10/10/2025
Ƙa’idojin Ma’aikatar Hajji ta Saudiyya Kan Tanadin Masauki Da Kamfanonin Hidimta Wa Mahajjata
Daga Ibrahim Muhammad
Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta fitar da sabbin ƙa’idoji da ke tsara yadda ƙasashe za su ɗauki kamfanoni masu yi wa alhazai hidima da kuma yadda za su samar da masauki da abinci ga mahajjatansu a biranen Makkah da Madina yayin aikin Hajjin shekarar 2026.
Takardar da aka raba wa dukkan ofisoshin Hajji yayin kammala zagayen ƙarshe na jigilar alhazai a 2025, yanzu ita ce madogara wajen ɗaukar masu yi wa mahajjata hidima da kuma kula da walwalarsu a biranen Makka da Madina.
Muhimmin abin da aka fi jaddadawa a cikin wannan sabuwar doka shi ne taƙaita yawan kamfanonin da kowace ƙasa za ta iya ɗauka. Kamar yadda shafi na 2, sashi na 5 na ƙa’idar ya nuna: “Ofishin Hajji na ƙasa yana da ikon ƙulla yarjejeniya da kamfanoni biyu kacal; ba a yarda a wuce wannan adadi ba.”
Wannan umarni yana nufin kowace ƙasa za ta iya ɗaukar kamfanoni biyu ne kawai, ɗaya don hidima a Masha’ir da Makkah, ɗaya kuma don shirye-shiryen ƙarin hidima don tabbatar da daidaito da tsari mai inganci wajen kula da mahajjata.
Har ila yau, shafi na 2, sashi na 7 ya bayyana cewa: “Kamfanin da aka ɗauka don yi wa mahajjata hidima shi kaɗai ne ke da izinin ƙulla dukkan yarjejeniyoyi da s**a shafi masauki da abinci ga mahajjata a Makkah da Madina ta hanyar amfani dandalin Nusuk.”
A aikace, wannan yana nufin Najeriya za ta iya ɗaukar kamfanoni biyu ne kawai don aikin Hajjin 2026, ɗaya don mahajjatan jihohi, gudan kuma domin kamfanoni masu zaman kansu - duk za su gudanar da shirye-shiryen masauki da abinci ta yin amfanin manhajar Nusuk.
Masu lura da al’amura na ganin wannan sabon tsari yana nuna yadda Ma’aikatar ke ƙoƙarin haɗa dukkan ayyukan Hajji a cikin Saudiyya. Wannan tsari ya riga ya rage ayyukan wasu hukumomin Hajji na ƙasa, kamar Hukumar Hajji da Umrah ta Afirka ta Kudu (SAHUC), zuwa matsayin masu sa ido kawai yayin Hajjin 2026.
Wata majiya daga Ma’aikatar ta bayyana cewa, wannan shawara ta biyo bayan matsalolin da aka fuskanta a lokacin Hajjin 2025, inda ta buga misali da Indonesia wadda ta ɗauki kamfanoni fiye da 11 a Hajjin bara.
“Bisa wannan dalilin ne Ma’aikatar ta rage yawan kamfanonin yawon buɗe ido masu zaman kansu da ake ɗauka daga kowace ƙasa. Misali, Pakistan tana da kamfanoni kusan 965, yayin da Bangladesh ke da kusan 658. Mu’amala da irin wannan yawan kamfanoni na haifar da ƙalubale mai sosai ga Ma’aikatar,” in ji majiyar.
A cewar Ma’aikatar, sabuwar dokar na da manufar sauƙaƙa lura da aikin Hajji, inganta sa ido kan kula da alhazai da kuma hana watsewar mahajjata daga ƙasa ɗaya a wurare daban-daban a Makkah.