Northern Media Leads

Northern Media Leads Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Northern Media Leads, No 140 Nagogo Road Kofar Durbi katsina, Katsina.

Wata babbar tawaga mai ƙarfi ta Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kai ziyara a ranar Lahadi zuwa al’ummomin Esiele da Yawot...
01/06/2026

Wata babbar tawaga mai ƙarfi ta Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kai ziyara a ranar Lahadi zuwa al’ummomin Esiele da Yawota da ke Ƙaramar Hukumar Oriire a Jihar Oyo, domin jajanta wa al’ummar yankin tare da duba halin da ake ciki bayan sace ɗalibai da malamai da aka yi daga makarantu daban-daban a ranar 15 ga Mayu, 2026.

Makarantun da lamarin ya shafa sun haɗa da:
• Community Grammar School (Makarantar Sakandaren Al’umma),
• Baptist Nursery and Primary School (Makarantar Firamare da Gandun Yara ta Baptist),
• L.A. Primary School (Makarantar Firamare ta L.A.).

Ziyarar tawagar gwamnatin tarayyar ta zo ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnati na bibiyar lamarin, jajanta wa iyalai da al’ummomin da abin ya shafa, tare da tabbatar da cewa jami’an tsaro suna ci gaba da ɗaukar matakan da s**a dace domin ceto waɗanda aka sace da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.

Har ila yau, tawagar ta gana da shugabannin al’umma, iyayen yara da malamai, inda s**a tattauna kan yadda za a ƙara ƙarfafa tsaro a makarantu da kuma hana sake aukuwar irin wannan mummunan lamari a nan gaba. Ziyarar ta nuna damuwar Gwamnatin Tarayya da kuma aniyarta na tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin ƙasar nan.

01/06/2026

Kalmomin falsafa da Sarki Sanusi II yayi a jawabinsa ga gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Lamarin tsaro a jihar katsina da Najeriya wankin hula yana Neman Kai Gwamnatin Dikko Radda dare duk da tsohon major da a...
01/06/2026

Lamarin tsaro a jihar katsina da Najeriya wankin hula yana Neman Kai Gwamnatin Dikko Radda dare duk da tsohon major da aka sache Sun biyo shi ne daga jihar kaduna suna ta bada bayanan shi Amma basu samu sa,ar k**ashi ba saida yazo chikin jihar katsina,

Lamarin Garkuwa Da Major General Rabe Abubakar Yana Cigaba Da Ɗaukar Hankalin Al,umma kuma sunata musayar ra,ayoyi akan wannan ta,addanchi da har jami,an tsaro ba,a bari ba

Wato lamarin harkar samar da tsaro a fadin Najeriya yana ta ɗaukar wani sabon salo kai kace wani wasan kwaikwayo akeyi.

Harkar tafiye tafiye a ƙasar nan sai dai kawai kayi neman kariyar Allah ka k**a hanya, duk inda zaka babban abinda yake tada tada hankali shine yadda aka bayyana cewa ana bibiyar tafiyar wadannan bayin Allah tun daga Kaduna har zuwa Katsina.

Bama iya wannan ba hatta lokacin da s**a zo marabar Musawa an bayyana cewa wai anga driver din yana nazari ko yabi ta Gidan mutum ɗaya ko kuma ya shiga ta marabar Musawa wanda a karshe s**aga yano hanyar musawa matazu,

Shigar Su wannan hanya ta baiwa yan ta,addanchi damar bada chikakken bayanin inda zasu tare su domin sachewa Wanda kuma dama kudi run su kenan ,

Abun tambaya anan tun daga kaduna babu inda s**aga ya dache ko kuma babu inda zasu iya Sache shi sai da aka shigo jihar katsina kuma a titin da yayi kaurin suna wanda ake fadin akwai kauyukan da suke da barayi da dama Wanda dukkanin barayin da suke jagorantar dabar yan bindiga iyayen su na wadannan kauyukan

Abunda ya rage gwamnati ta sanya ido a wadannan kauyukan da Al,ummar dake chikin su domin tantanchewa a gane na kirki agane yan ta,adda

31/05/2026

Yayin Da Guguwar Siyasa Ke Kara Tasowa, Hukumar NDLEA a Jigawa, Na Kan Bakanta Na Kwace Dukiyoyin Duk Wanda Aka Samu da Hannu Wajen Dillancin Kayan Maye. BBC Hausa BBC Isma'il Muhammad

Shekara ukku da hawan karagar Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan jihar Kano Riba ko faduwa a wannan mulkin
29/05/2026

Shekara ukku da hawan karagar Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan jihar Kano
Riba ko faduwa a wannan mulkin

Gwamna Dikko Umaru Radda  yau 29 ga watan may yake chika shekara ukku  dai dai  akan karagar  mulkin  jihar katsina wane...
29/05/2026

Gwamna Dikko Umaru Radda yau 29 ga watan may yake chika shekara ukku dai dai akan karagar mulkin jihar katsina wane bangare aka samu chigaba wane bangare Al,ummar katsina suke da shawara domin yin gyara kafin ya sake dawowa Neman kuri,a kashi na

Shawarar ku Tana matukar Amfani domin gyara

28/05/2026

Daga jihar katsina wajen bikin hawan sarki inda sarki yake kaima gwamna ziyara a gidan gwamnati

26/05/2026

Dalilina nayima jam'iyyar PDP Addua Allah wargazata - Prof Isah Ali Pantami

EFCC ta mika tsohon Ministan Lantarki, Saleh Mamman, gidan yari domin fara zaman hukuncin shekaru 75Hukumar Yaƙi da Cin ...
26/05/2026

EFCC ta mika tsohon Ministan Lantarki, Saleh Mamman, gidan yari domin fara zaman hukuncin shekaru 75

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa a Nijeriya (EFCC) ta mika tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, zuwa Gidan Gyaran Hali na Kuje da ke Abuja domin fara zaman hukuncin daurin shekaru 75 da kotu ta yanke mashi,

Hakan ya biyo bayan umarnin da Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama, Abuja, ya bayar a ranar Talata, bayan gabatar da Mamman a gaban kotun da EFCC ta yi.

kotun ta kuma saurari bukatar EFCC na kwace wasu karin kadarori guda biyar da ake zargin suna da alaka da Mamman, ciki har da gidaje da otel-otel da ke Abuja da garin Kaduna,

Address

No 140 Nagogo Road Kofar Durbi Katsina
Katsina

Telephone

+2347032043337

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Northern Media Leads posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Northern Media Leads:

Share