04/11/2025
🕊️ TA’AZIYA 🕊️
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. 😔
Da alhini da juyayi muke sanar da rasuwar😭 Malam Abubakar, mahaifin abokin aikimmu Capt. Adamu Abubakar, wanda yake rike da mukamin Deputy Director Finance, Jere LG FAG Fityanul Islam, Reshen Jihar Borno.
Marigayin ya rasu jiya a garin Damaturu, kuma ana sa ran gudanar da jana’izarsa yau da misalin ƙarfe 9:30 na safe. 🕘
A madadin Shugaban Rundunar ’Yan Agajin Kungiyar Fityanul Islam Reshen Jihar Borno, Brig. Gen. Muhammad Abdullahi Karaji, tare da dukkan ’yan agaji na jihar Borno baki ɗaya, muna mika ta’aziyya ga Capt. Adamu Abubakar da iyalansa bisa wannan rashi mai raɗaɗi. 💔
🙏Allah Ya gafarta masa kurakurai, Ya sa Aljanna Firdausi makomarsa 🕌, kuma Ya ba iyalansa haƙuri da juriyar wannan rashi. 🤲
Ameen. 🤍
✍️ Rabiu Babayo