09/05/2025
"Yaki da ake tsakanin jiragen yaki na Pakistan da aka yi a China, da jiragen Rafale na Indiya da aka yi a Faransa, sojoji za su sa ido sosai a kai, domin neman bayanai da za su iya basu galaba a rikice-rikicen nan gaba."
"A ranar Laraba, jirgin yaki na Pakistan da aka yi a China ya harbo aƙalla jiragen sojin Indiya biyu, kamar yadda wasu jami'an Amurka biyu s**a shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters. Wannan na nuna muhimmin ci gaba ga jirgin na Beijing."
"Pakistan ta yi ikirarin cewa ta kakkabo aƙalla jiragen Indiya biyar, ciki har da Rafale guda uku, a wani fada da ake zargin ya shafi jiragen yaki 30 na Pakistan da 70 na Indiya."
"Sashen BBC Verify ya ce ya tabbatar da sahihancin wasu bidiyo da suke nuna goyon baya ga ikirarin Pakistan."
"Wannan faɗan sama dama ce mai wuya ga sojoji su yi nazarin aikin matukan jirgi, jiragen yaki, da makamai masu linzami da ake amfani da su a yaƙi, su yi amfani da wannan ilimin don shirya rundunar sojin samansu don yaƙi."
Muhammed Arabi'u Zango TV #