24/03/2025
SHIRIN SABUWAR JIHAR JIGAWA (Kashi na 1)
Shirin namu na yau, zai yi duba ne a kan yadda gwnanatin jihar Jigawa ta ɗauki ɗamara kan farfaɗo da ilimin fasaha, ƙirƙire-ƙirƙire da dogaro da kai (TVET).
Shirin ya mayar da hankali ne kan yadda gwnanatin jihar Jigawa, s ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamnan jihar Jigawa Malam Umar A. Namadi FCA ya mayar da makarantar SANTAMI da ke Garki, zuwa makarantar koyar da sana'o'i da ƙirkire ta musamman (Center of Excellence for Vocational and Technical Education) wadda duk faɗin ƙasar nan babu irinta. Makarantar za ta dinga horas da ɗalibai tare da yaye su a fannin sana'o'in iri-iri domin dogaro da kawunansu.