Littafin yaki by ibrahim bebeji

Littafin yaki by ibrahim bebeji Littafin yaki,soyayya,ban dariya etc

Alhamdulillah! Today marks another year of my life, and I am deeply grateful to Allah for His endless mercy, protection,...
22/06/2026

Alhamdulillah! Today marks another year of my life, and I am deeply grateful to Allah for His endless mercy, protection, and countless blessings. Ya Allah, thank You for giving me life, health, guidance, and opportunities beyond what I deserve.

As I celebrate my birthday, I reflect on Your goodness and faithfulness throughout my journey. Every achievement, every lesson, every moment of joy is a gift from You. Alhamdulillah for the blessings I can see and the ones I cannot.

I pray that Allah forgives my shortcomings, increases me in wisdom, faith, good health, happiness, and barakah. May He guide my steps, strengthen my Iman, grant me success in this world and the Hereafter, and make me among His righteous servants.

Happy Birthday to me! Alhamdulillah for another beautiful year of life. May the years ahead be filled with Allah's mercy, blessings, and endless opportunities to do good. Ameen.

19/06/2026

Alhamdulillah am back fully active

01/04/2026

I just wanna make someone's daughter happy one day😘💜

24/02/2026

Watch, follow, and discover more trending content.

22/02/2026

RAMADAN KAREEM

15/02/2026

Innalillahi 😭 na tura masa Kuɗi 160k ya Saya min kaya Yayi blocking Ɗina 🥺😭 ga profil ɗinsa 👇
com/profile.php

07/02/2026

Mutum Da Aljan
Littafi Na Takwas (8)
Part D.
Marubucin littafin Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing by Ibrahim Alhassan bebeji

Labari ya Isowa ibson cewa..
NAN TAKE AKA FARA BUDE BARI GUDA NA KOFAR BIRNIN
KAICO AIKI SAI MAI SHI
kafin a gama bude wannan katuwar kofa sai da su sarki Alkasim s**a gaji
s**a kosa domin sai da aka kusan shafe rabin sa'a
kafin kofar ta wangame gaba daya ne s**a hango
dakarun dake budeta ashe adadinsu yakai ninkin dakarun dake kofar birnin
Ba komai ne ya haddasa hakan ba face tsananin girman kofar
da kuma mugun Nauyinta
kofar na gama budewa sai miliyoyin dakaru s**a k**a haki tamkar ransu zai fita saboda tsananin gajiyar aikin
da s**ayi
mamakine ya sake turnuke su sarki Alkasim tare dani
kaina Guyson Nan take aka yi musu inkiyar su shiga
cikin garin Sarki Alkasim ne ya fara wucewa gaba sannan
yarima kamsus na biye dashi saikuma ragowar tawagar
Da isowarsa daf da kofar sai s**a ga wani irin ruwa ya feshesu daga sama har kasansu ruwan ya
wanke dukkanin kurar dake jikinsu da kuma dukkan dattin dake kasan
kofaton ababan hawansu
kafin kiftawar ido wata irin iska mai dan dumi ta
bugesu nan take danshin jikinsu ya bushe gaba daya tamkar
digon ruwa bai taba su ba gaba dayan
jikinsu ya dume da kamshin turare irin kamshin da basu
taba ji ba mai saisaita kwakwalwa, duk an yi
haka ne domin kada su shiga cikin birnin Dilhar da kazanta
ko warin jiki
kawai sai gani s**ayi ababan hawansu na taka wani
abu k**ar gilashi a lokacin da s**a kunna kai zuwa
cikin birnin
Sai da s**a lura da kyau s**a gane cewa ashe ba gilashi
bane farin dutsen zinare ne mai haske da sheki wanda aka shimfide birnin gaba daya dashi
babu inda mutum zai sa kafarsa yaga kasa ko
kura face wannan farin dutsen zinare
fara tafiyarsu keda wuya sai ga wani bafaden sarki masaru
Anjana tare da mukarrabansa
sun nufi su sarki Alkasim
shi dai wannan bafade ya kasance kyakkyawan Aljani mai
matukar kwarjini Tamkar bil adama kuma ya caba ado irin na sarakai wanda yai matukar burge sarki Alkasim da
jama arsa
koda sarki Alkasim ya hango wannan bafade ya tunkarosu sai ya kamu da tsananin
farinciki domin a zatonsa sarki Masarul Anjana ne ya taho taryarsa
da kansa saboda haka sai sarki Alkasim yai sauri ya
tsaida dokinsa ya sauko kasa ya taryi bafaden ya mika masa hannu domin su gaisa..
Bisa mamaki sai yaga bafaden ya zube kasa a gabansa
ya kwashi gaisuwa yana mai cewa lale marhaban da sarkin
sarakunan bil adama wane ni na yi hannu dakai ina matsayin
sarkin fada kawai?
Nazo ne kawai domin nayi muku jagora zuwa masaukinku
dajin wannan batu sai nan take sarki Alkasim ya kamu
da tsananin kunya domin wannan ne karo na farko a rayuwarsa da ya risinawa
wani mahaluki daban
wanda bai kasance sarki ba k**arsa
bisa wannan dalili ne ya kasa juyasa ya hada idanu da
jama arsa domin ji yake k**ar kasa ta tsage ya shige
cikinta dan kunya, shi a ganinsa darajarsa ta fadi
kuma kimarsa ta zube a idanun jama arsa tunda gashi ya
risinawa bawan wani sarkin
nan fa takaici ya turnukeshi don haka da baya baya ya
isa inda dokinsa yake ya k**a ya hau nan dai sarkin
fada da mukarrabansa s**a yiwa su sarki Alkasim jagora
zuwa masaukinsu
kafin a isa masaukin sai da su sarki Alkasim s**a zamo cikakkun kauyawa saboda kalle kalle da waige waigen abubuwan
kawa da na al ajabi wadanda aka cika birnin dasu
Sarki Alkasim ne kawai ya dake ya sa idanunsa akan gabansa
kawai baya yarda ya kalli komai saboda izzarsa da
girman kansa
shi kuwa yarima kamsus sakin jikinsa yayi yayi ta baiwa idanunsa
abinci sai wage baki yake yana ta murmushi da dariya
tamkar gonar Auduga
Al amarin daya fusata sarki Alkasim kenan yaji k**ar ya daka masa tsawa amma sai ya basar
Aljanu maza da mata yara da manya sai kai kawo
suke a cikin birnin kowa na sha anin gabansa
babu abin da ya kara daurewa su Sarki Alkasim kai face
ganin yadda babu wanda ya kallesu bare ma a san dasu amma su kuwa dole s**a rinka
kallon jama ar garin saboda tsananin kyawunsu,
tsaftarsu da kuma iya adonsu, 'yan matan garin kuwa tamkar
sune s**ayi kansu saboda tsananin kyau kowacce budurwa sai dai kaga
hadimai suna take mata baya tamkar itace yar sarki
Masarul Anjana
Al amarin da yai matukar baiwa su yarima kamsus mamaki kenan har ya ayyana a ransa
cewa sai yayi tambaya akan hakan , Shikuwa sarki
Alkasim babu abinda yai maso ciwo face ganin yadda babu
wanda ya damu da ya ganshi a matsayinsa na sarkin
da babu k**arsa a kasashen bil adama
Tabbas ya san cewa babu inda labarinsa bai kai ba a duniya
cikin dukkan kasashen mutane da Aljanu to amma menene
dalilin da ya sa anan birnin Dilhar ba a dokin ganinsa?
Amsar da ya kasa bawa kansa kenan kuma hakan ne
ya jefa zuciyarsa cikin wasu wasi fargaba gami da
tunani
sabanin yadda aka basu masauki a birnin shugaba mandarul Aswad anan birnin
dilhar duk da tsananin yawan tawagar sarki Alkasim
sai da aka baiwa kowannan mutum katafaren gida
shi
Kadai cike da kuyangi, barori da hadimai, Guyson sunana
Al amarin da ya sa kowa ya kara firgita kenan da sha anin
Sarki masarul Anjana Lokacin da Sarki Alkasim ya shiga gidan
da aka bashi yaga cewa
wannan gida ya ninka fadarsa sau dari a girma
kawatuwa da hadimai kuma ya kasance tamkar Aljannar
Duniya domin wadansu abubuwan na jin dadin
rayuwa dake cikinsa ko a labari bai taba jin irinsa ba
kawai sai sarki Alkasim ya zauna a gefen luntsumemen gadon dake dakin barcinsa
yayi tagumi ya k**a zancen zuci inda yace da kansa ''
''
Hakika girman kai rawanin tsiya ne !!
A iya rayuwata ban taba zaton cewa akwai wani mahaluki
mai karfin mulki arziki da daukaka k**ata ba a wannan
doron kasa, amma yau gashi da idanuna naga wanda ya
yi mini fintinkau..
Tabbas wannan duniya da fadi take kuma abin cikinta da
yawa gareshi don haka ilimin duniya ba mai karewa
bane sai dai mai nemansa ya kare !!
Wata zuciyar kuwa sai tace da sarki Alkasim
'' haba yanzu kai shike nan tun yanzu ka bayar da kai
bori ya hau !
Ai idan an fika arziki da karfin mulki ba lallai bane a
fika jarumtaka tunda sai an gwada sannan akan san na kwarai !
Ka bari kayi GABA DA GABA da sarki masarul Anjana a
sannan ne zaka san matsayinka kuma ka san banbancinku''
++
Koda gama aiyana hakan sai sarki Alkasim ya bushe da dariyar
farinciki ya baje akan luntsumemen gadon yana ta kyakyata dariya tamkar
mahaukaci sabon kamu
++++++++++++++++++++++++
A bangaren yarima kamsus kuwa lokacin da shima ya
tsinci kansa a cikin nasa kawataccen gida sai ya kasa zama ko tsayuwa saboda
mamaki da al ajabin abubuwan da idanunsa ke gani
don haka bai ma bukaci ya shiga dakin barci ya kwantaba
domin ya huce gajiyar dake jikinsa kawai sai ya k**a
yawo a cikin katon gidan yana kalle kalle su kuwa hadiman gidan sai s**a rinka
yi masa dariya domin kallon dan kauye suke masa
Lokacin da ya isa inda wadansu kuyangi kimanin
su ashirin ke zaune suna baiwa furanni ruwa a cikin
lambu sai ya yafito daya daga cikinsu wata budurwa ma abociya kyawu fiye da sauran
cikin hanzari ta baro
yan uwanta ta zo gareshi ta zube kasa bisa guiwoyinta
a gabansa ta kwashi gaisuwa tana mai amsa kira
yarima kamsus ya k**a kafadunta ya tasheta tsaye yace yake wannan kuyanga bani
labari yaya k**annin gimbiya zulfulaifa yake
kuma menene dalilin da yasa naga gaba dayan
matan garin nan kyawawa ne k**ar su s**ayi kansu sai dai
wata tafi wata?
Lokacin da kuyangar taji wannan tambaya sai tayi murmushi
sannan tace yakai wannan dan sarki mai daraja ka yi sani
cewa hasken gimbiyata yafi duk wani haske wanda
idanunka ya taba gani tsagwaron laushin fatar jikinta kuwa
yafi na jaririn da aka haifa yanzu yanzu take yawan gashin kanta gami da kyalkyalinsa
tamkar an zuba narkakken ruwan lu'u lu'u ne a cikin kogi
dara daran idanuwanta dogon siririn hancinta gami da
dan karamin bakinta tamkar zanen Alkalami na sarkin
masu rubutu na duniya
Babu wani lafazi ko wani harshe da zai iya siffanta
iyakar siffofinta da kyawunta face abinda idanu s**a iya gani kawai
sannan tambayarka ta gaba
amsarta shine
! Ba komai ne yasa gaba dayan matan garin nan s**a
kasance kyawawa bakuma komai na garin nan ya zamo
mai kyau ba face GIMBIYA ZULFULAIFA ta tsani duk wani
mummunan abu ko yaya yake
Duk wani abu da take hulda dashi ko take gani sai ya
kasance kyakkyawa
ya kai wannan dan sarki mai daraja na sani cewa yanzu
dakaji labarin gimbiyata ka kagu da son ganinta?
Sai dai kash ! Burinka ba zai cika a yanzu ba !! Amma kayi
hakuri ba zaka ganta ba sai nan da cikar kwanaki
bakwai ranar da za a kaiku fadar sarkina sarkin duniya
mahaifin Gimbia zulfulaifa
maigirma sarki masarul Anjana a sannan ne za a fara
gabatar da wannan gasa ta duniya domin sanya
gimbiya zulfulaifa yin dariya
Hm wannan zance haka yake Nima Al amin ibson na
shirya tsaf domin halartar wannan fada ta mai girma sarki
masarul Anjana
domin yin gasar saka gimbia zulfulaifa dariya ehem ko zan dace na Samu Auranta ehem
ME ZAI FARU IDAN YARIMA KAMSUS YAYI ARBA DA GIMBIA ZULFULAIFA?,
ME ZAI FARU IDAN SARKI MASARUL ANJANA DA SARKI ALKASIM SUKAYI GABA DA GABA?
WAYE ZAI IYA SA GIMBIA ZULFULAIFA TAYI DARIYA?
YAUSHE NE JARUMI ZAIHAS DA JARUMA NAMRITA ZASU SAKE KAIWA SARKI ALKASIM HARI?
Marubucin Littafin yace Mu hadu alittafi Na Gaba domin
jin cigaban wannan kasaitaccen labari,,,,
wanda ni Ibrahim bebeji
nake jagorantar rubuto
mukushi
,
kuma a nan nake cewa Sai mun hadu a Littafi na gaba wanda yanzu haka babushi A hannuna
Amma da zarar na siyo Zakujini da shi Insha Allah.
Nidinne dai
Ibrahim Alhassan bebeji
Kuma Admin
A zauran labarai
sannan mai son ganin farin cikinku a koda yaushe
nake cewa mu hade a wani sabon littafin kafin na samo cigaban
wannan wanda muka karanta yanzu.
amma kafin nan zanso naji ta bakin kowa
daga cikinku shin me kake hange a tattare da haduwar SARKI ALKASIM DA SARKI MASARUL ANJANA
sannan ya zai kasance a lokacin da s**ayi Arba da juna hm
wannan Amsar zaiyi wuya a wajanku amma dai ina jiran hasashenku
Abokai da Qawaye..
Na barku lafiya

30/01/2026

Mutum Da Aljan
Littafi Na Takwas (8)
Part C.
Littafin Abdul aziz Sani M/Gini
Typing by Ibrahim Alhassan Abubakar bebeji

Labari ya isowa ibson301 Cewa..
A LOKACIN DA HAKORANSA GUDA BIYU SUKAYI FITAR BURGU
GAMI DA FURZAR DA NI , kafin kiftawar ido dakarun Aljanu
sama da dubu Arba'in sun bayyana a cikin dakin sun yiwa sarki Alkasim da yarima
Kamsus KAWANYA kuma sun zare mak**ansu zasu afka
musu sai shugaba damzurul Aswad ya daka musu tsawa s**a ja da baya
shugaba damzurul aswad ya mike tsaye yana mai kurawa
sarki Alkasim idanu cikin tsananin fishi a lokacin da ya
goge jinin dake kan lebensa har fuskarsa na yin gatsine
saboda bacin rai
Kwatsam ba zato ba tsammani kuma sai damzurul Aswad ya takarkare ya bushe da
wata mahaukaciyar dariya yana mai nuna sarki Alkasim
da dan yatsansa guda sannan yace tabbas ka cika sarki
guda daya na Bil'adama abin kwatance, Hakika ka cika MAI IZZA DA GIRMAN KAI gami da yarda da kai To amma
Ka sani cewa ' GABA DA GABANTA saika isa birnin sarkina
sannan zaka raina kanka kuma zaka gane cewa kai ba
kowa bane a Mulki, Daukaka da Isa.
Lallai saikayi nadamar wannan cin mutunci da kayi mini
domin zaka gane cewa wulakanta shugaba da kaskantar
dashi ba karamin kuskure bane Koda gama fadin hakan sai
Damzurul Aswad ya daga hannunsa guda sama
take dukkanin dakarun da s**a bayyana s**a bace bat ! Kawai
sai Damzurul Aswad ya fice daga cikin dakin
koda ganin hakan sai yarima kamsus yai sauri ya tattaro
kayansu s**a fito daga cikin gidan Ai kuwa suna fitowa waje
s**a iske gaba dayan jama'ar tawagarsu a tsaitsaye
bisa ababan hawansu
ba tare da bata wani lokaci ba sai sarki Alkasim da yarima kamsus
s**a yiwa tawagar tasu jagora s**a fice daga cikin kauyen
Lausus s**a durfafi Babban Birnin Dilhar Inda sarki Masarul
Anjana yAke.
Sai da aka shafe kwanaki uku cur Ana tafiya ba tare da an sake
riskar wani gari ba ko kauye kawai cikin muggan dazuzzuka ake ratsawa masu dauke
da muggan dabbobin daji da mugayen bakaken Aljanu
amma babu abinda ya sami kowa
A ranar kwana na uku ne da farkon dare sarki Alkasim
ya bayar da izinin a tsaya a yada zango ayi hutu na yan sa'o'i kadan Nan take kuwa aka bi
umarnin kowa ya tsaya aka kafa tantuna Bayan an gama
kafa sansanin sarki Alkasim tare da yarima kamsus na
zaune a cikin tanti suna shan shayi sai hira ta karke a tsakaninsu
Inda yarima kamsus ya dubeshi yace yakai abbana kayi
sani cewa lokacin da naji labarin da ka bani Akan yadda
ka hadu da mahaifiyata da irin gwagwarmayar da
kasha a gasar da kuka yi da kuma tsagwaron jarumtakar
daka nuna har ka sami nasarar kashe muguwar dabba razima sai naji guiwata tayi sanyi domin na tabbatar da cewa
ba zan iya yin irin wannan jarumtakar da kayi ba
Ta yaya sunana zai daukaka k**ar yadda naka ya daukaka??
Ta yaya zan iya cika babban burina na yin
gagarumin Abin Al ajabin da baza a taba mancewa dashi ba
a cikin wannan duniya k**ar yadda ka bar tarihin jarumtakar ka a kasar su mahaifiyata luslaiya
har duniya ta nade za a rinka tunaka a cikin tarihi
a matsayin jarumin da ya kashe dabbar da ta addabi
mutannen kasa guda tsawon shekaru sittiin da bakwai
lokacin da yarima kamsus yazo nan a zancensa sai
Sarki Alkasim ya bushe da dariya Al amarin da yayi matukar
baiwa yarima kamsus mamaki da tsoro kenan daga can
sai sarki Alkasim ya hade fuskarsa kuma ya dafa kafadar
kamsus yace kai yaro mai rai baya fidda tsammanin sa a da rabo
kada ka manta cewa sa a , rabo a cikin jinin gidanmu
yake don haka in dai zuciyarka bata mutu ba zaka iya
cika burinka' Ibrahim Alhassan Abubakar bebeji
Ibson sunana kenan daga
Littafin yaki by Ibrahim bebeji' babu abin da yake datse zuciya da burinta face mutuwa
wannan dalili ne yasa har yanzu jarumi ZAIHAS da yar uwarsa suke sa ran cewa
zasu iya daukar fansa a kaina su kasheni
a yanzu haka suna tare damu a cikin wannan sansani Na san
inda suke kuma nasan a irin siffar da suke
kawai na kyalesu ne domin naga iyakar gudun ruwansu
darajarka suke ci naki hallakasu saboda na fuskanci cewa
soyayya mai karfi ta kullu a tsakaninka da yar uwar zaihas
koda sarki Alkasim yazo nan a zancensa sai yarima
kamsus ya kamu da tsananin mamaki ya dubeshi yace
yakai Abbana ina fatan dai koda sun kawo maka hari a yanzu
ba zaka kashe su ba?
Dajin haka sai sarki Alkasim ya hade fuska yace aini bana
yin magana biyu tuntuni na gaya maka cewa kayi musu
gargadin kada su kuskura su sake kawo mini hari kuma
na san ka gaya musu
Idan ban manta ba suma sunce ba zasu sake kawo min hari ba
har mu isa birnin Dilhar, to ka gaya musu cewa ina nan ina jiransu idan mun isa can din
ai mai rabon shan duka sai yashashi, mazaka tashi ka tafi izuwa tantinka kayi
shiri domin saura dakiku kadan mu cigaba da tafiyarmu
saboda irin son mu isa birnin dilhar kafin cikar kwanaki goma sha ukun da shugaba Aswad ya fada
koda jin wannan batu sai na mike da sauri na nufi hanyar
fita daga cikin tantin amma saina waigo na dubi Sarki
cikin murmushi nace
''
Ina jinjina ga mahaifina jarumin da
yake dakawa Aljanu Gumba a tafin hannunsu !!
'' Kaine mai takalmin karfe mai take MUTUM DA ALJAN kuma kaine gaba da gabanta Aljani
ya taka wuta !!! ''
koda jin wannan kirari sai sarki yayi murmushi nan da nan yarima kamsus yaje ya yi
shiru ba tare da bata wani lokaci ba aka sake dunguma
aka ci gaba da tafiya ba sassauci....
++
Manyan birane uku su Sarki Alkasim s**a gani kafin su isa birnin Dilhar kuma
kowanne birni yafi dukkan biranen duniya wadanda s**a isa misali Girma
kawatuwa da karfin Arziki sau goma
A kwana na tara ne da yammaci sakaliya su sarki Alkasim
s**a iso kofar birnin Dilhar
Wohoho ! Hakika wanda duk baiyi yawo ba a cikin wannan
duniya to bai morewa idanunsa kallo ba kuma tabbas tafiya mabudin ilimi ce
tun daga nesa kafin su sarki Alkasim su iso kofar
birnin Dilhar gaba dayansu s**a dimauce wasunsu basu san
sa adda s**a wangame baki ba yawu na dalala saboda tsananin mamaki
wasu kuwa ba su san sa adda s**a k**a sambatu ba
tamkar sun sami tabin Hankali ba komai ne ya janyo hakan
ba face hango Girman Birnin da kawatuwarsa
iya hangen mutum bai isa ya hango karshen tsawo da fadin garin ba
kuma a cike yake da gidaje masu benaye hawa hawa babu gidan dake kasa da hawa dari
Kuma dukkanin gidajen birnin an ginasu ne da zallan
tubalin lu'u lu'u sai dai kowacce unguwa launin
gidajenta kala daban ne wasu koraye, jajaye, shudaye, ruwan dorawa da dai
sauransu
ko ina a cikin garin a haskake yake da wani irin haske na
musamman yadda ko allurace ta fadi sai mutum ya ganta
iskar dake kadawa gaba dayan harabar birnin kuwa itama ta
musamman ce wacce
bata da karfi bata da sanyi mai damu sai wani irin yanayi
mai dadin gaske har wani irin kamshine mai saita kwakwalwa a cikinta..
Lokacin da su sarki Alkasim s**a isa bakin kofar birnin
Dilhar kuwa sai s**a sake dimaucewa fiye da ko yaushe saboda ita kanta
kofar garin ta isa abin kallo domin idan mutum ya mallaketa
zai iya shiga gasar ATTAJIRAN DUNIYA
girman kofar a tsawo da fadi ya kai kamu dubu kuma
bari biyu ce Anyita da zallan duwatsu guda arba in wadanda s**a hada da
yakutu zinare jauhar lu u lu u zubar daji murjani da sauransu
nau'o'in duwatsu
wadanda mutane basu san da wanzuwarsu ba a doron
kasa
dakarun dake tsai tsaye a bakin wannan kofa suna gadinta
sun kai su miliyan dubu uku a cikin gagarumar shigar yaki
Duk iya yawon sarki Alkasim da bincikensa a HALLARAR TSAFI
bai taba ganin dakarun Aljanu masu girma da kwarjini k**arsu ba kuma sun
kasance tamkar tagwaye komai na jikinsu iri daya ne
hm marubucin littafin yace ' mai karatu misali ko bayani ko
kwatance ba zai iya bayyana iyakar siffar wadannan dakarun yaki ba
Al amin Ahmed Misau
Guyson sunana kenan nake magana, duk da tsananin jarumtaka gami da dakewar zuciya irin ta sarki Alkasim sai da yaji tsoro ya darsu a cikin zuciyarsa a lokacin da yayi arba da wadannan miliyoyin
dakaru
sauran jama arsa kuwa har da yarima kamsus
komawa s**ayi bayansa suna nokewa k**ar ace kyat su
barke da gudu saboda razana
tazarar dake tsakanin wadannan dakarun yaki dasu
sarki Alkasim takai taku Arba in amma sai da aka shafe kusan
dakika dari da sittin ana kallon kallo
Shi kansa sarki Alkasim ya kasa takawa ya karasa gaban
dakarun yayi magana daga can sai yayi kundun bala ya sakarwa dokinsa linzami ya
nufi bakin kofar
kawai sai aka hango wani abu a can sama ya taho cikin azababben gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya ya nufo kan sarki Alkasim
kafin sarki Alkasim yayi wani yunkuri tuni
Abin ya duro a kasa a gaban dokinsa ya cake a cikin kasa
fadin abin sai da ya rufe sarki Alkasim da dokinsa
Ashe ba komai bane wannan abu face mashin Shugaban wadancan dakarun yaki
masu gadin birnin Dilhar
tsulum saiga shugaban Dakarun ya bayyana a gaban sarki
Alkasim taamkar gIwa ta tsaya a gaban akuya
kawai sai yasa hannu daya ya zare mashin nasa ya azashi
bisa kafadarsa nauyin wannan mashi da girmansa yafi karfin bil adama dari uku su
rabashi da kasa
shugaban dakarun ya dubi sarki Alkasim cikin wata irin
kakkausar murya mai tsananin kara da firgitarwa yana mai daka masa tsawa yace
wanene kai har da zaka tunkaro kofar wannan gari mai albarka
ba tare da izininmu ba?
Koda jin wannan tambaya sai sarki Alkasim ya fusata ainun a lokacin da yaji dukkan tsoro ya kau daga cikin zuciyarsa kawai sai shima ya dakawa shugaban dakarun tsawa yace
NINE SARKI ALKASIM MAI BIRNIN MISRA.
Don me zaka bukaci sanin komu suwaye alhalin ku ne kuka
gayyacemu izuwa birnin naku?
Idan ba zaku bude mana kofa ba mu shiga ai saimu koma da baya izuwa tamu
kasar inda muke da cikakke iko
koda jin wannan batu sai shugaban dakarun yayi
dan guntun murmushi mai k**a da bacin ran dodo
sannan yace '' Marhaban da sarki Alkasim ka gafarceni
Ya shugabana wannan tsarin aikina ne na tuhumi duk mahalukin da ya zo
yana gama fadin hakan sai ya daga hannunsa na hagu sama
nan take aka fara bude bari guda na kofar birnin...
Kaico aiki sai maishi..
Ganin yadda ake bude kofar yasa na tsaya a nan
Nidinne dai
Ibrahim Alhassan Abubakar bebeji

Address

Ep 17 Lafiya Road Kinkinau Kaduna
Kurmin Mashi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Littafin yaki by ibrahim bebeji posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Littafin yaki by ibrahim bebeji:

Shortcuts

Share