kano Muhammadu Rumfa, Sarkin Kano na 20 a jerin Sarakunan haɓe, shi ne ya fara amfani da wannan takalmin. Shuhurar Rumfa ta kai matuƙa, ana iya cewa ba’a yi sarki a Kano k**ar Rumfa ba. Saboda shi ne ya gina gidan sarautar Kano na yanzu da wasu abubuwa da yawa na al’ada da addini da kuma ci gaba. Saboda haka daga kan Rumfa Sarakunan haɓe na Kano s**a gaji Takalmin Gashin Jimina, kuma shi ma sai ya zamto an taskanceshi ya zama cikin kayan Ala na Sarautar Kano. Bugu da ƙari a lokacin da Dabo ya zama Sarkin Kano, ya rubutawa Sarkin Musulmi Bello cewa yana son ya dawo da kayayyakin Hausawa na sarauta, ya amince masa, Takalmin gashin Jimina shi ya fara sakawa a cikin kayyakin sarauta da Hausawa s**a bari.
3. Kwari da Bakan Dabo
Kwari da baka shi ma wannan Ibrahim Dabo ne ya fara amfani da shi, kuma Sarki yana fita da shi a matsayin sanda ya riƙa godara shi musamman in za shi wani abu da ya shafi addini, k**ar Sallar idi, Sallar Juma’a da mak**antansu, shi ma wannan kwari da baka bayan rasuwar Sarkin kano Malam Dabo ya shiga cikin Ala ta Sarautar Kano, saboda haka babu wani Sarki da zai rataya kuma ya dogarasu face Sarkin Kano wanda yake kan gado.
4. Wuƙar Yanka
Wuƙar yanka ita kuma ta samo asali ne a lokacin mulkin Fulani a Kano, Sarkin Kano na farko a jerin Fulani, Sulaimanu a lokacinsa an ce wasu daga cikin Fulani sun yi masa bore, sabo da wasu na ganin ya yi ƙanƙanta da zama Sarki, sabo da a lokacin bai fi shekara 30 ba, amma saboda ilminsa Ɗanfodio ya amince da naɗinsa. Wannan ya sa ba duka Fulanin s**a bishi ba, da ya ga haka sai ya rubuta takarda ga
Shehu Ɗanfodio ta neman ɗauki, sai Ɗanfio ya bashi wuƙar yanka da takobi a kan duk wanda ya bijire masa ya yanka shi. Wannan ya sa tin daga lokacin Sarkin Kano Sulaimanu Wuƙar yanka ta shiga cikin Ala. Koda yake akwai tababar cewa har da ita kanta takobin tana cikin kayan Ala na sarauta ta Kano.
Wadannan kayayyaki su ne wanda Sarki ne kaɗai zai yi amfani da su. Akwai kuma sauran gudu uku da su kuma Sarki kaɗai ake yiwa amfani da su, wadannan abubuwa ana samunsu a sauran masarautu kuma su na iya shan banban a yanayin ko muhallin da ake amfani da su:
1. Kakaki
Kakaki shi ma yana cikin Ala ta Kano kuma shi ma Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ne ya fara amfani da shi, saboda haka shi ma sai ya kasance Sarki ne kawai ake busawa Kakaki a Kano, saboda sun saka shi cikin jerin abubuwan da s**a keɓanta da Sarki.
2. Figini
Figini shi ma wani kalar abin fifita ne da dogarawa suke yiwa sarki fifita da shi, su ma wadannan dogarai ana kiransu Figini. Ana yin shi ne da gashin Jimina da kuma ado na alfarma, shima k**ar Kakaki, Sarkin Kano Rumfa ne ya fara amfani da shi kuma shi ma daga lokacinsa ne ya shiga cikin ala ta sarauta.
3. Tambari
Tambari shi ma ya samo asali ne tin a lokacin mulkin haɓe, kuma shi ma ba’a kaɗawa kowa shi face Sarki. To shima Tambari yana cikin kayan Ala ta masarautar Kano wacce ta kebanta ga Sarki shi kaɗai.
4. Sandar Girma
Sandar girma wata Sanda ce da take da ɗauke da wani ado mai k**a da na azurfa, mai zubin kan sarki a samanta, ita kuma ta samo asali ne tin lokacin da Turawa s**a ci sarakunanmu da yaƙi, idan za’a naɗa sabon Sarki a ranar bikin naɗi Gwamna ko D O za su damƙa ta ga Sarki alama ce da take nuna ka zama sarki mai cikakken iko a gwamnatance. Wannan ya sa ake kiranta sandar Girma kuma shi ya sa ta shiga cikin ala ta kowace Masarauta.
Waɗannan su ne kayayyakin Ala ta Kano, kuma duk Sarkin da aka yi a Kano waɗannan su ne abinda ya ke gada kuma da su ne za ka shaida Sarkin Kano a ko ina, koda kuwa taron Sarakuna ne suke zaune za ka iya shaida Sarkin Kano in ka dubi ƙafarsa kaga takalmin gashin Jimina ko idan yana tafiya ka ganshi riƙe da tagwayen masu ko kwari da baka.
Masarautar Rano da Alar Sarautar Kano
Lokacin da aka yanke Masarautar Ringim daga Kano, Sarkin Ringim ya fara amfani da Tagwayen Masu, ganin cewa shi ma tsatson Gidan Dabo ne, saboda jikan Sarkin Kano Usman ne, to amma saboda ganin idan an kyaleshi ya ci gaba da amfani da shi to ba shakka wannan Alar ta Kano za ta samu tasgaro babba, wannan dalilin ya sa a lokacin Sarkin Kano Ado Bayero ya yi masa magana a kan ya yi haƙuri saboda a kare al’adar. Haka a zamanin Sarkin Kano Sanusi II shi ma a wannan lokacin Sarkin Ringim ɗin ya sake sabon yunƙurin riƙe Tagwayen Masun, a wannan lokacin ma Sarkin Kanon ya yi masa magana a kan ya yi haƙuri, ba don bai gada ba, sai don a kare alar Masarautar Kano.
Bayan Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sake yanka Masarautar Kano zuwa gida biyar, ya ƙara masarautu gudu hudu: Bichi da Gaya da Ƙaraye da kuma Rano a shekarar 2019. Sarkin Rano ya fara saka wannan takalmi na gashin jimina, wanda hakan abu ne da zai saka mutum cikin ruɗani. Domin alar Kano ce ba ta Rano ba. Hakan zai iya saka mutane tunanin cewa shin Sarkin Rano ma Magajin Rumfa ne? Mu ɗauka cewa, Sarkin Rano Magajin Rumfa ne, koda hakan ne babu wata hujja da zai saka Takalmin Gashin Jimina in ba shi ne ya gaji gidan Rumfar ba. Misali Sarakunan Bichi ba su taba amfani da wannan takalmi ba in ba sun shigo Gidan Dabo ba, k**ar yadda muka gani a wajen Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, har ya bar Ƙasar Bichi a matsayin Sarki bai taɓa amfani da Tagwayen Masu ko Takalmin Gashin Jimina ba .
Wannan ya yi nuni da cewar in har Sarkin Rano ya ci gaba da saka Takalmin gashin Jimina, babu abinda zai hana Sarkin Bichi ya saka ko ya riƙe Tagwayen masu, haka shi kanshi Sarkin Ringim babu abinda zai hana shi riƙe Tagwayen masu ko saka Takalmin gashin Jimina. Sarkin Kano murabus, shi ma babu abinda zai hana masa saka Takalmin gashin Jimina ko ya riƙe Tagwayen masu, saboda daman sun haramta a gareshi ne saboda suna cikin kayan Alar Masarautar da ya bari. To idan kuwa alar ta rushe babu abinda zai hanashi yin amfani da su.
Ina mai bada shawara cewar ya k**ata waɗanda abin ya shafa su yi duba cikin wannan al’amari su samar da mafita tin kafin salwantar alar Masarautar Kano. Allah ya kare mana Masarautunmu da mutuncin sarakunanmu gaba ɗaya.