08/09/2026
Gwamnatin Katsina Ta Kai Samame Wajen Siyar Da Sinadarin Kwamuso
Gwamnatin Jihar Katsina ta fara kai samame wuraren da ake zargin ana safarar da siyar da sinadarin Kwamuso, wanda ake amfani da shi wajen kula da yara marasa lafiya a jihar.
Samamen, wanda Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Katsina ta gudanar tare da haɗin gwiwar hukumomin lafiya na matakin farko da jami’an tsaro, ya gudana ranar Litinin, 7 ga Satumba 2026.
A yayin samamen, jami’an sun k**a mutane shida a wani asibitin Baƙin da ke Ƙaramar Hukumar Mashi, yayin da aka k**a wasu mutane biyu a cikin garin Katsina, bisa zargin hannu wajen safarar da siyar da sinadarin.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan kammala samamen, shugaban kwamitin da Kwamishinan Lafiya na jihar ya kafa, Hon. Musa Adamu Funtua, ya ce safarar sinadarin Kwamuso babban laifi ne da ke jefa rayuwar yara marasa lafiya cikin haɗari.
“Wannan abu ba kishin ƙasa ba ne, ba tausayi ba ne, kuma ba tsoron Allah ba ne. Ana ba da Kwamuso ne domin yara marasa lafiya, don haka duk wanda ke yin wannan ta’asa yana cutar da al’umma,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na kashe makudan kuɗaɗe wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya, musamman kula da yara, don haka ba za ta bari wasu mutane su yi amfani da kayan aikin lafiya domin cin moriyar kansu ba.
“Duk wanda ke da hannu cikin irin waɗannan laifuka, idan ya shiga hannu, zai fuskanci hukuncin hukuma,” in ji shi.
Shi ma Sakataren kwamitin binciken, Dr. Umar Bello Bindawa, ya bayyana cewa samamen na daga cikin matakan farko da kwamitin zai ɗauka domin gano dillalan da ke safarar sinadarin zuwa wuraren da ake siyar da shi ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ce mutanen da aka k**a za a miƙa su ga hukumomin da s**a dace domin gudanar da bincike da ɗaukar matakin da ya dace.
Dr. Bindawa ya yi kira ga masu safarar Kwamuso da su dakatar da harkar kafin su faɗa hannun jami’an tsaro, yana mai cewa duk wanda aka k**a zai fuskanci hukuma.
Samamen ya samu halartar ƙungiyoyi da hukumomin da ke da ruwa da tsaki a harkar lafiya, ciki har da masu kula da harkar abinci mai gina jiki (Nutrition) da sauran masu ruwa da tsaki.