Dandal Kura

Dandal Kura Wannan Shine Shafin Dandal Kura Na Facebook. Zaku Iya Tura Mana Sako Ko Kuma Kukaranta Labarai.

Yadda wata babbar mota a yammacin yau ta bar hanyar ta san nan ta haura tsakiyar hanya a titin yankin custom dake birnin...
08/09/2025

Yadda wata babbar mota a yammacin yau ta bar hanyar ta san nan ta haura tsakiyar hanya a titin yankin custom dake birnin Maiduguri.

Hotuna: Usman

Big thanks to Muhd Lawan Hassan, Abba Mohammed Kukawa, Alaibor Alhaji Ali, Mustapha Suleiman Damai, Bukar Aisami, Ibrahi...
08/09/2025

Big thanks to Muhd Lawan Hassan, Abba Mohammed Kukawa, Alaibor Alhaji Ali, Mustapha Suleiman Damai, Bukar Aisami, Ibrahim Bukar, Ahmad Umar, Prince Isa, Bukar Attom, Ibrahim M Kasim, Haruna Mohammed Zarami, Aliyu Garba, Adamu Usman, Ahmad Idris, Alhjiali Mustapa, Ramatu Yahaya, Hussaini Mukhtar, Haruna Dahiru, Baba na shehu abulfatahi, Rawana Mele, Ibrahim Mohammed, Lawan Abba Umar, Itz Dan Saurayi, Mohammad Ali, Pherlmerterh Kimemi, Almukhtar K Jidda, Ismail Bukar, Ali Aisami, Mohammed Usman, Mohammed Abdullahi Hassan, Wujema Zanna Kambar, Ismail Muhammad Gana, Abba Goni Ibrahim, Muhammad Mustapha, Umar Goni Umar, Tarfa Yusuf, Goni Hassan Muhammad, Malah Gana, Bakura Maidugu, Ibrahim Bukar Gaji, Abbas Ali Gubio, Abubakar Musa Abdullahi

for all your support! Congrats for being top fans on a streak 🔥!

Gadar dake kusa da Post Office, daura da BRTV a yau 8/09/2025. Allah ya sa ya wuce lafiyaHotuna: Muhammad Lawan Rabiu
08/09/2025

Gadar dake kusa da Post Office, daura da BRTV a yau 8/09/2025. Allah ya sa ya wuce lafiya

Hotuna: Muhammad Lawan Rabiu

Butulci ko Gaskiya: Shin meye ra'ayinku game da batun Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani kan batun cewa: " Babu Abinda Elrufa...
08/09/2025

Butulci ko Gaskiya: Shin meye ra'ayinku game da batun Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani kan batun cewa: " Babu Abinda Elrufai Ya Koya Min A Siyasa Bare Har Ya Zama Ubangidana, Iyayen Gidana A Siyasa Sune Shugaba Tinubu Da Marigayi Gani Fawehinmi.

Ya kuke ganin wan nan batun?

Gwamnan Katsina Dikko Radda kenan da mukarrabansa yayin da s**a kai ziyara Kabarin tsohon Shugaba Kasa Muhammadu Buhari ...
08/09/2025

Gwamnan Katsina Dikko Radda kenan da mukarrabansa yayin da s**a kai ziyara Kabarin tsohon Shugaba Kasa Muhammadu Buhari a Daura dake a Jihar Katsina.

Yadda aka samu gawar wani Mutumi a jikin transformer ta wutar Lantarki a Jami'ar Jihar Borno.
08/09/2025

Yadda aka samu gawar wani Mutumi a jikin transformer ta wutar Lantarki a Jami'ar Jihar Borno.

Yadda rashin masu fassara alamomin magana ga masu bukata ta musamman (Sign Language) ke sa kurame rasa rayukansu a Borno...
08/09/2025

Yadda rashin masu fassara alamomin magana ga masu bukata ta musamman (Sign Language) ke sa kurame rasa rayukansu a Borno


Daga: Isah Ojo

A cikin wannan rahoto, an gano cewa rashin masu fassara harshen kurame a cibiyoyin kiwon lafiya ke dagula al’amuran kiwon lafiya, tare da kashe marasa lafiya da s**a hada da mata masu ciki masu nakasar kunne da magana.

Bangaren kiwon lafiya a Najeriya na fama da kalubale daban-daban irin wadannan, inda wan nan matsalar kadai tana lakume rayukan al'umma.

A cewar shugaban kungiyar kurame ta jihar Borno ta (Borno state Deaf Association) Adamu Bukar yace kurame da dama suna fuskantar irin wannan matsalar inda har wasu kan rasa rayukansu sakamakon rashin iya isar da sako yadda ya kamata musamman Mata a lokacin haihuwa.

Yaya batun sada zumunci yake a wajen ku tsakanin yan'uwa da abokan arziki, Kuna iya zuwa sosai kamar da ko dai kunayine ...
08/09/2025

Yaya batun sada zumunci yake a wajen ku tsakanin yan'uwa da abokan arziki, Kuna iya zuwa sosai kamar da ko dai kunayine ta wayar salula?
Ku bayyana Mana ra'ayoyinku domin mu karanta muku a cikin shirinmu na Rumfa Sha Shirgi.

Yau bayan sallar Isha’a da misalin karfe 9:00 na dare, in sha Allahu za a sami kusufin wata. Za a yi Sallar Kusufi a Masa...
07/09/2025

Yau bayan sallar Isha’a da misalin karfe 9:00 na dare, in sha Allahu za a sami kusufin wata. Za a yi Sallar Kusufi a Masallacin Harami da Masallacin Annabawi. Ana karfafa baki masu ziyara su tsaya bayan sallar Isha’a su halarci wannan sallah, domin ita sunnah ce daga Manzon Allah ﷺ.

Annabi ﷺ ya ce:“Lallai rana da wata manyan ayoyi ne daga cikin ayoyin Allah Maɗaukaki. Ba su yin kusufin saboda mutuwar ...
07/09/2025

Annabi ﷺ ya ce:

“Lallai rana da wata manyan ayoyi ne daga cikin ayoyin Allah Maɗaukaki. Ba su yin kusufin saboda mutuwar wani ko rayuwarsa. To idan kuka gan su, ku yi tasbihi ga Allah Maɗaukaki, ku roƙe shi da tawali’u, ku yi salla, kuma ku bayar da sadaka domin Allah.”

(Al-Bukhari da Muslim s**a rawaito)

A wannan Lahadi ta yau 7 ga Satumba, 2025, za a ga wani gagarumin kusufi na wata a fadin Najeriya da sauran kasashen Afi...
07/09/2025

A wannan Lahadi ta yau 7 ga Satumba, 2025, za a ga wani gagarumin kusufi na wata a fadin Najeriya da sauran kasashen Afirka da dama.

Lamarin da ke faruwa a sararin sama, wanda kuma aka fi sani da “bloody moon,” yana faruwa ne a lokacin da duniya ta zo tsakanin Rana da wata, inda inuwar ke rufe saman duniyar wata.

A Najeriya, kusufin zai fara ne da misalin karfe 6:31 na yamma agogon kasar inda wata zai shiga inuwar penumbral ta duniya.

Jimlar lokacin kusufin, wanda duniyar wata za ta rufe shi gaba daya, zai fara ne da misalin karfe 6:31 na yamma kuma zai wuce zuwa misalin karfe 7:52 na yamma, wanda zai dauki kusan mintuna 83. Ana sa ran kusufin gaba ɗaya zai ƙare da ƙarfe 9:55 na yamma.

Duk da cewa wata zai tashi bayan an fara kusufin a wasu sassan Najeriya, yankuna da s**a hada da Abuja da ne za su shaida yadda lamarin ke gudana, tun daga lokacin da aka yi kusufin har zuwa karshensa.

Wasu yankunan yammaci na iya rasa matakan farko saboda lokacin fitowar wata.

Masana kimiyya sun tabbatar da cewa wannan kusufin ana iya ganinsa da ido ba tare da wani abin hange ba.

Najeriya da sauran kasashe an karfafa su da su kalli sararin samaniya a wannan yammacin Lahadin nan don ko zasu kalli abin mamaki.

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN Yadda Boko Haram s**a yi barna a garin Darajamal dake Karamar Hukumar Bama a Jihar Bo...
07/09/2025

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN

Yadda Boko Haram s**a yi barna a garin Darajamal dake Karamar Hukumar Bama a Jihar Borno.

Allah ya kawo karshensu ya gafartawa wadanda s**a rasu, ya kuma bawa iyalansu hakurin jure wan nan rashin.

Address

Maiduguri

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dandal Kura posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Dandal Kura Radio

Dandal Kura Radio International gives voice to the people of North East Nigeria and the Lake Chad Basin that have gone through one of the most complicated insurgencies in History. Our lineup of programmes include entreprenuership, counselling, human rights, listener feedback, health and reconnection which are pillars to recovery, rehabilitation and re-integration efforts of the government and humanitarian organizations.

About half of our programmes are designed to be interactive and center around women that have been at the receiving-end of the insurgency. Our goal is to foster dialogue between all stakeholders to ensure a peaceful North East Nigeria and Lake-Chad basin Region