01/09/2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin sama wa ƙwararrun ’yan Nijeriya aiki a ƙasashen waje
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani shiri mai suna “Hire from Nigeria” (wato 'A ɗauki ma'aikata daga Nijeriya') domin bai wa ’yan ƙasar nan damar yi wa kamfanoni da masu ɗaukar ma’aikata na ƙasashen waje aiki.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a wani taron manema labarai da aka yi a ofishin sa a Abuja.
Ya ce: “Ƙaddamar da wannan shiri wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarin da Nijeriya take yi na sanya ɗaya daga cikin manyan kadarorin ƙasar mu, wato mutanen mu, a sahun gaba wajen hulɗar tattalin arzikin mu da duniya.”
Ya ce yawan matasan Nijeriya, da ɗimbin ƙwararrun ma’aikatan ta da kuma bunƙasar fasahar zamani sun ba ƙasar damar yin gogayya da sauran ƙasashe a fagen tattalin arzikin duniya.
Idris ya ce: “Makomar tattalin arzikin Nijeriya za ta ƙara dogara ne kan ƙwarewa, ƙirƙire-ƙirƙire, fasaha da kuma ƙwazon jama’ar mu. A shirye Nijeriya take ta yi gogayya a fagen duniya. A shirye ƙwararrun ’yan Nijeriya suke su yi aiki, kuma ya k**ata duniya ta mayar da hankali kan Nijeriya."
Ya ƙara da cewa gangamin ya haɗa ma’aikatun tarayya na Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari da na Ilimi, NATEP, iDICE da kamfanoni masu zaman kan su domin haɗa ƙwararrun ’yan Nijeriya da masu neman ƙwararrun ma’aikata a duniya.
Ya ce shirin ya yi daidai da Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma burin Gwamnatin Tarayya na samar da guraben aiki miliyan ɗaya ta hanyar fitar da ayyuka zuwa ƙasashen waje.
“Ba sai matashi ɗan Nijeriya ya bar ƙasar ba kafin ya samu damar shiga harkokin tattalin arzikin duniya. Idan aka ba shi ƙwarewar da ta dace, ababen more rayuwa, ƙa’idojin sana’a da damar shiga kasuwanni, ’yan Nijeriya za su iya rayuwa, su yi aiki kuma su samu kuɗi a nan gida, yayin da suke samar da ayyuka ga abokan ciniki da masu ɗaukar ma’aikata a faɗin duniya,” inji shi.
Shi kuma Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ya ce ma’aikatar sa tana inganta ƙwarewar ’yan Nijeriya ta hanyar inganta tsarin koyarwa, koyar da sana’o’i da dabarun fasahar zamani, da kuma horar da su bisa buƙatun masana’antu.
“Manufar Ma’aikatar Ilimi ita ce, a duk inda ake neman ma’aikata a duniya, muna son ’yan Nijeriya su samu horo, su samu takardar shaidar ƙwarewa kuma su kasance a shirye don a ɗauke su aiki,” inji shi.
A nata ɓangaren, Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, ta ce gangamin zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasan Nijeriya, da ƙara fitar da ayyuka zuwa ƙasashen waje da jawo zuba jari.
“Shirin ‘Hire from Nigeria’ ya wuce kamfen na wayar da kai kawai; shiri ne na ƙasa da aka tsara domin bunƙasa tattalin arziki,” inji Oduwole.
Ta ce za a gabatar da kamfen ɗin a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, inda Nijeriya za ta bayyana fa’idar ɗaukar ’yan Nijeriya aiki ga masu ɗaukar ma’aikata na duniya.
Tun da farko, Babbar Mataimakiya ta Musamman kan Sadarwa ta Dabaru da NATEP, Misis Olajumoke Dan-Okayi, ta ce shirin zai magance matsalolin da ke hana ƙwararrun ’yan Nijeriya samun damar aiki a duniya.
Ta ce: “Ba ƙwarewa ce matsalar ba, kuma ba buri ba ne. Matsalar ita ce yadda za a gano ƙwararrun ’yan Nijeriya, amincewa da su da kuma samun damar shiga kasuwannin duniya. Don haka, shirin ‘Hire from Nigeria’ yana da ayyuka uku masu sauƙi: ya sauƙaƙa wa duniya gano Nijeriya, ya sauƙaƙa amincewa da ƙwararrun ’yan Nijeriya, sannan ya sauƙaƙa ɗaukar ’yan Nijeriya aiki.”
Ana sa ran kamfen ɗin zai haɗa ƙwararrun ’yan Nijeriya da masu ɗaukar ma’aikata, kamfanoni masu neman ma’aikata, masu zuba jari da kasuwannin ƙasashen waje.