03/12/2025
TASWIRAR SAKE GINA RAYUWA A CIKIN WATA 6
Ina kalubalantar ka: Ba da kanka wata shida kacal.
Bace daga idon mutane, ka rage surutu, ka daina neman yabo, ka shiga "Dakin Horo" na gina kanka.
Ga abin da za ka yi:
Ka daina kallon ba¥sa,
ka Rage cin Suga,
Ka daina shaye-shaye
Ka daina c**a
ka Sha ruwa sosai,
ka Motsa Jiki,
ka daina zuwa club,
ka Guji 'Drama',
ka Yi shiga ta mutunci,
ka Nemi kudi,
ka Yi kamshi,
ka riƙe ibada,
Ka Nemi Mata ta Gari.
Idan ka bi wannan tsarin, za ka dawo sabon mutum wanda kowa zai yi sha'awa:
1. Tsara Ranarka Tun Daren Jiya
Kafin ka kwanta, rubuta abin da za ka yi gobe. Wannan yana sa ka tashi da shiri. Rayuwa tana yin sauki idan kana da taswira, ba wai ka tashi kana "Gwadawa" ba.
2. Dokar Minti 5
Idan akwai aikin da zai dauke ka kasa da minti 5 (kamar goge takalmi, gyara gado, ko tura sako), yi shi yanzu-yanzu. Tara kananan ayyuka yana haifar da kasala mai yawa daga baya.
3. Samar Da Tsarin Safiya (Morning Ritual)
Yadda ka fara safiyarka, haka ranarka za ta kare. Tashi da wuri (Asuba), yi sallah, yi motsa jiki, ko karanta Qur’ani ko wani littafi cikin littattafai. Kar ka fara rana da duba waya ko karanta labarin da zai bata maka rai.
4. Yi Aiki Da Dokar 80/20
Kashi 20% na ayyukanka su ne suke kawo kashi 80% na nasararka. Gano wadannan manyan ayyukan ka ba su karfi. Aiki da yawa ba shi ne "Productivity" ba, aiki mai amfani shine nasara.
5. Samu Hutu Mai Kyau
Jikinka shine injin aikinka. Idan baka hutu, injin zai lalace. Bacci mai kyau yana gyara kwakwalwa da jiki don ka tunkari gobe da karfi.
6. Sha Ruwa Lita 3 A Rana
Kashi 75% na jikinka ruwa ne. Ruwa yana wanke datti a jiki, yana sa fata ta yi kyau, kuma yana kara kuzari. Sha ruwa da zaran ka tashi daga barci.
7. Motsa Jiki (Exercise)
Ko sau 3 ne a sati, ka motsa jiki. Motsa jiki yana gyara yanayin jiki da na tunani. Jiki mai karfi yana daukar kwakwalwa mai kaifin tunani.
8. Neman Mace Ta Gari (The Ultimate Asset)
Wannan ita ce gishirin rayuwar. Namiji yana bukatar gida mai