Fresh Media Garden

Fresh Media Garden Domin samun ingantattun labarai acikin harshen Hausa da Turanci da Larabci har da Faransanci. Babu shaci fadi acikin labaranta

02/08/2026

Ɗaya daga cikin kasuwannin kan iyaka dake jamhuriyar Nijer a wani gari kenan a wata jaha daga cikin jihohin arewa maso yamma. Wane gari ne kuma a wace jaha?

02/08/2026

Wace kasuwa ce wannan kuma a wane gari da jaha take daga cikin jihohin da s**a yi iyaka da Nijer?

31/07/2026
22/07/2026

FRSC Launches 'Operation Fushin Zuma' to Curb Road Crashes During Rainy Season - Commander AH Ibrahim By Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina ...

FRSC TA KADDAMAR DA 'OPERATION FUSHIN ZUMA' DON RAGE HADURRA A LOKACIN DAMINA - Kwamanda Ali HannaDaga Kabir Ahmed S/Kuk...
22/07/2026

FRSC TA KADDAMAR DA 'OPERATION FUSHIN ZUMA' DON RAGE HADURRA A LOKACIN DAMINA - Kwamanda Ali Hanna
Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina
Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Katsina ta kaddamar da wani shiri na musamman mai suna "Operation Fushin Zuma" domin rage yawan hadurran da ke faruwa a lokacin damina.
Kwamandan hukumar a Jihar Katsina, Aliyu Hanna Ibrahim, ya bayyana hakan a lokacin wata hira ta musamman da ya yi da wakilinmu a ofishinsa da ke harabar Sokoto Rima, cikin birnin Katsina.
A cewarsa, an bullo da wannan shiri ne bisa umarnin babban Kwamandan hukumar na kasa, Alhaji Shehu Mohammed, bayan lura da cewa yawan hadurra na karuwa a lokacin damina a fadin kasar nan.
"Babban Kwamandan kasa ya ga dacewar a bullo da wani shiri na musamman a fadin kasa baki daya domin dakile afkuwar hadurra a damina. Don haka aka kasa kasar zuwa shiyyoyi 12 domin aiwatar da aikin. Jihar Katsina tana karkashin Shiyya ta 1, wacce ta hada da jihohin Kano, Jigawa, Zamfara da Kaduna a matsayin hedkwatar shiyyar," inji Kwamandan.
Aliyu Hanna ya jaddada cewa manufar sintirin ba don takurawa al'umma ba ne, illa don wayar da kan masu ababen hawa kan matakan kiyayewa da ya kamata su dauka.
"Wannan aiki da muka fito da shi ba don takurawa al'umma ba ne, a'a, don su san abin da ya kamata su yi a lokacin da suke kan ababen hawansu, wanda idan ba a yi hankali ba zai iya janyo mummunan hadari da zai yi sanadin rasa rayuka," inji shi.
Ya lissafa wasu muhimman abubuwa da direbobi ya kamata su kula da su, da s**a hada da:
Tabbatar da goge ruwan gilashi (wiper) na aiki a lokacin ruwa, da tabbatar da ingancin tayoyin abin hawa, ba tsofaffi ko kwararrun ba, da kuma tabbatar da fitilun mota na aiki yadda ya kamata saboda karancin gani a lokacin ruwa. Haka kuma akwai bukatar rage gudu domin samun saukin tsayawa idan an taka birki.
Kwamandan ya ce a yayin wannan sintiri, jami'an hukumar na tsayar da motoci ba wai don direba ya karya doka ba, har ma da nufin jan hankalinsa kan lafiyarsa da ta sauran al'umma.
Ya ce akwai wasu laifuffuka da hukumar za ta dauki mataki a kai tsaye a lokacin sintirin, kamar yin lodi fiye da kima, rashin sanya hular kwano ga masu babura, da kuma yin overtaking a wuri mai hadari.
Dangane da ingancin taya, Kwamandan ya yi gargadi: "Batun taya na da matukar muhimmanci. Ya kamata a rika sayen nagari ba takumbo ba. Kuma a rika lura da wa'adin da taya ke yi, wanda mafi yawa shekaru hudu ne. A jikin taya ana rubuta satin da aka kera ta. Misali, idan aka rubuta 05/26, ma'anar sa an kera ta a sati na 5 na shekarar 2026. Yana da kyau masu ababen hawa su rika lura da wannan."
Haka kuma, ya ja hankalin masu tafiya a gefen t**i da su rika tafiya ta yadda za su rika ganin abin hawa da ke tunkarar su, domin samun damar kaucewa cikin sauki idan wani abu ya faru, maimakon juya masa baya.
A karshe, Kwamandan ya yabawa al'ummar Jihar Katsina bisa hadin kai da goyon bayan da suke ba hukumar, tare da godewa Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, bisa ci gaba da tallafawa ayyukan hukumar.

ƘUNGIYAR MASU SAYAR DA DABINO TA NEMI GWAMNATIN JAHAR KATSINA TA BASU FILI NA DIN-DINDINShugaban ƙungiyar masu sayar da ...
17/07/2026

ƘUNGIYAR MASU SAYAR DA DABINO TA NEMI GWAMNATIN JAHAR KATSINA TA BASU FILI NA DIN-DINDIN
Shugaban ƙungiyar masu sayar da dabino na jahar Katsina Alhaji Sama'ila Ibrahim ya roƙi gwamnatin jahar da ta samar masu da fili na din-dindin a cikin babban birnin jahar domin gudanar da sana'ar su tare kuma da kafa ƙananan masana'antun sarrafa dabinon da kuma gina ofis. Kamar yadda ya ce, a lokacin da shugabannin ƙungiyar s**a kai ziyarar bangirma da sada zumunci ga shugaban ƙaramar hukumar Katsina Honarabil Isa Miqdad AD Saude a ranar Alhamishin makon jiya.
"Wannan ƙungiya na mai shaida maka cewar, a yanzu jahar Katsina na cikin sahun masu haɓaka wannan sana'a ta sayar da dabino wadda kuma ke taimakawa wajen baiwa matasa aiyukan yi maimakon zaman kashe wando. Akan haka muke neman goyon bayan gwamnati domin cimma waccan manufa. Muna fata, shugaba zaiyi mana jagora domin kai irin wannan ziyara da kuma ƙara mika ƙoƙon barar mu ga shi Maigirma Gwamna Malam Dikko Umar Radda. A ƙarshe, muna addu'ar samun zaman lafiya ga wannan jaha tare da fatan ci gaba da samun ƙaruwar arziki".
A nashi jawabin, shugaban ƙaramar hukumar Katsina Honarabil Isa Miqdad bayan ya nuna farin cikin shi akan wannan ziyara, ya kuma tabbatarwa da 'yan ƙungiyar goyon bayan shi gare su, kamar yadda yace su ma sun nuna mashi goyon baya tare da zabar shi har ya zauna a bisa wannan kujera ta shugabanci. Shugaban ya ƙara da cewa, zaiyi iya ƙoƙarin shi na ganin ya ja su har zuwa ofishin Gwamna tare kuma da yi masu jagoranci don ganin sun samu wannan fili a lokacin da s**a sake miƙa kokon barar ta su a gaban shi mai girma Gwamna. Honarabil Miqdad ya ƙara shaida masu cewar kofar ofis nashi a bude take gare su a duk lokacin da suke son ganin shi. A ƙarshe ya ƙara jaddada kira gare su da su cigaba gwamnati goyon bayan domin ganin ta aiwatar da aiyukan alherin da take yi ga al'umma.

Waiting for your adverts, works and related areasMuna jiran tallace-tallacen ku, wani aikin ko abin da ya danganci wanna...
16/07/2026

Waiting for your adverts, works and related areas
Muna jiran tallace-tallacen ku, wani aikin ko abin da ya danganci wannan sashe

GOVERNOR RADDA AND THE SECURITY SITUATION IN KATSINA STATEBy Kabir Ahmed S-KukaBackground: How Banditry Entered KatsinaT...
15/07/2026

GOVERNOR RADDA AND THE SECURITY SITUATION IN KATSINA STATE
By Kabir Ahmed S-Kuka
Background: How Banditry Entered Katsina
The root of the banditry crisis in Katsina State, often blamed on cattle rustlers of Fulani origin, can be traced to an influx of displaced persons.
If we look back at the early stages of insecurity in Katsina, what was then reported as a problem of Zamfara and Sokoto States found its way into Katsina through refugees. During the administration of Governor Aminu Bello Masari, displaced persons entered Katsina from Tsafe Local Government Area of Zamfara State, which shares a border with Katsina.
They settled in areas such as Hayin Alhaji and Bedi in Yankuzo, Baurawa, Takare, Salihawa, Danmarke Z, Runji, Zangon Pauwa, Dansabau and other communities in Kankara Local Government.
At that time, figures such as Buharin Daji and one Dan Bannawa Mai Darek - believed to be the first bandit to grant an interview on social media claiming to possess an anti-aircraft gun - were active. They collaborated in acts of terror, mainly killings and cattle rustling. Kidnapping for ransom had not yet become prevalent.
According to our investigation, the arrival of these displaced persons was the entry point for bandits into Katsina.
Sources disclosed that when the displaced persons arrived in the Kankara area, the Katsina State Government under Governor Masari and prominent businessman Alhaji Dahiru Mangal provided them with food, blankets and other relief materials. Unknowingly, among the displaced persons were criminals who had disguised themselves to conduct surveillance. This marked the beginning of banditry in the state. While farmer-herder clashes were an old, annual occurrence, this new dimension was different.
The problem gradually spread, especially from the Kankara axis. As it escalated and with the Federal Government appearing to treat it as less critical than the Boko Haram insurgency, the Masari administration sought to negotiate with the armed groups.
How Two times Peace Deals Were Done
The Katsina State Government negotiated with bandits twice, but both efforts eventually collapsed.
The first peace deal under Governor Masari was held in Kankara. All aggrieved parties were invited. The bandits presented Buharin Daji as their representative, even though he was not an indigene of Katsina State, because they were all engaged in the same activity. The meeting was held on 15th January, 2017 in Dansadau.
During that deal, some bandits surrendered their weapons, which were later destroyed at the Polo Ground in Katsina after being inspected at the Army Barracks in Katsina.
The second deal was held in Lambar Rimi, on the border between Batsari and Zamfara. In a bid to ensure lasting peace, Governor Masari's efforts went beyond entering forests to dialogue with bandits and procuring armoured vehicles for security agents; it extended to engaging the neighbouring Republic of Niger, specifically Maradi Region, after observing that some cattle owners came from that axis. Like the first, the second peace accord also failed to yield lasting results.
The Worst Attacks
Among the numerous attacks carried out by bandits, a few stood out for their brutality. The first was in Yar Gamji village in Batsari Local Government, where more than ten farmers were slaughtered.
The second was the attack on Kadisau in Faskari Local Government. According to one of the attackers who spoke to journalists at the Katsina State Police Headquarters, the attack was organized by Adamu Aleru. About 450 motorcycles were used, each carrying three persons. Following that attack, the Katsina Police Command placed a bounty for information leading to the arrest of Adamu Aleru, who claimed he launched the attack to secure the release of his son who had been arrested.
Another horrific incident occurred in Tsauwa village, also in Batsari LGA, on 5th July, 2021. More than half of the village was burnt down. Victims were burnt beyond recognition. Four deaths were particularly disturbing: a pregnant woman, a nursing mother who had covered her children with her wrapper, children hidden inside a granary for safety, and an ailing man over 70 years old with the boy caring for him, all were burnt to ashes.
High-Profile Kidnappings
Our investigation by FRESH MEDIA GARDEN identified several kidnappings that shocked the public.
The most prominent was the abduction of nearly 400 students of Government Science Secondary School, Kankara, on 11th December, 2020. The attack was led by a bandit leader, Auwalu Daudawa. The students were released on 18th December after prolonged negotiations. Daudawa himself was killed in April 2021 during a clash among rival bandit groups after he allegedly abandoned the peace deal and stole cattle belonging to another group that later killed him - a fate similar to Buharin Daji.
The second notable case was the kidnap of Governor Masari's mother-in-law while he was in office. The operation was led by a youth known as Yalo, an indigene of Katsina town who became an informant for the forest Fulanis. After his arrest, he confessed at the Police Headquarters that he received N1.5 million out of the N30 million allegedly paid as ransom. The victim later regained her freedom.
The third was the abduction of Governor Dikko Umar Radda's brother, who is the Magajin Garin Radda. The most recent was the kidnap of late retired Major General Rabe, who died in the hands of his abductors.
Radda's Approach: No Negotiation With Bandits
Upon assuming office, Governor Malam Dikko Umar Radda made his position clear: his administration will not negotiate with bandits.
He stated that "there is no reason to negotiate with someone who does not keep trust. However, government will accept anyone who genuinely repents and embraces peace on his own volition", said Radda.
The declaration surprised many, given the failure of previous negotiations by his predecessors. But Radda came out directly to confront the bandits rather than seek reconciliation.
Establishment of Community Watch Corps (CWC)
Through strategic thinking and with divine help, Governor Radda introduced a new approach. His major initiative was the establishment of the Community Watch Corps (CWC). Personnel of the CWC were recruited from the local government areas most affected by insecurity and given special training. Governor Radda procured vehicles and motorcycles for the Corps. After training and graduation, each operative was deployed to his own community to protect his people.
This strategy has significantly reduced attacks. It is estimated to have curtailed insecurity by 70 to 80 percent. To date, the operatives continue to record successes despite facing challenges. According to reports, their monthly allowance was initially N30,000 and has now been increased to N50,000.
One of the challenges they face is informants who leak information to bandits. When such informants are arrested, their relatives often protest and even mount pressure for their release. The training and equipping of the CWC has been done twice, and successes are still being recorded.
Support For Victims
Even before becoming Governor, when he was Director General of SMEDAN, Malam Dikko Radda was the first top official from Katsina to visit victims of bandit attacks in Batsari. He provided bags of food items and cash to sympathize with them. The items were delivered through the Sarkin Ruma, the District Head of Batsari.
As Governor, Radda created the Ministry of Internal Security and Home Affairs to tackle insecurity. He also established a special office under the Special Adviser on Victims of Banditry to provide support.
In almost all affected LGAs, victims who sustained injuries, suffered severe losses, or families of those killed who left orphans behind have been supported to cushion their pains. Even security operatives, including soldiers who died or were injured, and their families, have received support or sponsorship from Governor Radda. He also took responsibility for the medical bills of all those injured by insecurity until full recovery.
The Governor also personally visits communities attacked by bandits to commiserate, despite his busy schedule. Where he cannot go himself, he sends a delegation.
Success or Failure?
The first indicator of success under Governor Radda is that roads abandoned for years due to insecurity are now being used safely. For example, the Katsina-Jibiya road, Katsina-Batsari road and other routes that were deserted from early morning and evening are now in use. At the height of the crisis, transport unions banned their members from plying those roads at certain times. Due to the Governor's determination, those major challenges have now become history. Markets, road travel and other activities thought to be permanently lost have resumed.
With no major breakthrough and with prayers, the bandits themselves have now sought peace with communities to end hostilities. The initiative started from Batsari Local Government without government involvement. One Abu Radde led the peace move from the bandits' side, as confirmed by a resident, Alhaji Hassan Dogon Faci, and peace has since prevailed in the area.
After Batsari, peace was initiated in Jibiya where one Abdu Lankai represented the bandits, and according to Alhaji Surajo, Chairman of the Jibiya Security Committee, no major problem has been recorded since, in an interview with our correspondent. Similarly, in Danmusa LGA, Alhaji Umar, popularly known as Minori, led the peace effort, and peace is also being enjoyed there as confirmed by the Chairman of the Security Committee, Alhaji Salisu Buhari.
Our investigation confirms that about 90 percent of communities whose residents fled have returned home and resumed farming. For instance, communities such as Birnin Kogo, Yankara and others in Faskari have resumed peaceful coexistence.
"If we are to be sincere to ourselves, we will say this is no small achievement brought by Allah during Governor Radda's tenure," said Alhaji Rabi'u.
Challenges Remain
Despite these successes achieved with relative ease, there are still challenges. Governor Radda himself has expressed concern that some people are sabotaging his administration's security efforts. Wherever success is recorded, some elements attempt to undermine it. Such was the case in Jibiya which led to loss of lives.
Currently, the Matazu-Musawa axis has become a death trap due to the atrocities of a bandit known as Kacalla Maha, who abducted the late Major General Rabe who died in his custody.
"I don't blame Governor Radda because he does not control any security agency except the CWC he established. Everyone knows where the problem lies. We ourselves are also to blame because we see informants among us but cannot expose them out of fear, forgetting that it is that information they use to kill us," said Abdulkarim Kabir.
Another resident who pleaded anonymity said the Governor's fault, in his view, was disarming local vigilantes who were defending themselves while leaving bandits armed.
"An example is Sayaya. If people were allowed to keep their self-defense weapons, this boy wouldn't have terrorized the area. So the Governor should order that wherever people's defensive weapons were collected, they should be returned if the matter is not yet over. But you disarm the defender and leave the attacker armed, no amount of justification will end the problem. The weak are always the victims," he said.

Address

Dutsin Safe Lowcost Jibia Road
Katsina
820261

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fresh Media Garden posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share