12/12/2023
Ba Ilimi Kadai Nake Buqata Baπ―π―π―
Tilas Ne Na Kasance Mai Gyara Zuciyata Da Aikata Kyawawan Ayyuka Da Kyautata Al'amura Tsakanina Da Ubangiji Allah Subhanahu Wata'ala.
Tilas Nayi Aiki Da Ilimi Bayan Na Same Shi, Tilasa Na Qasqantar Da KaiNa Zuwa Ga Allah Da Nuna Cewa Ilimi Na Bai Isa Komai Ba Agurin Allah Idan Ma Ina Da Ilimin,. Domin Tarin Ilimi Bai Hana Allah Hallakar Da Bil'ama Dan Ba'ura Ba, Haka Nan Tarin Bauta Bata Hana Allah Tsinewa (Azazilu ) Wato Iblis Ba,
Haka Nan Kusanci Da Allah Bai Hana Ya Hukunta Annabi Yunusa Ba, Da Zama Cikin Duhun Cikin Kifi Acikin Teku,
Saboda Haka Dole In Kiyayi Allah Inji Tsoron Sa Inyi Qoqarin Kyautata Al'amura Tsakanina Da Shi.
Amma Na Kan Ji Farin Ciki Idan Na Tuna Cewa Allah Shine Arrahmanu, Shine Gafururrahimu.
Nasihata Ni Da Kai Mai Karatu Gare Mu Mu Kiyayi Yiwa Allah Izgilanci Don Ilimi KO Dukiya KO Dukkanin Wata Ni'ima Da Allah Din Shine Yayi Mana Ita, Muyi Abun Da Yace Mu Bar Abun Da Ya Hana.
Ya Allah Ina Kuka Da Neman Tuba Gare Ka Da Qasqantar Da Kai Da Yarda Da Cewa Wallahi Ban Kai Komai Ba Gare Ka , Allah Ka Dube Ni Kadai Saboda Qaunar Da Nake Yiwa Masoyin Ka Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama Da Qoqarin Riqo Da Nake Da Littafin Ka Wanda Ka Bashi Matsayin Mu'ujiza Da Shari'ar Kaπ―π―ππππ