29/09/2026
LARABA, 30 GA SATUMBA
NASSI: YUNUSA 2:1-10
KAN MAGANA: ALLAH YANA AMSA ADDU’A
YUNUSA 2:1-10
1: Sai Yunusa ya yi addu'a ga Ubangiji Allah a cikin cikin kifin,
2: ya ce, “A cikin wahalata na yi kira gare ka, ya Ubangiji, Ka a kuwa amsa mini. Daga can cikin lahira na yi kira, Ka kuwa ji muryata.
3: Ka jefa ni cikin zurfi, Can cikin tsakiyar teku, Inda igiyoyin ruwa s**a kewaye ni, Kumfa da raƙuman ruwanka s**a bi ta kaina.
4: Na ce, an kore ni daga wurinka, Duk da haka zan sāke ganin Haikalinka mai tsarki.
5: Ruwa ya sha kaina, Tekun ta rufe ni ɗungum. Tsire-tsiren teku s**a naɗe kaina.
6: Na tafi can ƙasa ƙarƙashin tussan duwatsu. Ƙasar da ƙofarta take rufe har abada, Amma ka fitar da ni daga cikin ramin, ya Ubangiji Allahna.
7: Sa'ad da na ji raina yana rabuwa da ni, Sai na tuna da kai, ya Ubangiji. Addu'ata kuwa ta kai gare ka a Haikalinka tsattsarka.
8: Su waɗanda suke yin sujada ga gumaka marasa amfani Sun daina yi maka biyayya.
9: Amma ni zan raira yabbai gare ka, Zan miƙa maka sadaka, Zan cika wa'adin da na yi. Ceto daga wurin Ubangiji yake.”
10: Ubangiji kuwa ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunusa a gaɓar teku.
ALLAH YANA AMSA ADDU’A
Wace hanya ce mafi kyau don kammala jerin ayyukan bautar Allah a watan Satumba fiye da ta hanyar addu’a!
Daga mai da hankali ga al’amura na karshe a Wahyayin Yahaya, mun haura zuwa al’amura na siyasa ta duniya a Esta, kuma mun kare da batutuwan manufа a Yunusa. Muna da su duka a wuri daya ne.
Mun kammala da Yunusa yana addu’a a wani wuri da ba a saba gani ba: cikin cikin kifi! Wannan shine wuri na karshe da za ka bada shawarar gudanar da taron addu’ar ka! Amma kuma, Mulkin Allah yana fuskantarmu. Yana yin abubuwan al’ajabi a wuraren da ba a zata ba.
Addu’ar Annabi ita ce ta yabo, da sujada, da godiya ga Allah; i, har da Allahn da ya yi kokarin ya gujewa! A cikin wannan duka, Allah ya yi nasara!
Hakika ciyawa ta kan bushe, furanni kuma su yi yaushi, amma maganar Allah ba za ta taba faduwa ba (Ishaya 40:8). Muna tare da mai Zabura: Daga gabas zuwa yamma, a yabi sunan Ubangiji! Ubangiji yake mulkin dukan sauran al’ummai, daukakarsa tana bisa kan sammai, ba wani kamar Ubangiji Allahnmu. Yana zaune a can kwankolin Sama. (Zabura 113: 3-5).
Kamar yadda Ubangiji ya amsa addu’ar Yunusa daga cikin cikin kifin kuma ya sa ya amayar da shi a bakin teku, zai amsa addu’arka a yau. Amma ka tuna cewa kana da aikin da za ka yi masa. Ka shirya?
TAMBAYA:
Shin ka sami dalilin yin addu’a a wurare da yanayi da ba a saba gani ba?
ADDU’A:
Gare ka kai kadai dukan daukaka, da iko, da mulki sun tabbata har abada abadin. Amin.
Abincin Yini - 2026