Rariya

Rariya Jaridar Rariya jarida ce wadda take kawo muku sahihan labarai.

02/05/2024
Dan takarar Gwamnan jihar Sokoto Mohammed Sadiq ya yi wa jaridar Nasara jaje akan abin da ya faru da su na asaraTsohon d...
28/08/2023

Dan takarar Gwamnan jihar Sokoto Mohammed Sadiq ya yi wa jaridar Nasara jaje akan abin da ya faru da su na asara

Tsohon dan takarar Gwamnan jihar Sokoto Mohammed Sadiq ya yi wa jaridar Nasara jaje akan abin da ya faru da su na asara.

Sadiq ya roki Allah madaukakin sarki da ya mayarwa gidan jaridar ta Nasara da mafificin alkairin sa.

ZABEN RABA GARDAMA!!2023: Shin idan zaben 2023 ya kasance tsakanin Atiku Abubakar da Bola Tinubu wa kuke ganin zai iya z...
07/12/2021

ZABEN RABA GARDAMA!!

2023: Shin idan zaben 2023 ya kasance tsakanin Atiku Abubakar da Bola Tinubu wa kuke ganin zai iya zama sabon angon Najeriya ne?

Tinubu ko Atiku?

Sokoto Online

INNALILLAHI WA INNA ILAHI RAJI'UUN!Allah ya yi wa Malam Ibrahim Sambo Muqaddami shugaban Qadiriyya na jihar Sokoto rasuw...
07/12/2021

INNALILLAHI WA INNA ILAHI RAJI'UUN!

Allah ya yi wa Malam Ibrahim Sambo Muqaddami shugaban Qadiriyya na jihar Sokoto rasuwa

Za a yi sallar jana'izar sa da misalin karfe 12:00 na rana a Masallacin Shehu dake Hubbare.

Ubangiji Allah ya jikan sa da rahama ya kuma kyautata namu karshe.

S-bin Abdallah Sokoto

Zan jagoranci zanga-zangar adawa da karin kudin man fetur zuwa N340 da Buhari ke shirin yi , kai ba zanga-zanga kadai ba...
04/12/2021

Zan jagoranci zanga-zangar adawa da karin kudin man fetur zuwa N340 da Buhari ke shirin yi , kai ba zanga-zanga kadai ba, harma da kashe-kashe sai an yi idan ta k**a~Inji Sheikh Bello Yabo

Babban malamin addinin musulunci a jihar Sokoto Sheikh Bello Yabo ya mayarda martani kan shirin gwamnatin Najeriya na karawa man fetur kudi a cikin sabuwar shekarar 2022.

Babban malamin ya ce babu dalilin da zai sa su zura ido ana gallazawa talakkawa a wannan gwamnati, don haka doli ne su fito su yi zanga-zangar wannan rashin imani da tausayin talakkawa da gwamnatin Buhari ke shirin yi na karawa man fetur kudi zuwa N340.

Malamin ya ce k**ar yadda Buhari ya fito ya yi zanga-zangar karawa man fetur kudi kafin ya hau mulki mu ma za mu fito mu yi zanga-zangar adawa wannan rashin tausayi.

Malamin ya ci gaba da cewa, ba zanga-zanga kadai ba, har ma da kashe-kashe sai an yi idan gwamnati ta ce za ta zartar da wannan kuduri na ta.

Shin meye ra'ayin ku ne akan wannan?

Sokoto Online

Na amince zan tsaya takarar shugaban kasa 2023-Inji Atiku Abubakar Masu karatu miye ra'ayin ku ne?
03/12/2021

Na amince zan tsaya takarar shugaban kasa 2023-Inji Atiku Abubakar

Masu karatu miye ra'ayin ku ne?

DA DUMI-DUMIN SU!Mun ayyana 'yan bindiga a zaman 'yan ta'adda-Ministan Shari'a MalamiMinistan shari'a na kasa Abubakar M...
02/12/2021

DA DUMI-DUMIN SU!

Mun ayyana 'yan bindiga a zaman 'yan ta'adda-Ministan Shari'a Malami

Ministan shari'a na kasa Abubakar Malami (SAN) ya fitar da sanarwar ayyana 'yan bindiga a zaman 'yan ta'adda bayan kai ruwa rana.

Ministan shari'a ya ce irin yadda wadannan 'yan bindiga ke kai hare-haren ta'addanci ba kakkautawa doli ne a ayyana su a zaman 'yan ta'adda, domin wannan mummunan aiki da aikatawa tsantsar ta'addanci ne. Don haka wajibi ne mu ayyana su a zaman 'yan ta'adda k**ar sauran mayakan kungiyar boko haram.

Ayyana 'yan bindigar dai a zaman 'yan ta'adda shine zai bai wa jami'an tsaro damar shiga daji domin yakar su da dukkanin wani nau'in makami da ake yakar 'yan ta'adda da su.

Shin ya kuka ji da wannan mataki na ayyana su a zaman 'yan ta'adda?

Sokoto Online

DA DUMI-DUMIN SU!Mu sanya al'ummar garin Kurawa dake cikin karamar hukumar Sabon-Birni cikin addu'a, tun karfe 7:30 na y...
02/12/2021

DA DUMI-DUMIN SU!

Mu sanya al'ummar garin Kurawa dake cikin karamar hukumar Sabon-Birni cikin addu'a, tun karfe 7:30 na yammacin yau 'yan bindiga s**a afkawa garin har kawo yanzu

Rahotanni dake zuwa mana sun tabbatar da cewa yanzu haka cikin daren nan 'yan bindiga sun afkawa garin Kurawa dake cikin karamar hukumar Sabon-Birni ta jihar Sokoto mai fama da hare-haren 'yan bindiga.

Tunda karfe 7:30 na yammacin yau Alhamis ne s**a afkawa garin har kawo yanzu karfe 8:32 basu bar garin ba suna cin karen su ba babbaka.

Ubangiji Allah ya kawo misu dauki.

Daga: Nura Ahmad

Ina son aure yaro matashi dan shekara 25 zuwa 30~ Inji shugabar kungiyar maryar Zawarawa ta KanoHajiya Altine Abdullahi ...
02/12/2021

Ina son aure yaro matashi dan shekara 25 zuwa 30~ Inji shugabar kungiyar maryar Zawarawa ta Kano

Hajiya Altine Abdullahi ta bayyana cewa, tana matukar son auren yaro matashi sabon jini dan shekara 25 zuwa 30.

Matar ta bayyana cewa, akwai fa'ida mai yawa tsohuwa ta samu karamin yaro ta aura.

Akan haka matar ta bayyana cewa a shirye take data auri matashi dan shekara 25 zuwa 30 matukar ta yi shawara da ya'yan ta.

Dudda yake matar ta bayyana cewa koda ace ya'yanta basu amince ba ita a shirye take data auri matashi mai kananan shekaru, tun da har bai sabawa addinin musulunci.

Matar ta ci gaba da cewa" Da ace an k**a macce da karamin yaro tana lalata ai gara ace auren sa ta yi".

Shin ya kuke kallon kalaman wannan mata ne?

Zan fitar da Najeriya daga dukkanin matsalolin da take ciki idan na zama shugaban kasa~Inji Tinubu
02/12/2021

Zan fitar da Najeriya daga dukkanin matsalolin da take ciki idan na zama shugaban kasa~Inji Tinubu

DA DUMI-DUMIN SU!Kotu ta dage shari'ar jagoran yan aware na IPOB Nnamdi Kanu zuwa 18 ga watan Janairun 2022, wanda hakan...
02/12/2021

DA DUMI-DUMIN SU!

Kotu ta dage shari'ar jagoran yan aware na IPOB Nnamdi Kanu zuwa 18 ga watan Janairun 2022, wanda hakan na nufin zai shiga sabuwar shekarar 2022 a kurkuku.

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN Daya daga cikin matasan Malamai daga bangaren 'yan darika a jihar Kano Sheikh Mas'ud...
02/12/2021

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Daya daga cikin matasan Malamai daga bangaren 'yan darika a jihar Kano Sheikh Mas'ud Mas'ud Hotoro wanda ya wakilci darikar Qadiriyyah a mukabalar da aka yi da Sheikh Abduljabbar ya rasu a daren jiya

Kamar yadda na samu labari, Malam Mas'ud Hotoro ya rasu sak**akon mummunan hatsarin mota da ya rutsa dashi a hanyar Kaduna zuwa Kano.

Muna rokon Allah Ya gafarta masa, Allah Ya sa Aljannah ta zamo makoma a gareshi.

-Datti Assalafiy

Address

Maitama

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Rariya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share