29/05/2026
GAYYATA!
GAYYATA!!
GAYYATA!!!
Kungiyar Majma’u Ahbab Sheikh Ibrahim Inyass Association of Nigeria, reshen Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna, karkashin jagorancin Sheikh Alhaji Mustapha Bashir Maidiwani Saminaka, na farin cikin sanar da daukacin al’umma, musamman ‘yan uwa Musulmi, abokai da masu fatan alheri, cewa za ta gudanar da babban taron kaddamar da fara neman tallafin jama’a domin gina makarantar sakandare da cibiyar koyon sana’o’i a Karamar Hukumar Lere.
An shirya wannan taro ne domin fara gangamin tara tallafi ga wannan babban aiki da kungiyar ke da niyyar aiwatarwa, wanda ke da manufar bunkasa ilimi da koyar da sana’o’i ga matasa domin cigaban al’umma da kasa baki daya.
Za a gudanar da taron kamar haka:
Rana: Lahadi, 31 ga watan Mayu, 2026
Lokaci: Karfe 9:00 na safe zuwa 2:00 na rana
Wuri: Salama Event Center, Hayin Gada, Saminaka
Kungiyar na kira ga daukacin jama’a, masu hannu da shuni, ‘yan kasuwa, masu ruwa da tsaki, abokai da masu fatan alheri da su halarta tare da bayar da gudunmawa domin ganin an cimma wannan kyakkyawan buri na bunkasa ilimi da koyon sana’o’i ga matasa.
Domin karin bayani ko tuntuba, ana iya kira ta wadannan lambobi: 07037710983,08088692463, 08039452387.
Allah Ya ba mu ikon halarta tare da tallafawa wannan aiki na alheri. Ameen.
KHM TV HAUSA