Labaran Hausa NG

Labaran Hausa NG Yada labarai cikin harshen Hausa, turanci da kuma labaran abubuwa dake faruwa a Najeriya.

Babban layin lantarkin Najeriya ya sake samun matsalaCikin wata sanarwa da kamfanin rarraba wutar lantarki na birnin Abu...
12/02/2025

Babban layin lantarkin Najeriya ya sake samun matsala

Cikin wata sanarwa da kamfanin rarraba wutar lantarki na birnin Abuja ya fitar a shafinsa na X, ya ce matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safe.

Wakilin kasar Sin ya bukaci Carloha ya fadada kasancewar Chery a Najeriya. Wata alama ta zurfafa dangantakar tattalin ar...
04/02/2025

Wakilin kasar Sin ya bukaci Carloha ya fadada kasancewar Chery a Najeriya. Wata alama ta zurfafa dangantakar tattalin arziki a ƙarƙashin Ƙaddamarwar Belt da Road!

An harbe mutumin da ya kona Al-Qur'ani a SwedenAn ruwaito kashe Salwan Momika mai shekara 38 ne a yammacin ranar Laraba ...
31/01/2025

An harbe mutumin da ya kona Al-Qur'ani a Sweden

An ruwaito kashe Salwan Momika mai shekara 38 ne a yammacin ranar Laraba a wani gida a birnin Stockholm.

Farashin Kayan masarufi Abinci a Kasuwar Giwa, Kaduna State, a ranar Alhamis, January 23, 2025:Maize: ₦51,000–₦53,000Sor...
24/01/2025

Farashin Kayan masarufi Abinci a Kasuwar Giwa, Kaduna State, a ranar Alhamis, January 23, 2025:

Maize: ₦51,000–₦53,000

Sorghum: ₦50,000–₦51,000

Soybeans: ₦82000–₦83,000

White Beans (Zapa): ₦93,000–₦92,000

White Beans (Misra): ₦90,000–₦91,000

Small White Beans: ₦113000–₦114000

Rice: ₦55,000–₦57000

Millet: ₦67,000–₦67,000

Ƙasashen Sahel uku da s**a haɗa da Mali da Burkina Faso da Nijar sun sanar da cewa za su ƙaddamar da sabon fasfonsu a ma...
24/01/2025

Ƙasashen Sahel uku da s**a haɗa da Mali da Burkina Faso da Nijar sun sanar da cewa za su ƙaddamar da sabon fasfonsu a mako mai zuwa, ranar da wa’adin fitarsu daga ƙungiyar ECOWAS ke cika.

SERAP ta bukaci Trump ya kwato tare da mayar da kadarorin Najeriya da aka sace, inda ta yi kira da a dauki matakin kula ...
23/01/2025

SERAP ta bukaci Trump ya kwato tare da mayar da kadarorin Najeriya da aka sace, inda ta yi kira da a dauki matakin kula da kudaden cin hanci da rashawa da ke da alaka da jami’an kasar.

SERAP ta caccaki Amurka kan sama da fadin kadari da darajarsu ta iai dala biliyan 500 na dukiyar Najeriya da aka sace, tana mai kira ga Trump da ya dauki matakin yaki da wannan rashin adalci a duniya.

Kasancewar Najeriya a matsayin abokiyar kawancen BRICS wani babban ci gaba ne ga alakar ta da manyan kasashen duniya kam...
23/01/2025

Kasancewar Najeriya a matsayin abokiyar kawancen BRICS wani babban ci gaba ne ga alakar ta da manyan kasashen duniya kamar China, Rasha, da Brazil.

A  , ministan harkokin wajen kasar Sin Wang ya sanar da shirin bayar da tallafin soji na yuan biliyan 1 kwatankwacin dal...
20/01/2025

A , ministan harkokin wajen kasar Sin Wang ya sanar da shirin bayar da tallafin soji na yuan biliyan 1 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 136 da kuma zuba hannun jarin ayyukan layin dogo a wani bangare na shirin Belt and Road Initiative..

Najeriya na shirin yin amfani da dala miliyan 52.88 da ta kwato domin ayyukan samar da makamashi, wanda hakan ya fallasa...
18/01/2025

Najeriya na shirin yin amfani da dala miliyan 52.88 da ta kwato domin ayyukan samar da makamashi, wanda hakan ya fallasa dogon tarihin da ta yi na wawushe kayayyakin ƙasashen .

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce Afrika na da dukkanin abinda ake buƙata domin samar da ci gaban yankin a ƙashin kant...
15/01/2025

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce Afrika na da dukkanin abinda ake buƙata domin samar da ci gaban yankin a ƙashin kanta, kuma lokaci ya yi da za a fara ganin hakan a aikace, sabanin dogara da wasu ƙasashen ƙetare.

Chadi ta sanar da daƙile wani hari da ta ce mayaƙa ɗauke da muggan makamai sun kai fadar shugaban ƙasar da ke birnin N’D...
09/01/2025

Chadi ta sanar da daƙile wani hari da ta ce mayaƙa ɗauke da muggan makamai sun kai fadar shugaban ƙasar da ke birnin N’Djamena a yammacin jiya Laraba inda mutane 19 s**a mutu.

Kakakin gwamnatin Chadi Abderaman Koulamallah ya ce maharan 24 ne s**a farwa fadar kuma dakarun Sojin ƙasar sun hallaka 18 daga cikinsu, ko da ya ke suma sun kashe jami’i guda.

Wasu mayaƙa da ke da alaƙa da kungiyar ta’addanci ta IS sun kashe sojojin Najeriya 6 bayan wani artabu da s**a yi a sans...
07/01/2025

Wasu mayaƙa da ke da alaƙa da kungiyar ta’addanci ta IS sun kashe sojojin Najeriya 6 bayan wani artabu da s**a yi a sansanin sojin da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Address

No 4 Alh Sabitu Mai Omo Street
Lere
811104

Telephone

+2347000046414

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Labaran Hausa NG posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share