
20/11/2023
YANZU-YANZU: Jarumin Masana'antar Shirya Fina-Finai ta Kannywood Aminu S Bono ya rasu.
Ya rasu a yammacin yau Litinin, bayan yanke jiki da yayi ya faɗi jim kaɗan bayan dawowarshi daga aiki.
Makusantanshi sun tabbatarwa da Premier Radio rasuwar jarumin masana'antar ta Kannywood.
Muna rokon Allah ya jikansa ya sa Aljanna makoma.