20/10/2025
JAN HANKALI Ga Mutanen Mu A Kan Labarin Yunkurin Juyin Mulki Da Jarida Mara kishin kasa Ta Fitar!
Duk da cewa labarin ba gaskiya bane, amma ya kamata mu wayar wa mutane kai.
Sun kirkiri wannan labari na kanzon kurege ne kawai don wata manufarsu, da kuma janye hankulan jama da sanya su a cikin tashin hankali, da sanya kasar cikin rudani.
ME YASA S**A SANYA SUNAN SAHARA REPORTERS!
Shin wannan jaridar bogi na sahara reporters, me yasa s**a sanya sunan sahara reporters kuma meye manufarsu?
Da farko dai mamallakin wannan jaridar bogi na online shine sunansa ‘omoyele sowore' wanda yake da daurin g¡ñdī daga gomnatin Amrika akan manufarsa ta adawa da kasarmu Nigeria.
Ya sanya sunan ‘sahara reporters' ne saboda kawai ya janye hankalin yan Arewa da hausawa a kan manufofin sa da yake yadawa, domin yasan cewa yan Arewa sunfi son “Namu Namune", daga jin sunan sahara, toh yasan cewa yan arewa zasu saki jiki da shi.
Baza kayi tunani ba meyasa bai sanya sunan ‘omoyele reporters' ba, ko ‘sowore reporters' ba, ko wani suna a turance? Duk da cewa kasan ba son arewa yake ba?
Manufarsa shine, adawa da kasar Nigeria🇳🇬 da zamanta na dunkulewa da zaman sa kasa guda daya.
Ya je ya samu goyan baya sosai daga gomnatin Amrika, wanda take taimaka masa a duk abin da zayyi.
Ya fi yawan wallafe wallafe a kan duk abin da zai saba da Nigeria, zakulowa yake ya dinga wallafa tarzoma, sabani, tashin hankali, kai hatta kiyayyarsa ga Nigeria bai bar addinai ba, lokuta da dama yakan sakin baki da wallafa mumunan abu a kan Muslinci.
Haka yakeyi tun kafun Yar'adua ya hau mulki, har yau bai daina ba, bai taba yabon wani shugaba ba a kan wani aikin kirki da yayi ba, baya goyan bayan duk manufofin gomnatin da kasar ko na kwayar zarra, sai nuna kiyayya.
Haka kwana kwanan nan ya zauna ya kirkiri labarin karya, mara tushe, mara asali, cewa wai wasu sojoji suna yunkurin jūyīn mūlkī, daga ji ma kasan karyar makaryaci.
Read full story in comment...