Zawiyyar Sheikh Ibrahim Kaya Kaura Namoda

Zawiyyar Sheikh Ibrahim Kaya Kaura Namoda Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Zawiyyar Sheikh Ibrahim Kaya Kaura Namoda, Media/News Company, Kaura-Namoda.

*((( ZAWUYYAR SHEHU IBRAHIM KAYA )))*
A madadin *Maulana Khalifa Muhammad Nasir Ibrahim Kaya,* da dukkan "yan'uwa Muridan wannan Zawiyya, muna taya Dan'uwa *SI.Muntaka Lukman* murnar samun karin girm

((( ZAWIYYA SHEHU IBRAHIM KAYA ))) *إنا لله وإنا إليه راجعون !!!* Bisa jemame da bayyana alhini, a madadin Maulana Khali...
05/12/2022

((( ZAWIYYA SHEHU IBRAHIM KAYA )))
*إنا لله وإنا إليه راجعون !!!*
Bisa jemame da bayyana alhini, a madadin Maulana Khalifa, muna sanarda "yan'uwa Allah mai iko akan komai, mai bayarwa mai karba a duk lokacin da yaso, ya karbi Babban Limamin wannan Zawiyya, *Liman Lauwali Imamu Idris yanzunnan* , za'a yi janazar sa 2:30 In Sha Allah, anan Babbar Zawiyyar Shehu Ibrahim Kaya.
Muna fatar Allah ya jaddada masa rahama.
*Sanarwa: Maimagana da yawun Zawiyya amadadin Khalifa.*

22/09/2022

*((( ZAWIYYAR SHEHU IBRAHIM KAYA )))*
A madadin Iyalai da Almajirai na *Maulana Shehu Ibrahim Kaya R.A* na gayyatar dukkan "yan'uwa, zuwa Dauren Auren *Maulana Khalifa Muhammad Nasir Shehu Ibrahim Kaya.*
Daurin Auren zai kasance In Sha Allahu kamar haka:
*Rana:* Gobe Jumu'a 23/09/2022.
*Wuri:* Tudun Wada, kusa ga gidan Alh Namakka Super Market.
*Lokaci:* 7:30 na safe.
Allah ya bada ikon zuwa, wanda yake nesa yayi Addu'a.
*Announcer: Zawiyya Spoke Parson*.

27/08/2022

*((( ZAWIYYAR SHEHU IBRAHIM KAYA )))*
A madadin Maulana Khalifa Muhammad Nasir Shehu Ibrahim Kaya, na gayyatar dukkan Members na wannan Zawiyya, da masu yi muna fatar Alkhairi, Addu'ar zanen sunan Diyar da aka haifawa Dan'uwa *Barrister Naziru Lukman,* Addu'ar zata kasance In Sha Allahu kamar haka:
*Rana:* Gobe Lahadi 27/08/2022.
*Wuri:* Zawiyya.
*Lokaci:* Da safe kamar yanda aka saba.
*Sign: Mai Maimagan da yawun Zawiyya.*

*((( ZAWIYYAR SHEHU IBRAHIM KAYA ))]* A madadin Maulana Khalifa da dukkan "yan'uwa Muridan wannan Zawiyya, da sauran mut...
26/08/2022

*((( ZAWIYYAR SHEHU IBRAHIM KAYA ))]*
A madadin Maulana Khalifa da dukkan "yan'uwa Muridan wannan Zawiyya, da sauran mutanen unguwa da makwabta, muna mika sakon godiya ga Hon.Dr. Aminu Sani Jaji da " yan Kwamitin sa, akan gyara muna rijiyar murtsatsemmu da kenan Zawiyya, inda aka canza dukkan sandunan da ke jawo ruwa, da sauran wasu muhimman kaya.
Muna fatar Allah ya saka da Alkhairi.
*Sing: Maimagana da yawun Zawiyya.*

24/08/2022

*((( ZAWIYYAR SHEHU IBRAHIM KAYA )))*
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN.
A madadin Maulana Khalifa, muna sanarda dukkan "yan'uwa Allah ya yiwa daya daga cikin Muridan wannan Zawiyya, kuma hadin Shehu na cikin daki alokacin zaman Kaya, *HAKIMI DAN-DUMFAWA* rasuwa yau da safe, za'a yi janazar sa anjima da karfe 4:30 anan Zawiyya.
Allah ya gafar ta masa ya sada shi da masoyin sa.
*Sign: Maimagana da yawun Zawiyya.*

20/08/2022

*((( ZAWUYYAR SHEHU IBRAHIM KAYA )))*
A madadin *Maulana Khalifa Muhammad Nasir Ibrahim Kaya,* da dukkan "yan'uwa Muridan wannan Zawiyya, muna taya Dan'uwa *SI.Muntaka Lukman* murnar samun karin girma a wurin aikinsa, a ma'aikatar shige da fice (Nigerian Immigration Service), a matsayin Supretendant.
Da fatar Allah ya kara daukaka, ya tsare dukkan abunki.
*Sign: Maimagana da yawun Zawiyya.*

28/07/2022

A madadin Maulana Khalifa, muna gayyatar dukkan "Yan'uwa zuwa Addu'ar sunan danda aka haifawa Malam Murtala Muhammad T.G.K, gobe Jumu'a anan Zawuyya kamar yanda aka saba.
*Sing: Maimagaba da yawun Zawuyya.*

03/05/2022

*((( ZAWUYYAR SHEHU IBRAHIM KAYA KAURA-NAMODA )))*
A cigaba da karbar ta'aziyya da barka da Sallah daga Zawuyyoyi masau talluki da wannan Zawuyya, da sauran dai-daikun jama'a, daga cikin Zawuyyoyin da s**a zo akwai:
1. Zauwwar Dumfawa karkashin jagorancin Khalifa Mandi.
2. Zawuyyar Nahuce, karkashin jagorancin Khalifa Salisu.
3. Zawuyyar Billashe, karkashin jagorancin Khalifa Almajir.
4. Zawuyyar Gidan Danzara, karkashin Malam Habibu.
5. Zawuyyar Faru, karkashin Khalifa Sulaiman Na'ibi.
6. Zawuyyar Dolen Moriki, karkashin jagorancin Khalifa Abubakar.
7. Zawuyyar Danguro, karkashin jagorancin Khalifa Labbo.
8. Zawuyyar Jambako, karkashin jagorancin Khalifa Ummaru.
9. Zawuyyar "Yankaba, karkashin jagorancin Khalifa Almajir.
Bayan gabatar da ta'aziyya da barka da Sallah, Khalifa ya yi godiya da yima su fatar cigaba da rike wannan Alkawali da yake tsakanimmu, ya yi fatar Allah ya maida su gida lafiya.
*Sign: Zawiyya Spoke Parson.*

03/05/2022

*((( ZAWUYYAR SHEHU IBRAHIM KAYA KAURA-NAMODA )))*
A madadin Maulana Khalifa da dukkan "yan'uwan sa, da sauran jama'ar Zawiyya, na mika sakon godiya da bangajiya ga Hon. Sani Umar Dan-Galadima, Dan Majalisa mai wakiltar Kaura da Birnin Magaji a Majalisar Tarayya, Wanda ya yo tattaki da kansa ya zo yayi ta'aziyya da barka da Sallah, bayan gabatar da ta'aziyya sun tattauna magangano a sirrance shi da Khalifa da sauran jagororin Zawiyya, muna fatar Allah ya saka da Alkhairi ya tabbatar da abubuwan.
*Sign: Zawiyya Spoke Parson.*

03/05/2022

*((( ZAWUYYAR SHEHU IBRAHIM KAYA KAURA-NAMODA )))*
A madadin Maulana Khalifa, na mika sakon godiya ga dukkan "yan'uwa da s**a sami damar halartar Janazar Dan'uwa Hassan, musamman:
1. Khalifa Muhammad G/Makaranta da jamar sa.
2. Khalifa Kabiru Usman da jamar sa.
3. Khalifa Atiku Maisuna da jamar sa.
4. Khalifa Imam Sani Kambarawa da jamar sa.
da wadanda s**a zo ta'aziyya ko sauka aiko, dama wadanda s**a bugo waya, Allah ya sakawa kowa da Alkhairi.
*Sign: Zawiyya Spoke Parson.*

01/05/2022

إنا لله وإنا إليه راجعون !!!
Muna sanar da "yan'uwa Allah ya yiwa kanin mu rasuwa, Hassan Na Khalifa Nasir, za'a yi janazar sa yanzu karfr 5:30 anan Zawiyyar Shehu Ibrahim Kaya, Allah ya jadda da masa rahama.

16/03/2022
16/03/2022
16/03/2022
Al-Marhoom Sheikh Ibrahim Kaya Kaura Namoda Zamfara State, Nigeria Shehin Dariqar Tijjaniya
16/03/2022

Al-Marhoom Sheikh Ibrahim Kaya Kaura Namoda Zamfara State, Nigeria Shehin Dariqar Tijjaniya

Address

Kaura-Namoda

Telephone

+2348082380911

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zawiyyar Sheikh Ibrahim Kaya Kaura Namoda posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share