09/03/2023
*Hikimar zance:*
* Yawan jayayya alamace ta kin gaskiya.
* Yawan surutu alamace ta rashin kamala.
* Yawan kyauta alamace ta kauna.
* Yawan kawaici alamace ta mutuntaka.
* Yawan yafiya alamace ta daukaka.
* Yawan yabo alamace ta can-canta.
*Abun mamaki:*
* Idan za'a shiga Masallaci a kyauta ne, amma masu shiga 'yan kadan ne. * Idan za'a shiga gidan fasikanci biya ake, amma masu shiga suna da yawa. * Anya kuwa Jama'a ba barin Aljannah sukeyi kyauta ba, suna siyan wuta da kudin su? *Ka kyale mutum idan kaga yayi shuru:*
* Wani yayi shiru ne saboda lokacin maganar sa ne baiyi ba.
* Wani yayi shiru ne saboda yayi nazarin abun da zai fada.
* Wani yayi shuru ne saboda kawaici irin na sa.
* Wani yayi shuru ne saboda shine dacewa da shi.
*Kada ka dauka Addu'a makami kawai:*
* Makamice ga rago.
* Makamice ga mai karfi.
* Makamice ga Mumini.
* Cikin dare yake tashi ya wasa ta.
* Idan gari ya waye ya fara aikinta.
*Idan kana cikin damuwa mika lamarin ga Allah:*
* Sauraron waraka daga gurin Allah ibada ne.
* Kyautatawa Allah zato ibada ne.
* Yarda da duk wata Kaddra daga Allah ibada ce.
* Tabbas Allah shine mai yaye duk wata damuwa.
*Ka rabu da mutum kawai:*
* Domin shi mutum ba a iya masa.
* Kuma baza a iya masa ba har abada.
* Dan haka rabu da yabon mutum.
* Kawai ka nemi yabo a gurin Allah.
Ya Allah Kasa mu dace Duniya da Lahira,..🤲
Barka da juma'ah💖