02/06/2020
ZANGA ZANGA NA CI GABA DA YA MUTSA AMURIKA
Zanga-zangar tarzoma ta ɓarke cikin wasu birane a faɗin Amurka, kan kisan da 'yan sanda s**a yi wa wani Ba'amurke ɗan asalin Afrika da ba ya ɗauke da makami #
Gwamnan jihar Minnesota ya ce tashin hankalin mutuwar George Floyd a hannun 'yan sanda ta rikiɗe zuwa "wani abu daban da ya fi k**a da ɓarnata dukiya da gangan".
Yamutsi ya karaɗe gomman birane ciki har da New York da Los Angeles da kuma Washington, inda aka rufe fadar White House na wani ɗan lokaci.
An garƙame fadar shugaban ƙasar na wani ɗan lokaci yayin da zanga-zanga kan mutuwar Goerge Floyd ta fantsama har gidan gwamnatin Amurka.
Wasu masu zanga-zanga sun yi ƙoƙarin tsallaka katanga, yayin da wasu ke ƙona tutocin Amurka," in ji ta.
An tuhumi wani tsohon ɗan sandan Minneapolis da kashe George Floyd, sai dai masu zanga-zanga na son ƙarin jami'an da ake zargi da hannu su ma, su fuskanci shari'ah.
An ga Derek Chauvin, wanda farar fata ne, a hoton bidiyo ya danne wuyan George Floyd ɗan shekara 46 da gwiwarsa ranar Litinin.
Tuni dai aka kore shi daga aiki shi da sauran abokan aikinsa uku.
A Minneapolis inda aka kashe George Floyd, masu zanga-zanga sun bijire wa dokar hana fitar dare kuma ƙoƙarin 'yan sanda na tabbatar da aiki da ita kaɗan ne.
Matakin na zuwa ne bayan ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Georgia sak**akon wani maryace mai cike da tarzoma da ƙone-ƙone a birnin Atlanta.
A birnin Dallas, an riƙa jifan jami'an tsaro da duwatsu, su kuma sun mai da martani da hayaƙi mai sa hawaye.
Rahoton News24