02/07/2025
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
Tsohon shugaban majalisar dattawa na Najeriya, Sanata David Alechenu Bonaventure Mark, ya bayyana hukuncinsa na ficewa daga jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), wadda ya shafe fiye da shekaru 26 yana yi wa hidima.
A wata wasika da ya aikawa shugaban gundumar jam’iyyar PDP na Otukpo, karamar hukumar da ya fito a jihar Benue, David Mark ya tabbatar da barinsa jam’iyyar nan take. Wasikar mai dauke da kwanan wata 27 ga Yuni ta bayyana ne jim kadan bayan da wata kawancen jam’iyyu masu adawa s**a ayyana African Democratic Congress (ADC) a matsayin sabon dandamalin siyasar su tare da nada David Mark a matsayin shugaban kawancen.
A cikin wasikar, Sanata Mark ya jaddada cewa ya dauki lokaci mai tsawo yana marawa PDP baya, tun daga kafuwarta zuwa faduwar ta a 2015, inda ya zama daya daga cikin ‘yan jam’iyyar da s**a nace a cikinta duk da koma bayan da ta fuskanta.
“Kamar yadda kuka sani, shekaru da dama kenan ina cikin wannan jam’iyya ina kuma jajircewa wajen ganin ta ci gaba da tafiya bisa akida da nagarta,” in ji shi a cikin wasikar.
“Ko da lokacin da mafi yawan jiga-jigan jam’iyyar s**a fice bayan faduwar mu a zaben shugaban kasa na 2015, na dauki alkawari cewa zan kasance mutum na karshe da zai tsaya tsayin daka a PDP.”
Ya kara da cewa kokarinsa wajen sake gina jam’iyyar, sasanta bangarori, da kuma maido da martabarta ya taimaka kwarai wajen dawo da PDP cikin sahun manyan jam’iyyun da ke da tasiri a Najeriya.
Ficewar David Mark daga PDP dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fargabar rikice-rikice a cikin jam’iyyar, musamman duba da yadda wasu tsofaffin jiga-jiganta ke komawa wasu sabbin hadin gwiwar siyasa kafin babban zaben 2027.