25/11/2025
Shawarwari 10 ga matasa!
Duk wanda yake so ya rayu babu talauci, babu ƙasƙanci, cikin farin ciki da nitsuwa babu fushin Allah kokuma fushin iyaye to ya kula da waƴannan abubuwa guda 10
1) fara ci ko sha da Bismillah, sannan da hanun dama ba hagu ba, kuma a zaune ba'a tseye ba.
2) tsarkake zuciya akan aboki ko ɗan'uwa, ko musulmi in general, da kuma tsarkake kai (tufafi ko jiki)
3) Tseda sallah farillah, da kuma ɗaukan mataki akan yin sallah Nafila koda raka'a 2 ne kullum.
4) Yawaita tuna mutuwa tare da
yawaita ziyara ga maƙabarta.
5) Gudan zina da kwaɗayin Aure
ta hanyar halal.
6) Ciyar da iyaye mai daɗi ta hanyar
halal komi kanƙantarsa.
7) Gudan zama a majalisa don tsarkake kunne da kare baki daga batsa, idan kuma aka zauna a majalisa to a rufe zaman da fasubahanakal lahumma wabihamdika, ash-hadu Allah ilaha illah anta, Astagfiruka wa'atubu ilaihi.
8) Yawaita Addu'a da cewa Ya Ubangiji kada ka haliccemu musulmai kuma ka hanamu Rahamarka gobe ƙiyauma, ka tashemu cikin salihan bayi.
9) Ƙoƙarin sabo da sadaka wajen kyautatawa iyaye da kuma neman Addu'an su, da tawassali da faranta musu.
10) Tsayuwa akan Istigfari da salatin Annabi (SAW) akan hanya, a wajen taro, a kwance, a farkawa barci, sannan kuma a wajen aiki.
Kada ku manta kuyimin sharing saboda wasuma su amfana, kuma wallahi duk wanda ya ɗauki wannan matakin bazaiyi kuka ba duniya da lahira, Ya Ubangiji kasa mu amfanu da wannan karamin karatun a aikace.
Bilal Omar Baba Gombe ✍️