20/08/2024
♦️AL'AJABI ♦️
(DAGANI BABU TAMBAYA)
BY
HAJARA YUSUF
(Real Hajara Yusuf)
Episode 15
Bayan jamaa sun taru ana jimamin me yasa jamaar cikin adaidaita sahun s**a ruga aguje s**a fita, acikin jamaar kuwa harda abban fati.
Bayan kowa ya leka cikin napep din kuma ba wanda yaga wani abun tsoro, abban fatine yaje gaban kaka yace haba inna babu wani abun tsoro acikin adaidaita sahun amma duk kunbi kun daga hankalinku, kaka tace Ayuba lafiyan idonka lau kuwa? Abban Fati yace Wallahi inna bakomai sai Akuya da agwagwa. Kaka ta tashi aguje taruga cikin gida tana ihu Salati, yayinda itama zee tayi hanyar gidansu da gudu, shi kuma Hamisu yana gefe jikinsa yana rawa yanata maimaita inda Rabbana no Wahala, yayinda shi Ya'u ya samu waje ya zauna ya rattaba tagumi.
Abun dai yabawa kowa mamaki, abban fati yaje wajen ya'u yace wai meke faruwa dakune kuyi mana bayani mana hankalin kowa ya kwanta. Ya'u yace abundai sai INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUUN, Wancan agwagwan da kuka gani ya bace mana acan unguwarmu mun nemeshi sama da kasa bamu samuba, sannan akuyar ta mutu tun acan muka dauka muka bawa matasa suje su jefar. To yanzu gasu nan acikin adaidaita bayan bamu taho dasu ba.
Abban fati yace yanzu akuyarda ta mutu itace zata dawo tashiga adaidaita? to shikenan yaro yanzu abunda zaayi shine bari aciresu daga adaidaitan saika samu kaje kahuta, Ya'u yace bafa rudu muka shiga ba, Wallahi abunda nafada gaskiya ne. Mallam Ayuba yace kaidai kasamu kaje kahuta yaudin gobe sai kadawo kafamin asalin abunda yafaru.
Yana fadin haka yabar wajen yanufi inda adaidaitan yake, yasa hannu yafito da akuyar da kuma agwagwar yayi cikin gida dasu.
GIDAN FATI
Fati da jibrin suna zaune a parlour duk sunyi shuru k**ar kurame, fatice tayi gyaran murya sannan tace. Da karfe nawa zamu tafine naga har yanzu kaki ka motsa. Jibrin yace bazamu jeba su zasu zo, fati tace amma dadai munje din inyaso wani lokacin sai suzo. Jabir yace nidai nagama magana. Fati tace to shikenan amma ai daka fadamin nayi musu girki kafin su iso, amma dukda haka bai baci ba, bari nadafa musu koda taliya, daga haka tashiga kitchen tayi jajjagen kayan miyanta ta soya tazuba ruwa tafito tasameshi a inda tabarshi, tana zama tace su nawane zasu zo? yace su shida, fati tace to fadamin sunayensu sai yace akwai Mama sai wacce take biye mini Hasiya, sai sautanda sai musa sai yan biyunmu kuma yan auta Hassan da Hussaini. Fati tace amma kana ganin karfe nawa zasu iya isowa, jibrin yace karfe 2:00pm daidai.
Bayan fati tagama dafa abunda zata dafa tasa a warmer ta jera komai a dining table. Karfe daya da rabi nayi Sai taje tayi wanka ta dauro Alwala tazo tafara sallah, tana sallamewa kawai sai taji guguwa yana tashi, iska tako ina k**ar zai dauke gidan nasu, ga kuwwa da kururuwa da s**a mamaye ko ina. Fati ta tashi kenan zataje falo tayiwa jibrin magana kawai sai taji guguwa ya dauketa yayi sama da ita bata ankare ba taganta awani gagarumin jeji wanda baida gabas bare yamma, ga wasu mutane masu jajayen hakora masu k**a da ifiritai sun zagayeta, sannan dukkaninsu akwai kaho a kawunansu.
Fati tayi ihu ta tashi zata gudu daya daga cikinsu ya daka mata tsawa yayinda bakinsa yake amayarda wuta. Nan take fati tafadi kasa sumammiya.