02/09/2026
Kana Ci Gaba da Zama Amintaccen Jagora Wajen Gina Ƙasa” — Gwamna Radda Ya Taya Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Murnar Cika Shekara
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ya taya Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, GCON, murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya bayyana shi a matsayin amintaccen jagora wajen gina ƙasa wanda ƙwarewarsa, jajircewarsa da sadaukarwarsa wajen hidimar jama’a ke chigaba da bayar da gagarumar gudummawa wajen ci gaban Najeriya.
Gwamna Radda ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kafa tarihi mai ɗorewa na hidimar jama’a, tun daga lokacin da yake jagorantar Jihar Borno har zuwa matsayinsa na yanzu, inda yake taimaka wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wajen tafiyar da harkokin mulkin ƙasar nan.
A cewar Gwamna Radda nutsuwar Mataimakin Shugaban Ƙasar, fahimtarsa kan muhimman batutuwan ƙasa da kuma iya mu’amalarsa da mutane daga sassa daban-daban, yana daga cikin kyawawan halayen da s**a taimaka masa wajen sauke nauyin dake kansa.
Gwamna Radda ya kuma yaba wa Sanata Kashim Shettima bisa kulawarsa da al’amuran da s**a shafi Arewacin Najeriya, musamman ƙoƙarin ƙarfafa tsaro, bunƙasa noma, jawo jarin zuba jari da samar da damammaki ga matasa.
Ya ƙara da cewa shugabancin ƙasa na buƙatar haƙuri, kyakkyawan tunani da kuma shirye-shiryen yin hidima ga al’umma ba tare da fifita muradun kai ba, yana mai cewa Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ci gaba da amfani da ƙwarewarsa wajen yi wa Najeriya hidima.
Gwamna Radda, a madadin Gwamnati da al’ummar Jihar Katsina, yana taya Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, murnar zagayowar ranar haihuwarsa, tare da yi masa fatan ƙarin shekaru masu albarka, lafiya da kuma ci gaba da samun nasarar hidima ga ƙasa.