03/05/2025
ME YA FARU DA DR AHMED ISA?
Ana ta yada wasu labarai marar dadi akan Dr Ahmed Isa (Ordinary President) shahararren dan gwagwarmaya mai yaki da zaluncin azzalumai, wanda yayi kaurin suna wajen neman hakkin talakawa, wasu sunce an k**ashi an boye
Bayan na ga labarin, na dauki waya na kira wata aminiyarsa wanda ta hannunta nake waya da shi, ta tabbatar min ba'a k**a Dr Ahmad Isa ba, sai dai wani abu mak**ancin haka ya kusa ya faru, saboda azzalumai suna jin haushinsa
A halin yanzu Ahmed Isa yayi tafiya mai nisa kuma yana cikin aminci a gurin da yake, yana hutawa ne babu abinda ya sameshi sai alheri, zai dawo ya cigaba da gwagwarmaya ba da jimawa ba Insha Allah
Wannan bayani tabbaci ne nake baku dari bisa dari, ba'a k**ashi ba, yana cikin aminci
Muna rokon Allah Ya kareshi daga dukkan sharri da makirci