05/09/2021
RUWAN KOGI NA YUNKURIN MAMAYE ILAHIRIN WANI YANKI A GARIN JUMBAM DAKE KARAMAR HUKAMR TARMUWA LG. A JAHAR YOBE ,
Daga Kungiyar Arewa Media Writer's Reshen Karamar Hukumar Bursari LG.
Ruwan kogi na yunkurin shiga gida jen mutane a garin Jambam daka jahar Yobe , Wanda ruwan a halin yanzu Yana yiwa al'umar garin Jambam barazana , Hakan yasa al'umar garin cikin tashi hankali da firgici.
Inda wani mazaunin garin ne yake Shedawa Wakilan mu da s**a ziyarci Garin,
Sannan kuma shi mazauni garin ya sheda mana cewa ruwan kogin bashi ne karo Na farko ba da yake musu barazanar shiga cikin garin nasu,
A shekarar 2019 ruwan yashiga garin Sannan yayiwa jam'ar garin barna sosai wanda hakan ya jawo asara sosai a harkar Noma da kuma sauran dukiyoyi Al'ummar garin.
al'umar garin Suna bukatar taimakon gwamnati Sabida yadda Ruwan kogin da yazo a wannan shekarar yafi na shekarar baya, Sabida suna gani yadda ruwan ya fusata, Da yinkurin mamaye ilahirin yakin da ruwan yake,
Al'ummar garin Jumbam suna Kara godiya da nuna Farin cikin ga Gwamnati Jahar Yobe Kar kashin jagoran cin Mai girma Gwamna Mai Mala Buni. Bisa Irin kokarin da yamusu a Karon Farko Na samar musu magudanar ruwa na Kolbati,
Amma har a halin Yanzu Al'ummar garin Jumbam suna bukatar tallafin gwamnati sosai Sabida ruwan Ba irin wanda zasu meke kafa su zauna bane dole sutashi su tsaya dan neman tallafin mai girma Gwamna jaha.
Muna Kira da babban murya da mai girma Gwamna jahar Yobe da ya karkato da hankalin wakilan sa masu bada tallafin gaggawa zuwa garin jumbam domin basu tallafin,
Sabida garin jumbam Yana daga cikin manyan Ward da Tarmuwa Local Govt take jida da shi, Duba da yadda s**a futo kwansu da korkotan s**a Zabe Mai girma Gwamna Jaha.
Rubutawa✍🏽✍🏽 YUSUF FINANCE Shugaban Kungiyar Arewa Media Writer's. Reshen Bursari LG Yobe Chapter