Northeast Online News 24

Northeast Online News 24 Your North, Your news.

"Stay informed about the latest news and developments from the Northeast region and beyond with Northeast Online News24 - your trusted source for timely and accurate news coverage."

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da kudirin karin harajin kashi 15 cikin dari kan shigo da fetur da dizalHukumar kula da har...
13/11/2025

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da kudirin karin harajin kashi 15 cikin dari kan shigo da fetur da dizal

Hukumar kula da harkokin man fetur (Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority – NMDPRA) ta bayyana cewa ba za a aiwatar da kudirin karin harajin kashi 15 cikin dari kan shigo da man fetur (PMS) da dizal ba.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, George Ene-Ita, ya fitar a shafinsu na X (da aka fi sani da Twitter) a ranar Alhamis, inda ya ce aiwatar da harajin da aka tsara baya cikin tsarin gwamnati a halin yanzu.

Hukumar ta tabbatar da cewa akwai wadataccen isasshen man fetur, dizal da iskar gas (LPG) a kasar, wanda ake samu daga masana’antun cikin gida da kuma shigo da su daga waje, domin biyan bukatar al’umma musamman a lokacin bukata ta musamman.

NMDPRA ta bukaci ‘yan kasuwa da masu motoci da su guji boye mai, saye da fargaba ko kuma kara farashi ba bisa ka’ida ba, tana mai cewa za ta ci gaba da sa ido a kasuwa tare da daukar matakan da s**a dace domin tabbatar da cewa babu tangarda wajen rabon man.

“Hukumar na godewa dukkan masu ruwa da tsaki a sashen man fetur bisa kokarinsu na tabbatar da isar mai ba tare da katsewa ba, kuma muna tabbatar da aniyar mu na kare tsaron makamashi a kasa,” in ji sanarwar.

Tinubu misali ne na juriya da jarumtakar ‘yan jaridar Nijeriya, inji Ministan Yaɗa LabaraiMinistan Yaɗa Labarai da Wayar...
13/11/2025

Tinubu misali ne na juriya da jarumtakar ‘yan jaridar Nijeriya, inji Ministan Yaɗa Labarai
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin ainihin misalin juriya, jarumta, da jajircewa waɗanda s**a bayyana tarihin kafafen yaɗa labarai na Nijeriya tun farkon tafiyar dimokiraɗiyya a ƙasar nan.

Da yake jawabi a Taron Editocin Nijeriya na 2025 (ANEC) da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, wanda ya kasance karo na farko da wani shugaban ƙasa mai ci ya halarta, Ministan ya ce halartar Shugaban Ƙasa Tinubu wata alama ce mai ƙarfi ta girmamawa da haɗin kai da 'yan jaridar Nijeriya.

A cewar sa: “Rayuwa da jagorancin Shugaban Ƙasa na ɗauke da irin ƙarfin hali da jarumtar da s**a bayyana aikin jarida a Nijeriya tun asali. Kamar dai kafafen yaɗa labarai, Shugaban Ƙasa ya kasance a kan gaba wajen kare gaskiya, dimokiraɗiyya da haƙƙin jama’a na a saurare su. Labarin sa da na kafafen yaɗa labarai a Nijeriya abu guda ne – tarihin juriya da tsayin daka.”

Idris ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu tana ci gaba da nuna amincewa da kafafen yaɗa labarai a matsayin abokan hulɗa wajen sake gina ƙasa. Ya jero wasu daga cikin sauye-sauyen tattalin arzikin da ake aiwatarwa kamar cire tallafin mai, daidaita farashin naira, da kuma shirin sabunta tsarin haraji, waɗanda a cewar sa suna daga cikin matakan da za su tabbatar da ɗorewar bunƙasar tattalin arziki.

Ya ƙara da cewa: “Ana ɗaukar matakai masu wahala amma da muhimmanci don gina ƙasa mai ƙarfi. Irin wannan ya yi nasara a Legas, kuma da rahoton ku na gaskiya da adalci, zai yi nasara a Nijeriya ma.”

Ministan ya sake jaddada aniyar gwamnati wajen kare ‘yancin kafafen yaɗa labarai, inda ya bayyana cewa fiye da tashoshin rediyo da talbijin 1,000 ke aiki a faɗin ƙasar nan ba tare da tsangwama ko takunkumi ba.

Ya ƙara da cewa tun bayan hawan mulkin Shugaba Tinubu, babu wata kafar yaɗa labarai da aka rufe ko aka hukunta saboda bayyana ra’ayin ta.

Ministan ya jaddada cewa amincewar duniya da Nijeriya a fannin yaɗa labarai tana ƙaruwa, inda ya kawo misalin kafa Cibiyar Ilimin Kafafen Yaɗa Labarai ta Duniya (IMLI) a Nijeriya, wanda ya ce zai ƙara bayyana ƙasar a matsayin jagora a nahiyar Afrika wajen yaɗa sahihan bayanai da aikin jarida na ƙwarai.

Ya roƙi ‘yan jarida, musamman editoci, da su ci gaba da zama abokan cigaban ƙasa, tare da bayyana gaskiya, adalci, da kyakkyawar fata a labaran su.

Ya ce, “Wannan gwamnati ta yi imani da ƙarfin kafafen yaɗa labarai wajen tsara tunani da ƙarfafa fata. Muna gayyatar ku da ku shiga cikin tattaunawa mai fa’ida, ku yi s**a cikin girmamawa, kuma ku haɗa kai da gwamnati wajen zurfafa dimokiraɗiyya.”

Ya ce haɗin kai tsakanin gwamnati da kafafen labarai muhimmi ne wajen bunƙasa haɗin kan ƙasa da cika alƙawarin Shirin Sabunta Fata.

Jami’ar Tarayya ta Dutse Ta Karɓi Naira Miliyan 867 Don Tallafin Kuɗin Dalibai 7738 Daga NELFUNDJami’ar Tarayya ta Dutse...
12/11/2025

Jami’ar Tarayya ta Dutse Ta Karɓi Naira Miliyan 867 Don Tallafin Kuɗin Dalibai 7738 Daga NELFUND

Jami’ar Tarayya ta Dutse (FUD), dake Jihar Jigawa, ta bayyana cewa ta karɓi jimillar N867,381,000 daga Hukumar Tallafin Kuɗin Karatu ta Ƙasa (NELFUND) domin biyan kuɗin karatu na dalibanta.

A cewar wata sanarwa da Babban Akanta (Bursar) na jami’ar, Malam Hassan Balarabe, ya fitar a ranar 10 ga watan Nuwamba, an bayyana cewa kuɗin sun haɗa da N844,273,000 da aka ware wa ɗalibai 7,546, da kuma N23,108,000 ga dalibai 192.

Balarabe ya ce jimillar kuɗin da aka samu ya kai N867,381,000, wanda aka riga aka tura don biyan kuɗin waɗannan dalibai a ƙarƙashin tsarin tallafin da gwamnatin tarayya ta ƙaddamar.

Ya ƙara da cewa jami’ar na godiya ga gwamnatin tarayya da hukumar NELFUND bisa wannan taimako da zai rage wa ɗalibai da iyayensu nauyin kuɗin karatu, tare da ƙarfafa ci gaba da karatu cikin kwanciyar hankali.

Hanyoyin diflomasiyya suna aiki tsakanin Nijeriya da Amurka, inji Ministan Yaɗa LabaraiMinistan Yaɗa Labarai da Wayar da...
11/11/2025

Hanyoyin diflomasiyya suna aiki tsakanin Nijeriya da Amurka, inji Ministan Yaɗa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa hanyoyin diflomasiyya suna aiki yadda ya kamata wajen daidaita dangantaka tsakanin gwamnatin Nijeriya da ta Amurka.

Idris ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin "The World With Yalda Hakim" na gidan talbijin ɗin Sky News da ke Birtaniya, inda ya ce, “An buɗe hanyoyin sadarwa, kuma zan iya tabbatar da hakan; muna magana da su, kuma ina ganin suna fara fahimtar halin da ake ciki. Muna ganin cewa yawancin bayanan da suke samu sakamakon rashin cikakkiyar fahimta game da bambance-bambancen da kuma sarƙaƙiyar matsalar da muke fuskanta.”

Ministan ya kuma danganta wata ƙungiyar ‘yan ta’adda da aka haramta a Nijeriya da wasu masu neman goyon bayan gwamnati a Amurka, waɗanda ake zargin suna yaɗa bayanan ƙarya ga hukumomin Amurka.

Ya ce: “Ina so in bayyana cewa mun gano kai-tsaye akwai alaƙa tsakanin masu neman goyon bayan gwamnati a Amurka da wata ƙungiyar ta’addanci da aka haramta a Nijeriya. Mun kuma ga yadda s**a kafa wannan gungun neman goyon baya a Amurka, suna tuntuɓar manyan jami’an gwamnati domin su taimaka musu wajen neman goyon bayan.”

Ministan ya jaddada cewa gwamnatin Amurka ta daɗe tana goyon bayan Nijeriya wajen yaƙi da ta’addanci, kuma yanzu ma ƙasar nan tana buƙatar irin wannan haɗin kai.

Ya ce: “Abin da muke faɗa shi ne, e, lallai muna da matsaloli a Nijeriya, muna da rikice-rikice da matsalolin tsaro, amma a baya gwamnatin Amurka ta taimaka wajen magance irin waɗannan matsaloli. Don haka, muna kira gare su da su sake haɗa kai da mu domin mu kawo ƙarshen wannan matsala gaba ɗaya.”

Ya bayyana cewa Nijeriya ta yi mamakin wasu bayanai da ke fitowa daga Amurka da matsayin su kan wannan batun, yana mai cewa dole ne ƙasashen duniya su fahimci yanayin musamman da Nijeriya take ciki.

Ya ce: “Muna son mu shaida wa duniya cewa abin da ake yaɗawa ba haka yake ba. Muna jin damuwar ‘yan ƙasa da kuma damuwar ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, kan wasu kashe-kashen da ke faruwa, amma abin da muke nema yanzu shi ne fahimtar sarƙaƙiyar yanayin da muke ciki.”

Idris ya kuma yi shakku kan sahihancin bayanan da ake yaɗawa da ke nuna cewa ana nuna bambancin addini a Nijeriya, inda ya ce waɗannan bayanan “ba za su iya tabbatuwa ba idan an tantance su a kimiyyance.”

Ya tabbatar da cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadi ‘yancin addini, kuma ƙasar na ci gaba da kasancewa ƙasa mai addinai daban-daban duk da cewa wasu rikice-rikice suna faruwa, waɗanda ba su da nasaba da wariyar addini.

Gwamnati Ta Roƙi ‘Yan Nijeriya Su Kwantar da Hankali Kan Rikicin Diflomasiyya da AmurkaGwamnatin Tarayya ta buƙaci ‘yan ...
10/11/2025

Gwamnati Ta Roƙi ‘Yan Nijeriya Su Kwantar da Hankali Kan Rikicin Diflomasiyya da Amurka

Gwamnatin Tarayya ta buƙaci ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankalin su dangane da rikicin diflomasiyya da ake ciki tsakanin Nijeriya da Amurka.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya yi wannan kiran a garin Dutse, Jihar Jigawa, yayin ziyarar ban-girma da ya kai wa Gwamnan Jihar, Malam Umar A. Namadi.

A cewar sa, “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana da duk abin da ake buƙata don kare Nijeriya daga masu neman tayar da hankali, tare da gyara duk wata ɓaraka da ta taso tsakanin ƙasar mu da abokan hulɗar mu na ƙasashen waje. Don haka ina roƙon ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankalin su.”

Idris ya je Jihar Jigawa ne domin halartar Taron Matasa na Arewa-maso-yamma na shekarar 2025 da kuma gabatar da nasarorin da Shugaban Ƙasa Tinubu ya cimma bayan shekaru biyu a kan mulki.

Shugaba Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, murnar cika shekaru 70Shugaban Ƙasa, Bola Ahme...
10/11/2025

Shugaba Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, murnar cika shekaru 70 da haihuwa.

A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin a Abuja, Shugaba Tinubu ya yaba da rawar da Shekarau ya taka a fagen hidimar jama’a da kuma siyasa a Najeriya.

Shugaba Tinubu ya bayyana Shekarau a matsayin ƙwararren jami’in gwamnati wanda ya fara aiki a matsayin malami, kafin daga baya ya zama babban sakatare a ma’aikatar jihar Kano, sannan daga bisani ya shiga siyasa a farkon shekarun 2000.

Ya kuma bayyana nasarar da Shekarau ya samu a zaɓen gwamnan Jihar Kano a shekarar 2003, tare da irin tsarin mulkinsa na kula da walwalar jama’a a tsawon wa’adin mulkinsa biyu.

Bayan ya kammala mulkinsa, Shekarau ya yi aiki a matsayin Ministan Ilimi tsakanin 2014 da 2015, sannan daga baya aka zaɓe shi Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya daga 2019 zuwa 2023.

Shugaba Tinubu ya gode wa Shekarau bisa gudunmawar da ya bayar ga ci gaban ƙasa a matsayin malami, jami’in gwamnati, da kuma ɗan siyasa mai kishin ƙasa.

Ya yi addu’a ga Allah Ya ba shi lafiya da ƙarfi domin ci gaba da hidima ga al’umma da ƙasarsa baki ɗaya.

Gwamnatin Tarayya ta rage kuɗin aikin Hajjin bana na shekarar 2026. Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da rage ku...
10/11/2025

Gwamnatin Tarayya ta rage kuɗin aikin Hajjin bana na shekarar 2026.

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da rage kuɗin aikin Hajji na shekarar 2026 ga mahajjata daga sassa daban-daban na ƙasar, inda aka samu sauƙin kuɗi idan aka kwatanta da na bara.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, an bayyana cewa mahajjata daga yankin Borno da Adamawa za su biya Naira miliyan 7,579,020.96, maimakon Naira miliyan 8,327,125.59 da s**a biya a 2025, ragun da ya kai Naira 748,104.63.

Haka kuma, masu niyyar tafiya daga yankin Arewa za su biya Naira miliyan 7,696,769.76, wanda ke nuna ragin Naira 760,915.83 daga kuɗin bara da ya kai Naira miliyan 8,457,685.59.

A ɓangaren masu tafiya daga Kudancin ƙasar kuwa, farashin da aka sabunta na 2026 shi ne Naira miliyan 7,991,141.76, raguwar Naira 792,943.83 daga kuɗin 2025 da ya kai Naira miliyan 8,784,085.59.

Hukumar ta ce wannan ragin kuɗi na zuwa ne sakamakon ƙoƙarin da gwamnati da hukumomin da abin ya shafa suke yi domin sauƙaƙa wa alhazai, tare da tabbatar da cewa farashin bai zama cikas ga masu niyyar gudanar da ibadar Hajji ba.

NAHCON ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki tare da hukumomin Saudiyya da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da shirin Hajji na 2026 ya gudana cikin nasara da tsari.

Gwamnatin Tarayya ta ce farashin kayan abinci ya sauka ne sakamakon manufofin karfafa kasuwa da nufin farfado da nomaGwa...
09/11/2025

Gwamnatin Tarayya ta ce farashin kayan abinci ya sauka ne sakamakon manufofin karfafa kasuwa da nufin farfado da noma

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa raguwar farashin kayan abinci da ake gani a kasuwanni a ‘yan kwanakin nan, na da nasaba da manufofi da matakan musamman da aka dauka domin gyara harkar kasuwa da karfafa samar da abinci a cikin gida.

Ministan Noma da samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a yayin taron majalisar noma ta kasa karo na 47 da aka gudanar a Kaduna, ranar Alhamis 6 ga Nuwamba, 2025.

A cewar ministan, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dauki alkawarin tabbatar da ikon cin gashin kai a fannin abinci, inda Najeriya za ta rika samar da abincin da take ci, tare da tabbatar da wadatar kayayyaki a farashi mai sauki.

Ya ce, “Mun riga mun fara ganin sakkowar farashin wasu muhimman kayan abinci a kasuwa, wanda hakan ke nuna tasirin matakan da gwamnati ta ke dauka. Ko da yake ba mu kai inda muke so ba tukuna, amma wannan alamar tana tabbatar da cewa muna tafiya a madaidaiciyar hanya.”

Kyari ya bayyana cewa shirin National Agricultural Growth Scheme–Agro-Pocket (NAGS–AP), wanda ake aiwatarwa tare da hadin gwiwar Babban Bankin Raya Afirka (AfDB) da jihohi, shi ne ginshikin inganta samar da kayayyakin noman da kuma bunkasa amfanin gona.

Ya ce yawan jahohin da ke noma alkama ya karu daga 15 a zangon damina na 2023/2024 zuwa karin jihohi a zangon 2024/2025. Haka kuma, a watan Oktoba da ya gabata, an kaddamar da noman Alkama na rani (rainfed wheat) a Kuru, Jihar Filato, wani sabon salo da Cibiyar Binciken Tafkin Chadi ta kirkiro domin ba da damar noman alkama ba tare da dogaro da ban ruwa ba.

Ministan ya kara da cewa, “Wannan sabuwar fasaha za ta bai wa Najeriya damar yin noman alkama a ko’ina cikin shekara, musamman a yankunan Filato, Taraba da Kuros Riba, wanda zai taimaka wajen cimma burin wadatar alkama a gida.”

Don rage asarar amfanin gona bayan girbi da daidaita farashin kayayyaki, gwamnati ta kaddamar da Nigeria Postharvest Systems Transformation Programme (NiPHaST) tare da Alliance for a Green Revolution in Africa (AGRA).

Kyari ya kuma bayyana cewa gwamnati ta amince da Naira tiriliyan 1.5 domin sake karfafa Bankin Noma (Bank of Agriculture), tare da karin Naira biliyan 250 da za a ware domin tallafawa kananan manoma.

Haka kuma, an kaddamar da shirin national mechanisation programme tare da hadin gwiwar Heifer Nigeria domin taimakawa matasa da mata su kafa cibiyoyin injinan noma a dukkan yankunan kasar.

A nasa bangaren, Karamin Ministan Noma da samar da Abinci, Sanata Dr. Aliyu Sabi Abdullahi, ya bukaci a rungumi climate-smart agriculture, wato dabarun noma masu jituwa da yanayi domin dorewar samar da abinci.

Ya bayyana wasu muhimman shirye-shirye kamar shirin noman damina mai fadin hekta dubu 500, shirin samar da ruwa ta hasken rana, da kuma “Every Home a Garden” da uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu ke jagoranta, domin karfafa noman gida.

A jawabinsa na bude taron, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce, “A wannan lokaci da muke ciki, batun samar da abinci ya wuce batun manufa kawai, ya koma batun rayuwa da dorewar kasa.”

Ya bayyana cewa karkashin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu, gwamnati ta sanya noma a matsayin jigon tattalin arzikin kasa, ta hanyar inganta sarkar samar da kayayyaki, da sabunta kayan more rayuwa a karkara.

Gwamnan ya ce, a Kaduna, gwamnati ta mayar da noma “ba wai sana’a kawai ba, amma ginshikin cigaba da tushe na walwala.”

Kafin bude taron, ministoci da jami’an ma’aikatar sun kai ziyarar gani da ido zuwa wasu cibiyoyin noma kamar De-Branch Farmers, Afrexim Bank Quality Assurance Centre, Olam Agri, Tomato Jos, da TMDK Agro Park, inda s**a yaba da irin ci gaban da ake samu wajen kirkire-kirkire da samar da ayyukan yi a karkara.

An kammala taron da bayar da lambar yabo ga manoma da ‘yan kasuwa da s**a nuna bajinta a fannin noma da bunkasa abinci a kasar.

Kungiyar Tarayyar Afirka ta gargadi Amurka kan tsoma baki cikin lamurran Najeriya tare da kira ga tattaunawar Diflomasiy...
08/11/2025

Kungiyar Tarayyar Afirka ta gargadi Amurka kan tsoma baki cikin lamurran Najeriya tare da kira ga tattaunawar Diflomasiyya

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta bayyana goyon bayanta ga cikakken ikon Najeriya kan harkokinta na cikin gida tare da tabbatar da ’yancin addini da bin doka da oda a kasar.

A wata sanarwa da Hukumar Tarayyar Afirka (AUC) ta fitar, ta jaddada cewa tana da cikakken kishin kiyaye dokokin da ke cikin kundin kafa kungiyar, musamman kan batun ikon kasa, rashin katsalandan, da ’yancin addini.

Hukumar ta ce ta damu da wasu kalamai daga gwamnatin Amurka da ke zargin gwamnatin Najeriya da hannu wajen kashe mabiya addinin Kirista a kasar, da kuma barazanar kai farmakin soja kan kasar.

A cewar sanarwar, Najeriya na daga cikin mambobin AU masu muhimmanci wadanda ke taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya, yaki da ta’addanci, da hadin kai a nahiyar.

“AU tana mutunta cikakken ikon Najeriya wajen tafiyar da lamurran tsaronta, tsaron kasa, da ’yancin addini bisa tsarin kundin mulki da ka’idojin kasa da kasa,” in ji sanarwar.

Hukumar ta ce ta amince da matsayar da gwamnatin Najeriya ta sha nanatawa cewa kundin tsarin mulkin kasar yana baiwa kowane dan kasa ’yancin yin addinin da yake so, kuma gwamnati ba ta amince da wani nau’in wariya ko zaluncin addini ba.

Ta kuma jaddada cewa matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta na da sarkakiya, suna shafar mabiya addinai daban-daban, ciki har da matsalar ta’addanci, satar mutane, rikicin kabilanci da rikicin makiyaya da manoma.

Hukumar ta yi kira da a kara hadin kai tsakanin kasashen yankin da abokan hulɗa na kasa da kasa domin taimakawa Najeriya da sauran kasashen Afirka wajen karfafa matakan tsaro, kare rayuka, da gurfanar da masu aikata laifuka.

“Ya zama wajibi a guji amfani da addini a matsayin makami na siyasa ko bayanin da zai iya haifar da rikici,” in ji AUC.

Hukumar ta kuma bukaci kasashen waje, musamman Amurka, da su ci gaba da tattaunawa da Najeriya ta hanyar diflomasiyya, musayar bayanan tsaro, da taimakon ci gaban ƙwarewa maimakon barazanar kai farmaki, wanda ka iya barazana ga zaman lafiyar nahiyar.

A karshe, Hukumar Tarayyar Afirka ta tabbatar da aniyarta ta ci gaba da tallafawa kasashen mambobinta wajen tabbatar da zaman lafiya, kare hakkin dan Adam, da cigaban tattalin arziki, tare da mutunta ikon kowace kasa da ka’idar rashin tsoma baki.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙuncin mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Saad Abubakar III a yau Ju...
07/11/2025

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙuncin mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Saad Abubakar III a yau Juma'a a fadar A*o Rock dake Abuja.

Tinubu: Gwamnatin Najeriya Na Ci Gaba da Tattaunawa da Kasahen Duniya Ta Hanyar DiflomasiyyaShugaban Ƙasa Bola Ahmed Tin...
06/11/2025

Tinubu: Gwamnatin Najeriya Na Ci Gaba da Tattaunawa da Kasahen Duniya Ta Hanyar Diflomasiyya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya na kan hanyar ci gaba da tabbatar da alaƙar diflomasiyya, yayin da manufofin tattalin arziƙin gwamnati ke fara haifar da sakamako mai gamsarwa a gida da kuma ƙasashen waje.

Shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) a ranar Alhamis, bayan rantsar da sabbin ministoci biyu, Dr. Bernard Mohammed Doro da Dr. Kingsley Tochukwu Udeh (SAN). Doro zai jagoranci Ma’aikatar Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, yayin da Udeh zai rike Ma’aikatar Kirkire-Kirkire, Kimiyya da Fasaha.

Tinubu ya ce gwamnatin sa tana ci gaba da yin mu’amala da sauran ƙasashe ta hanyar diflomasiyya, duk da kalubalen siyasa da ake fuskanta.

Game da batun tsaro, Tinubu ya ce gwamnati ba za ta lamunci rashin zaman lafiya ba, yana mai tabbatar da cewa Najeriya za ta yaƙi ta’addanci gaba ɗaya.

“muna da matsaloli, muna fama da ta’addanci. Amma za mu ci nasara a kansu. Za mu tabbatar da an tsabtace ƙasar nan daga miyagun laifuka. Muna buƙatar abokanmu su taimaka mana, domin mu kawar da ta’addanci,” in ji shi.

A zaman majalisar, Shugaban Ƙasar ya umurci Ministan Kuɗi, Wale Edun, da ya gabatar da rahoton cigaban tattalin arziƙin ƙasar.

Edun ya bayyana cewa rahoton tattalin arziƙi ya nuna ƙaruwa sosai, inda ya ce ci gaban GDP na Najeriya ya kai kashi 4.23 cikin 100 a zangon na biyu na shekarar 2025, kaso mafi girma cikin shekaru goma.

Ya ƙara da cewa bangaren masana’antu ya kusan ninka ci gaban da ya samu daga kaso 3.72% zuwa kaso 7.45%, yayin da hauhawar farashin kaya ya sauka zuwa kashi 18.02% a watan Satumba, kuma ajiyar kuɗin ƙasar ya kai dala biliyan 43.

“An kuma samu riba ta kasuwanci ta naira tiriliyan 7.4, alamar da ke nuna tattalin arziƙi na samun kwanciyar hankali. Yawan kuɗin da jama’a ke kashewa wajen abinci, sutura da zama ya ragu daga kashi 90 cikin 100 zuwa kusan rabin abin da ake samu, alamar cigaba daga rayuwar dogaro da kai zuwa ci gaban arziki,” in ji Edun.

Ya ce hangen nesan gwamnatin Tinubu na cimma tattalin arziƙin dala tiriliyan ɗaya nan da 2030 abu ne mai yiwuwa, muddin ana ci gaba da samun ci gaban kashi 7% a duk shekara.

Edun ya kuma bayyana cewa nasarar Eurobond da aka fitar jiya ta dala biliyan $2.35, wadda ta jawo buƙatar Naira ta sama da $13 biliyan, ta nuna yadda masu saka jari ke sake amincewa da shugabancin Tinubu da manufofin gwamnati.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da neman hanyoyin da za su tabbatar da ci gaba mai ɗorewa, musamman ta hanyar haɗin gwiwa da jihohi don tabbatar da ayyuka masu amfani ga jama’a da jawo jari.

Address

Maiduguri

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Northeast Online News 24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share