
26/06/2025
2027: Idan Tinubu ya bani takarar mataimakin shugaban ƙasa da gudu zan karɓa - Barau Jibrin
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana cewa ko da yake ba ya son ya shiga cikin muhawarar wanda zai iya zama abokin takarar Shugaba Bola Tinubu a 2027, zai karɓi kowane nau’in aiki da Shugaban ƙasa zai danka masa cikin farin ciki da biyayya.
Yayin wani taron manema labarai da aka shirya dangane da shirin jin ra’ayoyin jama’a a shiyyoyi daban-daban da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sauya Kundin Tsarin Mulki , Barau ya ce: “Duk abin da Shugaba ya bukace ni da in yi, zan yi shi dari bisa dari ”
Wannan bayani na zuwa ne bayan wata magana da ya yi a ranar Talata, inda ya shawarci wata ƙungiya da ke goyon bayan kudurin sa ya zama mataimakin shugaban kasa a 2027 da su maida hankali wajen goyon bayan shirye-shiryen gwamnati maimakon batun siyasa.
“Lokacin siyasa zai zo, amma yanzu lokacin shugabanci ne.”
Barau ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin uban gidansa na siyasa wanda yake da cikakkiyar biyayya a gare shi.