Haske Newspaper

Haske Newspaper Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Haske Newspaper, Newspaper, BLK Maiduguri, Maiduguri.

FOLLOWING HASKE NEWSPAPER DAILY MAGAZINE  ................   Ku Miƙa Sunayenku ga Rundunar Ƴan Sanda - IG ga Jagororin Z...
27/07/2024

FOLLOWING HASKE NEWSPAPER DAILY MAGAZINE ................ Ku Miƙa Sunayenku ga Rundunar Ƴan Sanda - IG ga Jagororin Zanga Zanga na kowace Jiha

Babban Sufeton Ƴan Sanda Kayode Egbetokun, ya buƙaci masu shirin zanga zangar adawa da matsin rayuwa da yunwa a faɗin Najeriya da su miƙa sunayen su ga jami'an ƴan Sanda kafin ranar ɗaya ga watan Agusta da aka shirya zanga zangar.

Da yake Jawabi ga manema labarai Mista Kayode ya buƙaci duk wata ƙungiya da take da shirin shiga zanga zangar ta miƙa sunan ta ga ƙwamishinan ƴan Sanda na Jihar da take, yana mai nuni da cewa tunda dai zanga-zangar ta lumana ce toh akwai Buƙatar sanin Jagororin ta.

Ya ƙara da cewa mun yadda cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa ƴan ƙasa damar haɗuwa domin yin zanga-zanga cikin lumana, amma saboda tsaron rayuka da dukiyoyin Al'umma, muna bada Shawara ga ɗaukacin ƙungiyoyin da zasu yi zanga zangar da su miƙa sunayen su ga ƙwamishinan ƴan Sanda na Jihohin su, tare da bayyana hanyoyin da zasu bi, da wurin taruwa da sauran bayanai.

Sifeton ƴan Sandan ya kuma tunatar da masu shirya zanga zangar akan matakan da zasu ɗauka wajen ganin ba'a karya doka da Oda ba kuma wasu ba zasu sauya manufar ta ba, idan kuma sun lura da masu yunƙurin yin hakan su bayyana su domin tsame su daga cikin su.

Mista Kayode ya bayyana cewa Rundunar a shirye take domin bada kariya ga masu zanga zangar matuƙar sun baiwa jami'an tsaro haɗin kai.

A wani ɓangaren kuma Sufeton Ƴan Sandan ya bayyana cewa sun samu wasu bayanai da suke nuna yiyuwar wasu daga ƙasashen waje suna yunƙurin karkatar da zanga zangar domin cimma wata manufar su da ƙashin Kai.

Daga Lukman Aliyu Iyatawa

Address

BLK Maiduguri
Maiduguri

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Haske Newspaper posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share