09/04/2023
Ko wa dai akwai kazar da sai ya fige da hannunsa
Ina ta mamakin wai har zuwa yanzu ana ta cece-ku-ce akan maganar yarinyar da ta yi kukan cewa tana kaunar wani kuma shi baya tare da ita. Ina gani bai dace ba a yi ta muzanta mata, saboda ta bayyana abunda ke ran ta, domin ba ta yi wani laifi ba. In kuma akwai wanda yake ganin ta yi laifi to ya gaya mana, menene hukuncin wannan laifin a hukumance ko a shariance?
Ya kamata mutane su gane cewa ita mace mutumce mai zuciya da hamkali kamar kowanne namiji, yadda namiji zai iya jin kaunar mace ta shige shi hakanan mace mace mai kan iya jin haka.
Hakanan kuma babu wani abun kunya ko zubar da aji ga mace ta bayyana kaunar ta ga namiji a Musulumce ko a zamanan ce. Asali ma Sayyadah Khadija ce ta nuna sha'awar ta ga auren Annabi SAW na farko kuma cikin shi ya samu yayan shi guda 6 duka. Sannan an samu mata da dama da s**a bayyana kaunar su gare shi SAW ya auri wasu ya kuma salami wasu da kalamai ma su dadi.
A fahimta ta, abun kunya da ke nuna alamar tawaya da rashin wayewar addini da zamani shine namijin da zai wulakanta mace saboda ta bayyana ma shi kauna. Wannan din shine kauyanci kuma rashin fahimtar addini da rayuwa ke kawoshi.
Abunda ake tsammani ga mutum mai hankali da nazari shine; yayin da mace ta ce tana kaunar shi, ya binciki zuciyar shi, shin dagaske ta dace da abunda ya ke so? Sai ya amsa mata ba tare da kaskanci ba, kuma yayi kokari ya nuna cewa shine ma ya ke son ta din kafin ma ta nuna tana son shi. Sannan idan ba ta dace ba, sai ya lallabata da kalamai ma su dadi ya sallame ta ba tare da ya wulakanta ta ba, ko ya tozarta ta a duniya ba.
Saboda haka; ni a gani na wannan yarinyar ba ta yi laifi ba ko kadan don ta bayyana kaunar ta ga wanda ta ke, shine ya yi kauyanci da ya kasa bi da ita ta hanyar da zai lallabata har ta hakura, har ya kai su ga irin wannan tereren a bainar jama'ah.