25/06/2025
Hukumar NBTE ta amince da makarantar koyon Sana,oi ta Katsina Youth Craft Village (KYCV) ta zama cibiyar horas da matasa tare da bada satifiket
Hukumar kula da ilimin fasaha ta ƙasa (NBTE) ta amince da Katsina Youth Craft Village a hukumance a matsayin cibiyar bayar da horo karkashin tsarin National Skills Qualifications (NSQ).
Wannan amincewa na kunshe ne a cikin wata takarda da Sakatare Janar na NBTE, Farfesa Idris M. Bugaje, ya sanya wa hannu, bayan nasarar binciken kayan aiki da ingancin horo da hukumar ta gudanar.
Da wannan ci gaba, Katsina Youth Craft Village dake da rassansa a Katsina da Malumfashi, yanzu zata rika horar da matasa a fannoni daban-daban kamar ink
Gyaran motoci, aikin kafinta, gyaran kwamfuta, gyaran jiki (cosmetology), girki da hidimar abinci, dinkin kaya, kera takalma da jikkuna da Sauran kayayyaki na fata, gini, gyaran wayoyin hannu, daukar hoto da fina-finai, aikin famfo, walda, da gyaran na’urorin tauraron dan adam (satellite).
NBTE ta bayyana cewa wannan amincewa ta fara aiki daga 24 ga Yuni, 2025, tare da buƙatar cibiyar ta yi rajista da hukumomin bayar da takardar shaidar NSQ bisa kowane fanni.
Gwamnan Jihar Katsina,Mal Dr Dikko umaru Radda ya taya cibiyar murna bisa wannan nasara.
Acewar Gwamnan Wannan wata babbar nasara ce ga jihar Katsina, kuma ta tabbatar da kudirinmu na samar da sana’o’in dogaro da kai ga matasa, tare da buɗe masu ƙofofin arziki a matakin ƙasa.
Shi ma Injiniya Kabir Abdullahi , shugaban cibiyar, ya bayyana wannan ci gaba a matsayin wani tarihi ne da ya dace da hangen nesa na Gwamna Radda na karfafa matasa da basu sana’o’in da zasu dogara da kansu da kuma samar da ayyukan yi.
Kuma Ya tabbar da cewa wannan mataki yana daga cikin muhimman manufofin gwamnatin jihar Katsina karkashin shuganchin Dikko Radda na gina rayuwar matasa da rage rashin aikin yi a jihar Katsina.
Sakon APC MEDIA LEADS Katsina