Mai Labari TV

Mai Labari TV Ku bibiyemu domin kawo muku labaran cikin gida da na ketare, da tallata hajarku da sauransu. like and share

Mai Labari TV :Rayuwarmu a hannun Allah yake, ba a hannun shugaban kasar Nigeria ba. Mu yawaita tuba, mu tausayawa junan...
02/03/2023

Mai Labari TV :
Rayuwarmu a hannun Allah yake, ba a hannun shugaban kasar Nigeria ba. Mu yawaita tuba, mu tausayawa junan mu. Tabbas! Allah masani ne kuma mai hikima ne.

26/02/2023

Maiduguri: Yan kwana-kwana (fire service ) suna iya bakin kokarinsu wajen kashe gobarar.
"Muna buqatar addu'o'inku", acewar yan kasuwan da s**a jarabtu da gobarar.

Abdullahi Mohammed Ibrahim Maiduguri Monday market.

Kubiyomu domin sabonta muku labarai da dumi-duminsu. Min gode!!!
https://www.facebook.com/profile.php?id=100083520335970&mibextid=ZbWKwL

25/02/2023

Mai Labari TV: Barka da war haka, da fatan an gama za6e lafiya? Wannan shafi na Mai Labari Hausa T√ tana muku addu'a, Allah Yaza6a mana shugaba mafi alkhairi
Na gode!

Abdullahi

Ku bibiyemu domin kawo muku labaran cikin gida da na ketare, da tallata hajarku da sauransu.

SIYASA BA GABA BANEMai Labari TV Kuri'arku kimarku...1. Karku siyar....2. Karku jafar....3. Karku gaji da jiran layi.......
23/02/2023

SIYASA BA GABA BANE

Mai Labari TV

Kuri'arku kimarku...
1. Karku siyar....
2. Karku jafar....
3. Karku gaji da jiran layi....
4. Kur kuzo kada kuri'a da lalle ko kunshi ahannu....
5. Kar ku manta da yiwa kasarmu Addu'a....
6. Kar Ku manta da bibiyan wannan shafin....

*Kuyi mana , &

 ....Duk da cewa yan Nigeria sun maida hankulansu gaba daya akan wadannan mutanen domin samun saukin rayuwa ko kuma ciga...
23/02/2023

....
Duk da cewa yan Nigeria sun maida hankulansu gaba daya akan wadannan mutanen domin samun saukin rayuwa ko kuma cigaban kasa. Amma azahiri, mu muka jefa kan mu cikin matsalolin da Muke ciki ayau. Don haka, "shawara yaragewa mai shigan rijiya".
Kuma waiwaye adontafiya ne.
Mai Labari TV

KO KUN SAN CEWA GISHIRI NA DA MUTUKAR ANFANI GA LAFIYARMU?Ayau zamu duba amfanin Gishiri guda 10 da ya k**ata kowa ya sa...
23/02/2023

KO KUN SAN CEWA GISHIRI NA DA MUTUKAR ANFANI GA LAFIYARMU?

Ayau zamu duba amfanin Gishiri guda 10 da ya k**ata kowa ya sani:

Gishiri yana da amfani da yawa bayan zubawa a cikin abinci, mutane da yawa sun zata amfanin gishiri shi ne kawai a zuba a cikin miya, amma ina, amfaninsa ya fi ga haka.

Amfanin Gishiri kwararru a fannin kiwon lafiya sun tabbatar cewa baicin abin da muka sani na al’ada, wato amfanin Gishiri cikin miya, hakikatan sun tabbatar cewa Gishiri dai yana da dimbin sirruka da amfani ga dan adam.


1. Na farko, kowa ya san cewa idan Kyandir ya diga a waje, tilas zai manne da wajen, har sai an kankare shi da karfin tuwo, amma muddin ki ka jika Kyandir din ki na tsawon awa biyu ko uku, to da zaran kin kunna shi, yana ci, ko da zai diga a waje, ba zai k**a ba. Za ki sha mamaki, domin da kin dan murje shi, zai fita, tamkar Kyandir bai taba diga wajen ba.

2. Ina mata masu amfani da risho ko abin gashi irin na lantarki ko wanda ake amfani da Gas?

Mafi yawan lokaci idan kina girki za ki ga ruwan girkin ko man gyada da ki ka yi suya da shi, ko dai wani abu da ki ka dafa a kan risho ya bata shi sosai, kafin kuma ki gama girkin ya bushe, don haka da rishonki ya fara baci sai ki barbada gishiri a wajen, da kin gama girki idan ya huce kina saka soso za ki ga ya fita.

Haka ma za ki yi wa dukkanin ababen girkin ki.

3. Idan kina tantaman kwai ko ya lalace ko yana da kyau, sai ki zuba gishiri karamin cokali biyu a cikin ruwa, ki kada, ki zuba kwan a ciki, idan yana da kyau za ki ga kwan ya yiwo sama yana yawo, idan kuma ya lalace ne kuma za ki ga ya yi kasa, sabanin abin da aka saba gani.

4. Sosan wanke-wanke idan ba a tsaftace, shi sai ya zama waje ne da kwayoyin cuta suke dabdalarsu a ciki, don haka duk lokacin da ki ka gama wanke-wanke ki wanke sosan sosai, sai ki jika shi a cikin ruwan gishiri na awa daya ko biyu, kuma da zarar kin ga ya fara lalacewa ki yar da shi ki sayi wani, ba wani tsada ne da shi ba.

5. Idan kin sayi tsintsiya kuma kina so ta dade miki, idan kin sayo tsintsiya kafin ki fara amfani da ita sai ki jika ta a cikin ruwan gishiri kafin ki fara amfani da ita.


6. Idan zuma ta harbe ki, sai ki yi sauri ki zuba ruwan gishiri a wajen, yin hakan zai rage zafin harbin zumar, kuma wajen ba zai tashi ya yi ja ba.

7. Amfani da ruwan gishiri mai dumi a lokacin da mutum yake fama da ciwon hakori da kuma ciwon makogaro yana kawo sauki, sai dai da kuna, idan kika daure kunar na wani lokaci ne, amma kafin jimawa za ki ga kin sami sauki.

8. Ina masoya masu aikewa da junansu fulawa ko kuma masoya fulawa?

Amma fulawar da nake nufi fulawar roba, na san ba kowa ne zai zauna ya goge fulawar ba idan ta yi datti ko kura, domin lungu da sakon da take da shi.

Ki tsoma fulawar a cikin ruwan gishiri na ‘yan mintuna ki girgiza, dukkan dattin da ya ke jiki zai fita.

9. Idan kina da madarar ruwa kuma tana saurin lalacewa, sai ki zuba gishiri dan kadan a ciki ki jijjiga ki rufe.

10. Idan jini ya bata miki kaya, sai ki jika su a cikin ruwan gishiri ki wanke, sannan ki saka su a cikin ruwan dumi da Omo ki wanke.

Haka kuma idan gumin hammata ya bata miki kaya, sai ki zuba gishiri a cikin ruwan dumi ki wanke kayan.
Mai Labari TV

DA ƊUMI ƊUMINSA: Kotun Koli ta dage shari’ar badaƙalar canjin takardun kuɗi zuwa 3 ga Maris domin yanke hukunciMai Labar...
22/02/2023

DA ƊUMI ƊUMINSA: Kotun Koli ta dage shari’ar badaƙalar canjin takardun kuɗi zuwa 3 ga Maris domin yanke hukunci

Mai Labari TV

Kotun Koli ta saurari Lauyoyin mgwamnonin da s**a kai karar gwamnatin tarayya da babban bankin Kasa CBN, da suke kalubalantar wa’adin kashe takardun kuɗi da ka canja launin su a kasar nan.

Lauyoyi sun tattauna a zauren kotun kolin inda manyan alkalai su 7 na kotun kolin s**a saurare su.

Ba ya ga jihohi 10 da ke adawa da kuma ƙalubalantar wannan tsari na gwamnatin tarayya, akwai jihohi k**ar su Bayelsa da ke goyon bayan gwamnati da babban bankin Najeriya, CBN.

Bayan mahawarar da aka yi, babban alkali John Okoro a madadin sauran alkalan ya ce an dage zaman kotun zuwa 3 ga Maris domin yanke hukunci akan takaddamar.

Idan ba a manta ba, gwamnonin akalla 10 da s**a hada da Kaduna, Jigawa, Kano, Kogi da sauran su sun maka gwamnatin tarayya da CBN, suna kalubalantar canjin fasalin takardun naira da gwamnati ta yi

A dalilin wannan canji, an jefa ƴan kasa cikin ruɗani da halin ƙaƙanikayi a dalilin rashin kaiwa ga kuɗaɗen su.

A jihohin Ogun da Ondo, hasalallun matasa sun kona wasu manyan bankuna da lalata na’urorin ATM.

22/02/2023

Domin nishadi da tallata hajarku

YANZU-YANZU:  lauyoyin ko wani bangarorin biyu sun isa kotun koli, inda za'a sarari yadda kotu zata yanke hukunci a yau....
22/02/2023

YANZU-YANZU: lauyoyin ko wani bangarorin biyu sun isa kotun koli, inda za'a sarari yadda kotu zata yanke hukunci a yau. Akan karban tsofin takardun kudi ko dakatarwa.

Ku biyo mu domin jin yadda zata kaya a kotun
- MAI LABARI HAUSA TV

IZALA Ba Kungiyar Siyasa Ba Ce, Don Haka Ba Tada Wani Dan Takara, Kowa Yaje Ya Zabi Wanda Ya Chanchanta, Muna Fatan Alla...
22/02/2023

IZALA Ba Kungiyar Siyasa Ba Ce, Don Haka Ba Tada Wani Dan Takara, Kowa Yaje Ya Zabi Wanda Ya Chanchanta, Muna Fatan Allah Ya Zaba Mana Shugaba Mafi Alkairi A Zaben 2023 Dake Tafe, A Cewar Shugaban Kungiyar IZALA Na Kasa Sheik Abdullahi Bala Lau

Hakika irin haka muke son muji duk wani shugaban kungiyar musulunci yayi domin a irin halin da muke ciki ware wani dan siyasa a wurin malamai ba karamin zubar da mutunci bane.

Jiya Sheikh Dahiru Bauchi ma yace ba shida dan takara kowa yaje ya zabi wanda yafi chanchanta.

Fatanmu Allah ya zaba mana mafi Alkhairi a cikin su.

 Matashiyar kamfanin na   tana muku barka da wannan lokaci tare da fatan kuna lafiya. Bayan haka tana tallata muku hajar...
21/02/2023


Matashiyar kamfanin na tana muku barka da wannan lokaci tare da fatan kuna lafiya.
Bayan haka tana tallata muku hajarta ga duk mai bukatan ya siya ko ayi masa.

Ga links din mu akasa domin Karin bayani...

👇👇👇👇👇👇
Katura sakon SMS zuwa ga wannan lambar 09020602505
Ko kuma kutuntubi wannan shafin (Mai Labari Hausa TV) kai tsaye.

Mun gode!

Address

Maiduguri
1122

Telephone

+2348037872250

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mai Labari TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Mai Labari TV:

Share