05/02/2023
Ina neman alfarmar dukkannin abokaina na wannan dandalin da su zabi Alhaji Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasar Najeriya a zabe mai zuwa.
Bance Atiku Abubakar yafi kowa iyawa ba, ko kuma yafi kowa adalci ba, kuma ban baku tabbacin cewa lallai sai ya gyara Najeriya kamar yadda muka sa rai idan Buhari yahau mulki ba zai gyara ta.
Inada tabbaci da yakini Insha'Allah idan kuka zabi Atiku Abubakar ya zama shugaban kasar Najeriya na tabbata da zaran yahau mulki zai bude bododin Najeriya, wanda hakan zai jawo kayan abinci suyi sauki, kayan kamfanonin gida da na kasashen waje duk zasu yi sauki sosai.
Shinkafar waje, Taliya da sauran su zasu yi mugun karyewa, Insha'Allah Man Fetur zai wadata, za'a samu saukin rayuwa fiye da yadda muke tunani.
Sannan ina da yakinin zai cigaba da tono danyen Man Fetur dake Arewa kuma zai kara kaimi wurin bawa al-ummar Najeriya tsaro kuma Insha'Allah zai gudanar da manyan ayyukan cigaba wa 'yanda zasu amfani talakawan Najeriya.
Na tabbata iya wa 'yan nan ayyukan kadai idan Atiku Abubakar ya gudanar dasu talakawan Najeriya zasu ji dadi kuma zasu yi murna da kasancewar shi a matsayin shugabansu.
Dukkannin abubuwan da na fada wallahi ko baka son Atiku a cikin zuciyar ka, na tabbata kai kasan Atiku zai gudanar dasu duba da kasancewarshi gogaggen dan kasuwa kuma masanin farfado da tattakin arzikin Najeriya.
Bance lallai sai kun amshi rokona ba, nasan kowa nada nashi ra'ayin, amma idan kuka karbi rokona kuka zabi Atiku Abubakar ya zama shugaban kasar Najeriya Insha'Allah ba zai bamu kunya ba
✍️ Comr Abba Sani Pantami