
16/03/2025
Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da yake bude baki tare da malamai da limaman Jihar Kano.
Ban yi dana sanin rushe Masallacin Idi ba, saboda muggan laifukan da muka tarar ana aikatawa a ciki, kamar ajiyar makamai, store-store na giya. Wannan abin takaici ne a irin wannan masallaci mai tarihi.
In shaa Allahu, nan da bayan Sallah, za mu jagoranci tawagar malamai daga kowane bangare domin dasa harsashin gina cibiyar taron addinin Musulunci a Masallacin Idi na Kofar Mata.
Gwamna Alhaji. Abba Kabir Yusuf, ya kara da cewa, za mu gina wannan cibiya ta addinin Musulunci domin mika amanarta ga malamai, ta yadda duk lokacin da aka bukaci taron addinin Musulunci, ba sai an je filin wasa (stadium) ba.
Comr Muhammad M Alasan
For KKSY Reporters GHK.