26/08/2026
LABARI CIKIN HOTUNA 25/08/2026
Assalamu Alaikum,
Majalisar Sarakunan Arewan Agege, a karkashin jagorancin mai Martaba Sarkin Hausawan Agege kuma NATIONAL LEADER na ITTLAN Alh Musa Muhammad Dogon Kadai, a wajan taron kaddamar da zagayan Maulidin bana (1448) a Garin Agege.
Mai Martaba ya yi kira da muyi koyi da dabi’un Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, mu kuma yiwa kasar mu Nijeriya da karamar hukumar mu ta Agege adduar zaman lafiya da kuma bunkasar tattalin arziki.