18/05/2026
DA DUMI-DUMI: Kotu ta bayar da belin Nasir El-Rufai kan Naira miliyan 100
Wata babbar kotu da ke Abuja ta bayar da beli ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan zargin karan tsaye ga tsaron kasa da ake yi masa.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta bayyana cewa an bayar da belin ne kan kudi Naira miliyan 100, tare da sharadin cewa wanda zai tsaya masa dole ne ya kasance mazaunin yankin Maitama ko Asokoro da ke Abuja.