Alkalami

Alkalami Ku kasance da mu domin samun labarai daga ko ina a faɗin duniya.

Ko zan rasa abincin da zanci bazan taɓa barin Matata ta tafi Saudiyya neman kuɗi ba.Abinda naje na gani da idona ba wani...
10/04/2025

Ko zan rasa abincin da zanci bazan taɓa barin Matata ta tafi Saudiyya neman kuɗi ba.

Abinda naje na gani da idona ba wani ya bani labari ba b***e nace ƙarya yake shine hujjojina akan hakan.

Duk wanda yabar matarsa, Matar Aure kam ba wai Bazawara ko wata mara aure ba Lallai ya tafka hamaganci mafi girma kuma dole ya tafka dana sani.

Yawanci Bance duk ba idan mace ta waye ta shekara ɗaya shikenan zata wanke Fuskata da Fitsarin ɓauna zata bar Gidan "Uwar jirgin "da ta kawo ta. Zata k**a haya ne kawai ko da bata da aikin gidan larabawa a hannu ko aikinta ya "Kassare" ɗakin da ta k**a haya nan zata zo ta zauna ko wata nawa zata yi bata da aiki tana nan gidan .

Kuma kada kace gidan wai ɗakunan mata zalla ne , ƙaryane , Mata da Maza ne wani ɗakin ma da matan da Mazan billahillazi a cakuɗe suke kwana akan katifa ɗaya.🫣

Don duk Macen da ka ga ta iya k**a ɗaki ɗaya ita kaɗai babu haɗin gwiwa to ta kai jan wuya ba ƙaramin kuɗi ta tara ba.

Kuma irin gidan nan kowa shiga yake kowanne takari afkawa yake a gaban ƙarti matan suke canja kaya sai kaga ɗaki daya ƙarti biyar , shida sun zauna an dafa musu abinci suna ta hira da matan idan bacci ya k**a mutum kawai haka zai cewa Macen '' ɗan matsamin na kishingiɗa jiya kwana nayi a "Magasala" anan zai kwana ga ƙugunta ga nasa suna bacci bayan an gama shan Maganin Bacci.

Kuma Matan sun zama abun banza " Da Tsiren Ashara riyal na bakin"TITIN NEXT LEVEL" Sai ka yi "Dug-Dug".

To dama "Ƴar Haja" tayi wata uku ko biyu bata aikin komai bata da ko riyal ɗaya Yaseen da Shinkafar "Sitta Riyal" sai ta Bari ƙaton banza ya haska fitilar sa.

Kuma bayan duk nasan wannan kuma da yake Ni cikakken ajawo ne sai na bar matata taje wannan ƙasar aikatau.

Yo ko gidan Larabawan ba tsira suke yi ba, Mai gida ya kawo musu hari yaran gidan Maza Manya da ƙanana suna kawo musu hari.

Ƙaton banza balarabe sai yasa tayi masa tausa kuma wallahi sai tayi ko tayi asarar albashin ta, Kwanciya zai yi rubda ciki tayi ta mammatsa masa cinya har kaga ya zuge wandonsa ya sassauta shi ya ɗan leƙo da 'Alkasarsa" yana Mata showing.

Irin wannan baɗalar da ake tafkawa naga cewa irina Bawan Allah bai dace na zauna a "Riyadh" na Koma jidda ashe duk kanwar ja ce kawai dai banbancin "Takari" sunfi yawa a Riyadh.

Kana zaune a Najeriya ƙaton asara ka tura matarka wai Saudiyya neman kuɗi.

Ƙarshe idan taje ta ɗanɗano daɗin Maza Matasa tana dawowa sakinka zata yi ta Auro mai jini a jika.

Ƴan Ƙalilan ne Na Allah mata Masu zuwa ƙasar nan.

A Maza Ina cikin Bayin Allah na gari.

Wabillahillazi Farkon zuwana aka kaini wani gida a jarradiya aka nuna min wajen kwanciyata wai katifarmu ɗaya da wata Mace Ƴar Kaduna nace kai Wai dan Allah nan Saudiyya ne ko "Los Angeles" ko zamana a "South Afirka" Banga wannan ta'addancin ba. Wallahi naƙi kwana har wani tanɗe baki naga tana yi matar nan ga ta rusheshiya taga Yaro " Mai Ƙamshin tuffa' .

Allah Ghalib.

Copied...
Baffa Kabeer

Kamfanin sadarwa na MTN Nigeria ya rage farashin wasu daga cikin data bundle da ya kara kudin su a kwanakin baya.Idan ba...
17/02/2025

Kamfanin sadarwa na MTN Nigeria ya rage farashin wasu daga cikin data bundle da ya kara kudin su a kwanakin baya.

Idan baku manta ba a Talatar makon da ya gabata ne, MTN s**a kara kudin 15GB data data N2000 zuwa N6000 wanda hakan ke nufin anyi karin kashi 200 cikin 100 wato 200%, wanda bakan ne ya jawo ce-ce kuce daga ma'abota amfani da layin kamfani.

Tun a farko dai hukumar sadarwa ta Nigeria wato NCC ce ta sahalewa kamfanonin da suyi karin da bai wuce kashi 50 cikin 100 ba 100% na tsohon farashin saide kuma kamfanonin sunyi gaban kan su wajen wuce gona da irin kan karin da s**a yi.

Itama kungiyar kwadagon kasar wata NLC ta bayyana bacin rabta inda ta ce wannan karin farashin rashin adalci ne ga ƴan kasar tuni dama su ke fama hauhawar farashin abinci, man fetur da wutar lantarki.

A ranar Alhamis, jaridar The Punch, tace MTN sun maido da tsohon farashin datar a wata wasika da s**a aikewa da masu amfani da layin su inda s**a ce "forgive and forget"

Kazalika MTN ya ce duk da cewa yana da dalilan karin farashin, "Mun yarda cewa wannan kuskure ne.”

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, An amince da karin farashin tun da farko ne saboda tsarin 15GB - wanda kawai ake samu ta hanyar manhajar MTN ragi ne na wani takaitaccen lokaci na tallata don jawo hankalin masu karamin karfi da kuma kara shiga intanet.

Tuni dai kamfanin ya sanar da cewa tsofaffin masu amfani da tsarin 15GB din ne kawai zasu iya cigaba da siyan sa a tsohon farashi inda ya bayyana cewa sababbin masu amfani da tsarin zasu biya sabon farashin da akayi kari.

Tuni dai kungiyar kwadagon kasar wato NLC tayi kira ga kamfanonin MTN, Airtel da kuma GLO da su gaggauta maido da tsohon farashin da suke siyar da dukkan datar su kafin 1 ga watan Maris mai zuwa ko kuma su dauki dakatar da ayyukan kamfanonin gaba daya.

06/02/2025

MAJALISAR WAKILAN NAJERIYA TA BAYAR DA SHAWARAR ƘIRƘIRO SABBIN JIHOHI 31

Kwamitin sake nazarin kundin tsarin mulkin Najeriya na majalisar wakilan ƙasar ya bayar da shawarar ƙirƙiro ƙarin sabbin jihohi 31 a ƙasar.

Mataimakin kakakin majalisar wakilan ƙasar, Hon.Benjamin Kalu ne ya bayyana haka lokacin da ya karanto wasiƙar kwamitin, a zaman majalisar da ya jagoranta yau Alhamis.

Idan aka amince da buƙatar adadin jihohin Najeriya zai kai 67.

Ga jerin sabbin jihohin da kwamitin ya bayar da shawarar ƙirƙira daga wasu jihohin ƙasar na yanzu:

AREWA TA TSAKIYA

Benue Ala daga jihar Benue.
Okun daga jihar Kogi.
Okura daga jihar Kogi.
Confluence daga jihar Kogi.
Apa-Agba daga jihar Benue.
Apa daga jihar Benue.
Abuja dada babban birnin ƙasar.

AREWA MASO GABAS

Amana daga jihar Adamawa.
Katagum daga jihar Bauchi.
Savannah daga jihar Borno.
Muri daga jihar Taraba.

AREWA MASO YAMMA

New Kaduna da daga jihar Kaduna State.
Gurara daga jihar Kaduna.
Tiga daga jihar Kano.
Kainji daga jihar Kebbi.
Ghari daga jihar Kano.

KUDU MASO GABAS

Etiti daga duka jihohin yankin shida.
Adada daga jihar Enugu.
Urashi daga duka jihohin yankin shida.
Orlu daga jihar duka jihohin yankin shida.
Aba daga duka jihohin yankin.

KUDU MASO KUDANCI

Ogoja daga jihar Cross River.
Warri daga jihar Delta.
Bori daga jihar Rivers.
Obolo daga jihohin Rivers da Akwa Ibom.

KUDU MASO YAMMA

Toru-ebe daga jihohin Delta da Edo da kuma Ondo.
Ibadan daga jihar Oyo.
Lagoon daga jihar Lagos.
Ijebu daga jihar Ogun.
Oke-Ogun daga jihohin Ogun da Oyo da kuma Osun
Ife-Ijesha daga jihohin Ogun Oyo da kuma Osun.

Madogara BBC HAUSA

Buhari, ya bayyana haka ne yayin jawabi a taron jam'iyyar APC a Katsina, wanda ya ce bai azurta kansa da dukiyar ƙasa lo...
27/01/2025

Buhari, ya bayyana haka ne yayin jawabi a taron jam'iyyar APC a Katsina, wanda ya ce bai azurta kansa da dukiyar ƙasa lokacin da yake mulki ba.

A cewar tsohon shugaban ƙasar, sha'anin shugabanci a Nijeriya sai Allah, saboda 'yan ƙasar ba su san ƙalubalen da ke tattare da jagoranci ba.

Me za ku ce game da kalaman tsohon shugaban ƙasar?

A safiyar wannan rana ta Asabar 28/12/2024 al'ummar yankin Rimin Auzinawa dake karamar hukumar Ungogo dake birnin Kano s...
28/12/2024

A safiyar wannan rana ta Asabar 28/12/2024 al'ummar yankin Rimin Auzinawa dake karamar hukumar Ungogo dake birnin Kano s**a rufe titin da ya taso daga kofar kansakali zuwa Ring Road ga masu manyan motocin diban yashi.

Wannan na zuwa ne sak**akon take wata mata da wani mai Tipper yayi a jiya juma'a a kan titin wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar matar.

Al'ummar yankin da abun ya faru sun bayyana cewa, ya zama wajibi masu manyan motocin su dinga tsayawa iya Ring Road.

A karshe sunyi kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki don magance musu wannan matsala.

Imam Maleek Auwal Warure ✍️

30/11/2024
28/11/2024

Menene banbanci tsakanin so da kauna?

Sanarwar rundunar sojin ta Nijar ta ce an rika bin lakurawan da jirage marasa matuka har zuwa dajin Muntseka dake yankin...
26/11/2024

Sanarwar rundunar sojin ta Nijar ta ce an rika bin lakurawan da jirage marasa matuka har zuwa dajin Muntseka dake yankin Konni sannan aka yi musu ruwan wuta.

Nasiha Kuke Bukata ko 50k Cash ?
26/11/2024

Nasiha Kuke Bukata ko 50k Cash ?

Labari: Ya kasance daya daga cikin mutanen da s**afi Tallafawa Al'umma A 2024... Ahmed Musa Ya Yafewa Masu Hayarsa shagu...
26/11/2024

Labari: Ya kasance daya daga cikin mutanen da s**afi Tallafawa Al'umma A 2024... Ahmed Musa Ya Yafewa Masu Hayarsa shagunan sa kudin Hayar Shekara Daya.

Dan wasan na Super Eagles da Kano Pillars, Kaftin Ahmed Musa, ya yafe wa kudaden hayar shagunansa na shekara dake kan titin gidan Zoo.

Bisa la’akari da wahalhalun da kasar nan ke ciki, Musa ya bukaci mazauna shagunan nasa da su gina babban jarinsu, da kuma mayar da hankali wajen rike kudin hayarsu.

Allah ya cikawa kaftin Ahmed Musa MON burinsa Allah yakara karfin imani ameen.

● Fagen Wasanni

Maza suna gudu na saboda yalwar hanci da Allah yai min. Amma nayi Imani mijina na nan tafe. Cewar wannan baiwar Allah. I...
26/11/2024

Maza suna gudu na saboda yalwar hanci da Allah yai min. Amma nayi Imani mijina na nan tafe. Cewar wannan baiwar Allah.

Imam Maleek Auwal Warure

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Alkalami posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Alkalami:

Share