05/07/2025
Sheikh Abubakar Elmiskin ya na magana a badadin dukkan shehina Darikar Tijjaniyya na jahar Borno bisa kubutan su daga dukka muridai da su ke sabawa umurni Allah da Manzon Allah SAW.
Sheikh Abubakar Elmiskeen ya ce:=
بأننا جميعا بريئون من كل متخلق بأخلاق الفاسقين والمنافقين ولوانتسبوا إلى الشيخ، إذ انتسابهم الى الشيخ على هذا الحال باطل، ونحن بريئون أيضا من كل مرتكب المعاصي أو يرتكب بحضرته وهو ساكت،وإذ سكوته من ذلك رضى، ونحن بريئون منهم الف يراءة كما تبرأ الشيخ في بعض رسائله
Fassara:=
Sheikh Abubakar Elmiskeen ya ce"-" Dukkan mu munkubuta da da dukkan mai hali irin na halayen fasiqai da munafakai
(wanda su ke cewa halal da haram duk dayane) ko da da kuwa sun nasabtu
i zuwa shehu Tijjani ko shehu Ibrahim Inyass a bisa wannan bacaccen halin.( na kin yin sallah, a zumi, cin haram da alaqa da mata wanda ba muharraman su ba).
Sheikh Abubakar Elmiskeen ya ci gaba da cewa 'kuma mu shehunan Jahar Borno ( Sheikh Ahmad Abulfathi, Sheikh Abubakar Elmiskeen, Sheikh shariff Ibrahim Saleh, sheikh shariff Tijjani, Sheikh Idris khadi, sheikh Abagoni, sheikh Adam Dankellori, Sheikh Muhammad maidala,ilu, sheikh Goni modu Goni kolo, Sheikh Abubakar Gonimi, Sheikh Abdussalam, sheikh Modibbo Gidado,) munkubuta daga dukkan wani shehi, muqaddami ko muridi da ya ke aikata sabo ko ake aikatawa a halaran shi ya yi shuru bai hana ba, domin shuru alamane ca ta yarda.
Sheikh Abubakar Elmiskeen ya cigaba da cewa 'mun kubuta daga su kubuta sau dubu, kamar yadda shehu Ibrahim Inyass ya kubuta da su a ciki wa su da ga cikin wasikun shi,
Mu na kira ga masu da da,awa ta karya, ta jahilci, da neman abun duniya, da tara mabiya su ji tsoron Allah sudai na anfani da sunan manyan shehina i da su ka koma ga Allah da wanda su ke raye, su rika aika a bun da babu shi, a cikin Darikar Tijjaniyya da faidar shehu Ibrahim Inyass.
Duk wanda ku gani ko ku kaji ya nasabta kan shi ga shunan Jahar Borno da kuma ya ke aika a bun da bai dace ba to wallahi bai rayu da su ba, kuma shi ba almajirin su bane kar ku yarda da shi makaryaci ne.
Allah ka kiyaye imanin mu.
Mansur Usman Mani
5/7/2025.