21/11/2023
Wannan ziyarar mai girma Gomna Zulum a garin Baga ba shi da wani alfanu ga talakawan da yenzu haka suke rayuwa a garin kuma cikin wahala da yunwa da fatara
Kuma abinda ya janyo wannan damuwa da wahala su ne👇
rashin samun damar yin kasuwanci da noma da kuma kamun kifi dan kowa yasan cewa su ne harkokin da duk wasu mazauna garin Baga s**a dogara da shi
daga kin gaskiya de sai bata wallahi tallahi kowa yasan cewa babu daya daga cikin wadannan harkokin da na lissafo wanda a halin yenzu mutanen Baga su ke samun damar gudanar da ita
tun a yakin neman zaben sa na biyu da yaje Baga yayiwa al'umma alkawarin zai bude kan hanyoyin kan ruwa
tun daga Baga har zuwa Kəngallam kuma zai shimfida hanyar mota wato kwalta tun daga cikin garin Baga zuwa bakin Fishdam
ya kara da alkwarin bude gidajen man fetur acikin garin sabida su dinga sayar da mai a farashin gomnati sabida masu yin noman rani su samu saukin samun mai
sannan ya sha alwashin cewa hanyar Baga zuwa Monguno da ake wahalar zuwa shima daga ranar ya roki jami'an tsaro sun basa tabbacin anan gaba ya kare
wadannan kadan daga cikin alkawura da shi mai girma Gomna Zulum yayi kenan a cikin garin Baga kuma wallahi tallahi da kunnuwana naji yayi duka wannan alkawuran
amma wallahi tun da ya fita daga garin bai sake komawa ba sai bayan watanni shida
shidin ma sai da al'ummar gari s**a shiga cikin mummunar yanayin yunwa da takaiga jama'a sun soma rokon abinda zasu ci daga yan uwa
har korafi ya kaiga dan majalisar dokokin jaha mai wakiltar karamar hukumar Kukawa
Hon. Karta Lawan ya je yayi masa korafi akan halin da ake ciki
sannan yaje ya bayar da abinci wanda shi ne na karshe da bai sake zuwa ba kusan watanni hudu sai jiya da ya tafi ya hau kan girgin ruwa yayi ta guje-gujensa ya dawo
tare da yin alkawarin bogi akan gina makarantar High Islam
a daidai lokacin da al'ummar gari ke ta watsewa sabida tsadar rayuwa
na rasa gane me yake nufi komai baya tafiya a garin kuma kungiyoyin agaji sunyi sunyi dan suje su taimakawa al'umma amma ya hana
ina kira ga dukkan manyan mu da masu wakiltar mu a majalisar jaha harda na tarayya ya kamata ku kawo dauki ga al'ummar ku
kuma sanin kowa ne cewa daukar nauyin wakilcin al'umma saida sadaukar wa ya kamata ku fito fili ku fadawa gomna gaskiya, musamman ma
Hon. Karta Maina Ma'aji Lawan ku fadawa gomna gaskiyar lamari koda zai zama sanadiyar mulkin ku sabida jama'a ne s**a zabe ku inde dan su zaku rasa mulkin ai ba damuwa bane.
✍️Ali modu Add more Baga