24/08/2022
YANZU-YANZU: Gwamna Mai Mala Ya Cika Alkwarinsa Na Samarwa Biyu Daga Cikin 'Ya'yan Marigayi Sheik Goni Aisami Aiki
A bisa alkawarin da Gwamna Mai Mala Buni ya yi wa iyalan marigayi Sheik Aisami Goni, mukaddashin shugaban ma’aikatan gwamnati Alhaji Garba Bilal, ya gabatar da wasikun k**a aiki ga ‘ya’yan marigayi Malam Sheikh Babagoni Aisami.
Mai magana da yawun mukaddashin Shugaban ma"aikatan Jihar Yobe, Alhassan Sule Mamudo ya sanar da rahoton a hukumance asafiyar yau laraba, anyi taron ne a conference hall na HOS dage cikin garin Damaturu ajihar Yobe.
Alhaji Garba Bilal, ya ce a yayin gabatar da wasikun daukar aiki ga wadanda s**a ci gajiyar aikin, hakan zai kawo karshen wahalhalun da ake iya fuskanta bayan rasuwar malamin, sunan yaran marigayin sheik aisami goni akwai, sa'ad mohammed goni da fatsuma Ibrahim Shariff.
Idan dai za a iya tunawa gwamna Mai Mala Buni a ziyarar ta’aziyya da ya kai ga iyalan marigayi Sheik Goni Aisami, wanda aka kashe a ranar Juma’ar da ta gabata, a hanyar Nguru zuwa Gashua, yayi alkawarin bayar da aiki ga iyalan malamin da ake zargin jami'an sojoji ne s**a kashe shi.
Gwamna Mai Mala Buni kuma yadau alwashin ganin an hukunta wayenda s**a aikata wannan kisan k**ar yadda dokar kasa ta tanada.
Inda shugaban ma'akatan jihar yobe Alhaji Garba bilal yayiwa marigayi addu'a ubangiji Allah yajikanshi da rahama yakai haske kabarinsa muna idan tamu tazo Allah yasa mucika da Imani ameen ya Allah.
Rahoto daga
Hassan Peppe Gujba Special Assistant on Social Media to His Excellency Mai Mala Buni.