20/11/2025
: ππππ RUΔANI ππππ
NA
FATIMA ΔAHIRU FUNTUWA BINTA
Page 58
09042512952
Ya ce "Allah dai ya kiyaye, Aiku matanne da anyi maku zancen kishiya shikenan yanzun mutum ya' bata shirin shi."
Ta ce "A'a ka daina yin jam'i, ni ka ta'ba ganin na yi?"
Ya ce "To na ta'ba zo maki da zancen kishiyar ne?"
Ta ce "Haba ai kasan ni ba abinda zai faru."
Ya ce a'a ai ba'a san maci tuwo ba sai miya ta 'kare. "
Tayi dariya tare da fad'in "Ai dai ya k**ata ka shaide ni."
Ya ce "Taya za'ayi in shaide ki? Tunda ban ta'ba zo maki da zancen 'kara auren ba, amma ba komai, wata rana koda wasa ne zan tone ki da zancen kishiya, inga yadda zakiyi."
Ta ce "To ai ka riga kace tono na zakayi, kaga daka fad'a dama na sani, don haka ya za'ayi in tada hankali na, tunda na san wasa kake."
Sukasa dariya baki d'ayan su.
πππππKATSINA TA DIKKO 'DAKIN KARA πππππ
Ko da ta je wurin su H-Amina sai da hankalin ta yayi mummunan tashi, saboda ta same su a wani Irin yanayi, sunyi ramar da basu ta'ba yin Irin ta ba, ga bugu, duk an farfasa masu jiki, fuskar su duk ta kumbura, sunyi wani zuru-zuru, duk wanda ya gansu dole ya tausaya masu, bata san lokacin da hawaye s**a zubo mata ba, sai da ta dake sannan ta ce
"H-Amina me yasa kika kashe kishiyar ki?"
H-Amina ta d'ago da idanun ta, wad'anda har sun 'kan'kance saboda azabar kuka.
Ta ce "Bani na kashe ta ba."
Barrister Haseenat ta ce "To yaya akayi?"
Ta ce "Zargi ne kawai akeyi, Al-halin ni da naje gidan ma ko ganin ta banyi ba, kuma lokacin da aka kashe ta ni na riga na kai kano, ban san yadda akayi ba."
Barrister Haseenat ta ce "Kin tabbatar ba ke kika kashe taba?"
"Bani na kashe ta ba, kuma ban san wanda ya kashe ta ba, tunda ni bamma ta'ba zuwa garin ba sai wannan ranar, ballan tana in san ala'kar ta da mutane."
Barrister Haseenat ta ce "Da kika shiga gidan me yasa baki ganta ba?"
"Sabo da mujin ta ya rufe 'kofar, ko falon ma bai bari na shiga ba, har nabar gidan, kuma bayan na tafi shima ya biyo ni a baya, ni lokacin na isa kano, shi kuma ya kusa kaiwa, aka kira shi a waya aka sanar da shi cewa yaje an tarar da gawar matar shi a cikin d'akin ta, daga haka ni bansan komai ba. "
Barrister Haseenat ta ce "Kin tabbatar abinda kika fad'a min gaskiya ne?"
H-Amina ta ce "Iya kar gaskiya ta na fad'a maki."
Barrister Haseenat ta ce "Idan har aka samu akasin haka, to ni babu yadda za'ayi in iya fitar dake, ma'ana in dai ke kika kashe ta, to dole gaskiya zatayi halin ta."
H-Amina ta ce "Wallahi ba ni na kashe ta baπππ."
Dai-dai nan kuka ya kwace mata.
Barrister Haseenat tayi waje, don bazata iya ci gaba da ganin yanayin da Amina take ciki ba.
COURT
Ranar litinin biyu ga watan February aka fara shari'ar H-Amina Mansur.
Kamar yadda aka saba, ko wace ranar Monday courtu tana cika ma'kil da jama'a.
Haka aka fito dasu duk sun fita k**annin su.
Bayan an natsu, maga takardar kotun ya kira sunan shari'ar da z'a fara yi a yanzun, sannan lauyoyi s**a gabatar da kansu k**ar haka.
"Sunana Barrister Abubakar Ibrahim, ni lawyer ne daga hukumar kare ha'k'kin d'an Adam, na tsaya ne a wurin nan domin kwato ma iyalan marigayiya ha'k'kin su na kisan 'yar su da akayi."
Daga d'aya ' bangaren kuma ta ce
"Sunana Barrister Haseenat, ni lawyer ce wadda nake kare wadda ake zargi da kisan marigayiya Mariya."
Sannan gaba d'ayan su s**a zauna.
Al-'kali ya ce "Daga ' bangaren kare ha'k'kin 'Dan Adam, ko zaka sanar damu dalilin da yasa kuke zargin H-Amina da cewa ita ta kashe kishiyar ta?"
Barrister Abubakar ya sake mi'kewa tsaye, sannan yayi godiya ga Al-'kali ya ci gaba da cewa
"Ranar Ashirin da uku ga watan January, H-Amina da 'kawar ta sun shiga gidan marigayiyar da tashin hankali mai tsanani, wanda daga 'karshe har ita H-Aminar tayi ikirarin cewa :Lallai bata fita gidan sai taga gawar ta, kuma hakan ta fad'e shine a bainar jama'a, bayan kuma ta bar gidan da wasu awanni, sai aka tarar da gawar mamaciyar a d'akin ta, inda aka kashe ta da wu'ka, ta hanyar caka mata ita a 'kafon zuciya, don haka muke neman wannan kotu mai adalci da ta d'auki matakin daya dace akan wannan mata, na gode. "
Zuwa can sai Al-'kali ya ce "Ko Lawyer wadda ake zargi tana da abin cewa?"
Sai ita ma ta mi'ke bayan Barrister Abubakar ya zauna.
"Kwarai kuwa ya mai shari' a, Maganar cewa H-Amina ta ambaci zata kashe Mariya, wannan ba abin mamaki bane, domin kuwa kowa yasan zafin kishi ga d'iya mace, a yayin da Irin abinda ya faru ga H-Amina ya faru gare ta, zata iya fad'in ko wace Irin kalma ce a yayin da take cikin 'bacin rai, harma abinda ba zaka iya aikatawa ba.
Ta fad'i kalmar kisa ne badon zata iya aikatawa ba, sai don zafin kishin da take ciki a wannan lokacin, sai kuma