
28/03/2025
Da farko dai, Muna Mika Ta’aziyya ga yan uwan da Abokanan Arziki da ilahirin Mutanen Arewa a bisa Waenda wannan Ibtila’in Kisan Gilla a Faru dasu a Wani Gari a Edo State.
Nayi Mutukar Girgiza, Zuciyata ta kasa Ganin wannan Kisan Gillan da wasu bara gurbi mutanen kuma fa Yan Nigeria ne, waenda zuciyansu ya kekashe, wa’enda talauci yayi musu katutu a zuciyansu , saboda kwai kishi na jahilci akan su yan Arewa ne!
Na tsani Nuna Kabilanci ko na bangaren yare, Ko na Addini ko kuma Jinsi, ko kuma na Gari, wannan Abun ba karamin koma baya yake jawo wa a harka rayuwa da cigaba ba.
Wannan kisan Gillan ya wuce misali, ya firgitani, kuma nashiga dimuwa matuka! Kuma insha Allah muna magana da Manya manya Hukumomi, Kungoyoyin Kare hakkin bil’adam da kuma wasu masu kishin Arewa don samun matsaya akan wannan ibtila’in.
Haka kawai K**a Mutum da Ran shi, ka daure shi, ka saka shi cikin taya, ka zuba mishi petroluem ko kalanzir, ka Ketta masa wuta, kuma kashe shi , kana kallonsa yana ihu yana kuka kaikuma kana mishi Dariya har sai kaga ranshi ya fita, batare da wata Dalili ba kuma kai ba Hukuma ba!
Kai wannan Abu yayi muni!
Insha Allah sai mun bi kadin hakkin waenaan bayin Allah.
Muna Kira ga Jami’an tsaro da gaggauta Kamo waenda s**ayi wannan Kisan Gillan don girban Abunda s**a aikata.
Daga