05/05/2015
salam kawaye,
kamar dai yadda kuka sani shirin kawaye, shiri ne da yake magana akan matsalolin kawaye, tsakanin ki da Mijin ki,saurayin ki,abokiyar zaman ki,surukanki
da makwabtan ki, dama dukkan rayuwarki gaba daya...
zamu rika kawo maku sakonnin da kawaye suke turowa domin tattaunawa akai da basu shawara akai. Kuma zamu rika turo maku lokacin da muke gabatar da shirin kai tsaye a gidan radion vision FM 92.1ktn, domin ku bada taku gudumuwar acikin shirin. Haka kema kawa idan kinada taki matsalar, zaki iya turowa anan. insha Allah zamu dubata domin kawaye su baki shawara. nagode