29/07/2026
Kanada Ta Tabbatar Najeriya A Matsayin Muhimmin Abokiyar Hulɗa A Nahiyar Afirka – Bagudu Ya Ce Zuba Jari Ya Fi Tallafi Amfani
Jakadan riƙo na Babban Ofishin Jakadancin Kanada a Najeriya, Dr. David Sproule, ya bayyana cewa Najeriya na daga cikin manyan ƙasashen da Kanada ke bai wa muhimmanci a Afirka. Ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da haɗin gwiwa da Najeriya domin bunƙasa tattalin arziki, samar wa matasa aikin yi, ƙarfafa kamfanoni masu zaman kansu, yaƙi da sauyin yanayi, da kuma inganta hukumomin gwamnati.
Dr. Sproule ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja.
Ya ce Kanada ta ware sama da dala miliyan 127 domin tallafawa Najeriya a shekarar 2024 zuwa 2025, ta hanyar shirye-shirye daban-daban da s**a haɗa da bunƙasa tattalin arziki, daidaiton jinsi, kiwon lafiya, yaƙi da sauyin yanayi, da ƙarfafa cibiyoyin gwamnati.
A cewarsa, sabuwar manufar Kanada game da Afirka ba ta taƙaita ga bayar da tallafi kawai ba, tana kuma ƙarfafa zuba jari, samar da ƙwarewa ga matasa, da bunƙasa harkokin kasuwanci.
Da yake mayar da martani, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yabawa Kanada bisa ci gaba da haɗin gwiwa da Najeriya, yana mai cewa dangantakar ƙasashen biyu ta ginu ne kan mutunta juna da kuma burin ci gaba.
Bagudu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki domin jawo masu zuba jari, ƙara damar kasuwanci, da rage talauci.
Ya jaddada cewa zuba jari ya fi amfani ga Najeriya fiye da karɓar tallafi, domin hakan yana samar da ci gaba mai ɗorewa da kuma ƙarin ayyukan yi ga al'umma.
Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da Shirin Ci gaban Ward na Renewed Hope, wanda zai tsara bukatun ci gaba a dukkan ƙananan yankuna 8,809 na Najeriya, domin gwamnati da abokan hulɗa su san inda ake buƙatar ayyukan ci gaba, su guji maimaita aiki, kuma su tabbatar da cewa ci gaba ya kai ga al'umma.
Bagudu ya gayyaci Kanada da kamfanoninta masu zaman kansu su zo su zuba jari a Najeriya, yana mai cewa ci gaban ƙasa ba zai samu ba sai da haɗin kan gwamnati, masu zuba jari, da abokan hulɗar ƙasa da ƙasa.
Ya ƙara da cewa gyare-gyaren da gwamnati ke yi sun fara jawo hankalin masu zuba jari, tare da ƙara inganta yanayin kasuwanci da tattalin arziki.
Haka kuma ya ce Najeriya na ci gaba da samun manyan jarin gine-gine da sauran ayyukan raya ƙasa, kuma tana ƙoƙarin zama ƙasa mai jan hankalin masu zuba jari daga sassa daban-daban na duniya.
Bagudu ya ce yana da muhimmanci a riƙa bayyana nasarorin Najeriya ga duniya, domin dimokuraɗiyyar ƙasar da sauye-sauyen tattalin arzikinta na zama abin koyi ga sauran ƙasashe.
A ƙarshe, bangarorin biyu sun tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da haɗin gwiwa wajen bunƙasa tattalin arziki, samar wa matasa damar aiki, da ƙarfafa dangantakar Najeriya da Kanada.
Ciroman Koko Media Team
29/07/2026