06/11/2025
MATSAYI DA DARAJA WANDA KE CIKIN GIDAN (SAYYEEDA-ZAHRA) ALAIHASSALAM.
ACIKIN AL-QUR'ANI. DA KUMA HADISAN ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU-ALAIHI WA'ALIHI WASSALLAM.
فِي بُيُوتٍ أَذِنَ اللَّهُ أَن تُرْفَعَ وَيُذْكَرَ فِيهَا اسْمُهُ يُسَبِّحُ لَهُ فِيهَا بِالْغُدُوِّ وَالْآصَالِ
Gidan da hatta ( Manzon ) Allah baya shiga sabili da matsayin gidan sai ya naimi izini a gurin masu gidan wato ( Sayyeeda-Zahra ) da ( Imam Aliyu ) gidan da ba'a shiga sai an kira sunan Allah da naiman iz'nin masu gidan sabili da darajan su.
Wannan aya da mukawo a sama tana magana ne akan daraja da matsayi na gidan Annabawan Allah Subhanahu-Wata'ala.
Daga ciki kuwa harda gidan ( Sayyeeda-Zahra ) salamullahi alaiha.
Sabili da akawi hadisi da yake nuni akan cewa akaw gidan (Sayyeed Zahra ) Acikin hadisin kuma daga (Manzon) Rahma ne kai tsaye.
Watarana a massallaci wani mutum ya mike a masallaci ya tambayi (Manzon - Rahama) cewa ayannan da ta sauka wato.
( Fhi-Bhuyutin----zuwa karken ayan)
Yake tambayan (Manzon) rahama ana magana akan wani gidane ?
Sai (Manzon) rahama yace dashi gidan Annabawa ake nufi.
Sai shi kuma ( Abubakar ) ya miqe ya tambaya? cewa ya ( Rasulullah ) daga cikin gidajen da ayan nan taka sauka akwai wancan gidan sai yayi nuni da gidan da Imam ( Aliyu Da Sayyeeda ) suke zaune.
Sai Manzon Allah ya amsama (Abubakar) da cewa yana cikin mafi girman gidan da ayan ta sauka akansu.
Amma duk da matsayi da daraja na wannan gidan wanda ba'a shiga sai ankira sunan Allah da ( Manzon ) Allah a ciki.
Shine gidan da hatta (manzon) Allah baya shiga kai tsaye sai ya kira sunan Allah da masu gidan.
Amma ahaka a samu (Abubakar) bayan kwacen Khalifan cin Manzon Allah da ayi a basa ahaka bai bariba saida ya tura ( Umar Ɗan Khaɗɗab ) gidan ƴar ( Manzon Allah ) dashi da rundunan sa domin suje su ɗaƙƙo Imam ( Aliyu Da Sayyeeda Zahra ) akan wai sai sunyi bai'a ya zuwa khalifancin da aka bama ( Abubakar )
A lokacin da ( Ummar ) ya isa gidan(Sayyeeda Zahra) yana zuwa ya k**a kira da ƙarfi cewa yake ƴar gidan ( Manzon - Allah) Imma kizo dake da mijinki kumiƙa wuya da shugabancin khalifa ( Abubakar ) Ko kuma wallahi sai mun ƙona wannan gidan naki
Wani acikin rundunar ( Ummar ) yaji maganan tayi girma sosai yace ya kai ( Umar ) gidannan da kake cewa ko sufito sumiƙa wuya ko muƙonashi akwai fa ƴar'( Manzon) Allah a gidan fa yace eh, yasani koda itan sai me....
Wa'iya zubillah kaduba girman wannan maganan fa
Daganan sai ( Sayyeeda-Zahra ) ta taso domin ta buɗe ƙofan da taji buga ƙofan yayi yawa.
Tana zuwa bakin ƙofan sai wani ya buga ƙofan da ƙarfi harta bugi ƙirjin ta sannan ta faɗo mata akan awazunta ya 😭😭😭😭 ( Sayyeeda-Zahra )
Daganan ta faɗi daman akwai cikin ɗanta wanda za'ahaifa wanda aka saka masa suna ( MUHSIN ) wah'musibatah, ya ( Zahra )😭😭😭😭
Daganan basubarta haka ba akwai wani la'anan nen Allah wanda ake kiransa da ( Ƙumfuz ) wanda yayita dukanta a ƙirji har'sai da tayi shahada.😭😭😭😭
Wannan hadisi ya zone a littafi wanda ake kira daga ( Ibn - Ƙhutaiba ) ( Al-Imamah-Wassiyasah )
Allah Subhanahu-Wata'ala Ya Tabbatar Damu A Cikin Masu Wulaya Da Manzon Allah Da Iyalangidansa.
Daga : Khalid Ahmad Kudan Turiyya