Arewa updates

Arewa updates Arewa Hausa updates

20/10/2024

Hadisi ne zan karanta muku Amma ina neman alfarma guda awajenku kafin ku karanta Hadisin nan... Alfarmar da nake nema awajenku ita ce, ku tsayar da duk abinda kukeyi, ku nutsu ku karantashi da kyau.
Domin na tabbata sai ya girgiza zuciyar duk wani mai Imani.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Tsira da aminci su tabbata bisa Annabin Karshe, da dukkan Iyalansa da Sahabbai baki daya.

Yazeedur Raqqaashiy ya karbo Hadisin daga Anas bn Malik (R.A) yana cewa:
Watarana Mala'ika Jibreelu (A.S) yazo wajen Manzon Allah (S.A.W) awani lokacin da bai saba zuwa masa ba. Yazo, gaba dayan launin fuskarsa
ya canza. Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa "MAI YASA NAGA LAUNIN FUSKARKA DUK YA CANJA HAKA?".
Yace "Ya Muhammadu (S.A.W) nazo maka ne awannan lokacin da Allah yayi Umurni da Masu hura wuta suci gaba da Hura ta.
Duk wanda yasan cewa Jahannama gaskiya ce, Wuta gaskiya ce, Azabar Kabari gaskiya ce, kuma Azabar Allah ita ce mafi girma, to bai kamata yayi wani farin ciki ba har sai ya tabbatar da cewa ya samu tsira daga wannan".
Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa "YA JUBREELU INA SO KA SIFFANTA MUN YADDA
JAHANNAMA TAKE".
Sai yace "Na'am. Hakika Allah madaukakin Sarki yayin da ya halicci Jahannama, yasa an hurata tsawon Shekaru DUBU. Har sai da ta zama JA -JAWUR.
Sannan aka sake hurata tsawon Shekaru DUBU har sai da ta zama FARI - FAT!!
Sannan aka sake hurata tsawon shekaru DUBU har sai da ta zama BAKA - KIRIN!!!.
Tana nan har yanzu BAKA KIRIN ce, mai tsananin duhu ce.
Harshen Balbalinta basu mutuwa ballantana Garwashinta.

Na rantse da Girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya, da ace za'a bude misalin kofar allura daga wutar Jahannama, Wallahi sai dukkan Ma'abotan doron duniyar nan sun kone baki dayansu saboda tsananin zafinta.

Na rantse da girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya, da ace za'a ratayo tufafi guda daya tufafin 'Yan Wutar Jahannama a makaloshi atsakanin Sararin Samaniya, da sai Dukkan Ma'abotan doron kasa sun Mutu baki dayansu saboda tsananin Warin wannan Tufafin.
Da kuma zafin dake tattare dashi. Babu wanda zai yi saura acikinsu don tsananin abinda zasu riska na zafin wannan tufafin.

Na rantse da girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya amatsayin Annabi, da ace za'a dauko zira'i guda na Sasarin nan na 'yan wuta (wato CHAINS din da ake daure su dashi sannan arika jansu ajan fuskarsu). Wannan Wanda Allah ya ambata Acikin Alqur'ani, a dorashi bisa wani dutse daga duwatsun duniyar nan, da sai dutsen ya narke ya zagwanye har zuwa Kasa ta bakwai.

Na rantse da girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya amatsayin Annabi, da ace za'a ajiye wani mutum a mafa'dar rana ana yi masa azaba, da sai wanda yake mahudar rana ma ya kone kurmus saboda bala'in zafinta. Zafinta mai tsanani ne. Zurfinta mai nisa ne.
Tufafin cikinta na karfe ne. Abin shan cikinta HAMIMU ne (tafasasshen ruwan azaba) da kuma ruwan Gyambo.
Mayafan cikinta kuma an yankosu ne daga Wutar".
Tana da Kofofi guda bakwai, Kowacce kofa tana da wani yankin cikinsu da aka tsaga mata (zasu shiga ta cikinta) daga Mazaje da mataye.
Sai Manzon Allah (saww) yace: "SHIN KOFOFIN NAN IRIN NAMU NE?".
Sai Jibreelu yace: "A'a sai dai ita kofofin abude suke, wata kofar tana kasan wata.
Tsakanin kowacce Kofa da wata kofar, tsawon tafiyar
shekara SABA'IN ne.
Kowacce kofa ta ninka wacce take sama da ita atsananin azaba har ninki SABA'IN.
Za'a rika kora makiyan Allah cikinta. Kuma duk sanda aka koro wasu ('Yan wuta) zuwa wata kofa, Zabaniyawa ne zasu tarbesu da Sarkoki da Sasarai. Za'a zira musu Sasari (chains) ta cikin bakinsu sai ya fito ta duburarsu. Sannan za'a daure hannunsa na haggu ajikin wuyansa, hannunsa na dama kuma za'a fasa Kirjinsa dashi aturoshi ta cikin zuciyarsa sai ya fito ta bayan kafadarsa. Sannan ahada adaure da wancan Sarkar.

Kowanne Dan Adam za'a hadashi tare da shaitani guda acikin Sarkar Sasarin, Sannan arika Jansa akan fuskarsa (acikin Garwashin wutar da kuma dagwalonta) Mala'iku kuma suna Jibgarsu da Gudumomin Baqin Karfe. Duk lokacin da s**a nemi fita daga cikinta saboda bakin ciki da wahala, Sai a sake dawowa dasu cikinta. Sai Annabi (S.A.W) yace ma Jibreelu (R.A) "SHIN
SU WANENE MAZAUNAN CIKIN WADANNAN KOFOFI?".
Sai Mala'ika Jibreelu yace: "Kaga amma Kofar nan wacce take chan Karkashin Kas, ita ce mazaunar Munafukai da kuma wadanda s**a kafirce daga Mutanen Annabi Eisa (A.S) (Wadanda aka ce kar su boye abinci amma s**ayi taurin kai s**a boye). Da kuma Mutanen Fir'auna.
Ita wannan wutar sunanta "HAAWIYAH".

Sai kuma Kofar nan ta biyu, wadanda zasu shiga cikinta sune MUSHRIKAI. Kuma sunanta "AL-JAHEEM".

Kofar ta uku kuwa masu bautar taurari ne zasu shiga ta cikinta. Sune mazaunan cikinta. (awani wajen ance zasu zauna tare da masu wasa da sallah). Kuma sunan wannan wutar "SAKAR".

Kofar wuta ta hudu, ta nan ne IBLIS (L. A.) zai shiga cikinta tare da Mabiyansa da kuma
Majusawa masu bautar Wuta.
Kuma sunanta "LAZAA".

Kofa ta biyar kuwa ta cikinta YAHUDAWA zasu shiga. Kuma sunanta "ALHUTAMAH".

Kofa ta shida kuwa, NASARA ne zasu shiga ta cikinta. kuma sunanta "SA'EER".

Daga nan kuma sai Mala'ika Jibreelu ya sunkuyar da kansa yayi shuru, ya kasa ci gaba da magana son jin kunyar Manzon Allah (S.A.W).
Sai Manzo (S.A.W) yace masa "SHIN BA ZAKA BANI LABARIN KO SU WAYE MAZAUNAN CIKIN WANNAN KOFAR TA BAKWAI DIN BA?".
Sai Jibreelu yace: "Sune Ma'abotan Manyan Zunubai daga cikin al'ummarka. Idan har s**a mutu basu tuba ba" Nan take Sai Sayyiduna Rasulullahi (S.A.W) ya fadi YA SUMA!!!!
Sai Mala'ika Jibreelu ya dauki kansa ya dora akan cinyoyinsa har sai da ya farfado sannan
yace:
"YA KAI JIBREELU LALLAI MUSIBA-TA TA GIRMA!
KUMA BAKIN CIKINA YA TSANANTA!!! YANZU ASHE AKWAI WANDA ZAI SHIGA WUTA DAGA CIKIN AL'UMMATA?".
Sai yace "Eh amma Ma'abotan Manyan zunubai daga cikinsu".
Daga nan Sai Manzon Allah (S.A.W) yasa kuka, Mala'ika Jibreelu ma yana kuka...!!!".
Ibnu Katheer ya kawo wannan hadisin da ruwayoyi daban daban acikin Littafinsa mai suna AN-NIHAYAH FIL FITAN WAL MALAHIM. Acikin
babin dake magana akan wuta da azaba cikinta.

Allah (S.W.T) Ya yafe mana zunuban mu manya da kanana.
Amin. Manzon Allah (S.A.W) yanacewa mutanen dake kusa dani a ranar tashin Alkiyama sune masu yawan yi min salati! Allahumma salli Ala Muhammad wa sallim!

Ya Allah muna rokonka da sunayenka tsarkaka, don darajar Al'arshi, don girman mulkinka Allah, don soyayyar ka da Annabi Muhammad (S.A.W) duk wanda ya tura wannan sakon ga yan'uwa musulmai ya Allah kaji kansa, ka gafar ta masa, ka daukakashi duniya da lahira...

Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum🙏

19/08/2024

NO RESULTS? Keep working
BAD RESULTS? Keep working
GREAT RESULTS? Keep working
THE CONSISTENCY IS KEY

19/08/2024

*X AND .

By Zainab Abdumalik

A man can have s*x with a lady and still don't have any feelings for her, men only need space to have s*x but women need reason to have s*x.

A woman cannot have s*x without feelings except s*x workers. A man can travel for eight hours 'just to have s*x with a female friend and yet, not love her. S*x makes men act as if they are in love while they are not. The eight hours travel sacrifice, gifts bought, hotel paid for and other expenses may seem to be coming from true love but they were all in the sacrifice for s*x and nothing more.

The foolish thing is this, the majority of women would jump up inside them and conclude that this is the art of true love.
S*x is not an act of commitment. Men still leave the women they sleep with on bed and start thinking of the next woman to sleep with. The satisfaction that comes from s*x dies in minutes. It is in the nature of Lions to go miles to hunt. The same with men. A man who can afford the expenses of flying from the UK to Nigeria for s*x would do it as if he would never turn to another woman for s*x.

S*x drives men to do what seems like the impossible and such turns women around and they start acting weird. S*x and love are not on the same page even in the dictionary. People can abandon their gold mines and dig the grave for s*x. Most young men do terrible things just to have the resources to keep many girls in their life.

You may think they are working hard to live well in the future but they are just living for fun and that is all. Students are now living together like husbands and wives, and our society calls it love. What kind of people do these students become when they leave school?
This is why we have a lot of frustrated graduates than nations building graduates.

Today, a 16-year-old girl is already into s*x. She wants to wear everything on trend. She is already a pr******te in the sense that any man that comes her way for relationship must show some signs of money and she would respond to him.

The funny thing is this, almost all those girls that have become s*x symbols end up in a deep mess. How many of them today is changing the world they are into? What kind of spirit would they do well within life? They have sold their souls out to s*x. They pride on what they wear and hotels they go to. That is their biggest achievement. The girls they called cowards are setting up economic empires. Their future is already exhausted when they come to their true senses?

Advice to my beloved brothers and sisters:
For men; never allow your er****on today to destroy your future directions, stay positive.
My sisters, all that glitters is not gold, make your future bright and its start today.

I am not posting this to make anyone guilty or stand as a judge. We have turned Eid and other festivities to S*xual seasons instead of The season of Grace n Mercy.

Let us fear Allah" if you don't fear Allah, you can't please HIM. " If you know how to please Allah, what you're looking for, will be looking for you.

DA DUMI DUMINSU~Yau kimanin sati biyu an tsinci wani mai kimanin shekara biyu(2) da haihuwa a anguwan MUNA GAREJI dake G...
28/06/2022

DA DUMI DUMINSU~Yau kimanin sati biyu an tsinci wani mai kimanin shekara biyu(2) da haihuwa a anguwan MUNA GAREJI dake Garin Maiduguri Borno state haryanxu ba'a ga no iyayen wannan yaron ba
Dan Allah kuyi sharing saboda taimakawa iyayen wannan yaro 👌🙏

Address

Maiduguri

Telephone

+2349061699817

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa updates posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share